Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-02-24 16:07:10    
Ruhun wasanni ya inganta karfin zuciyar yaran mazauna wuraren da girgizar kasa ta Wenchuan ta shafa

cri
Bayan aukuwar mummunar girgizar kasa a gundumar Wenchuan ta lardin Sichuan a ran 12 ga watan Mayu na shekarar 2008, kamar yadda sauran jama'ar kasar Sin suka yi, 'yan wasan kasar Sin su ma sun ba da kyautar kudi da kayayyaki cikin himma da kwazo domin taimakawa al'ummar wuraren da girgizar kasar ta rutsa da su. Bayan watanni 9 ko fiye da aukuwar bala'in, wasu 'yan wasan da suka zama zakaru a yayin gasar wasannin Olympic ta Beijing, da masu aikin wasannin motsa jiki sun je wuraren da bala'in ya shafa domin karfafa gwiwar yara mazauna wuraren bisa ruhun wasannin motsa jiki don su karfafa karfin zuciyarsu domin jure wahala.

A bayan dakunan karatu na wucin gadi da aka gina a makarantar midil ta Nanxuan a birnin Mianzhu da ya fi shan wahalar girgizar kasar a shekarar bara, Kim Chang-back, tsohon babban malamin horas da wasanni na kungiyar wasan kwallon gora a fili ta mata ta kasar Sin, wanda asalinsa dan kasar Korea ta Kudu ne ya tsinci gorar da ya lakance ta sosai. Wannan filin wasa da ke gabansa yana da muhimmanci sosai kamar yadda filin wasan da aka yi amfani da shi a yayin gasar wasannin Olympic yake kasancewa.

A farkon watan Mayu na shekarar bara, cibiyar kula da wasan kwallon gora a fili ta babbar hukumar wasannin motsa jiki ta kasar Sin ta zabi makarantar midil ta Nanxuan da ke birnin Mianzhu a matsayin sansaninta na horaswa da kuma tace 'yan wasa sabbin jini. Amma mummunar girgizar kasa ta Wenchuan ta wargaje shirin gina sabon filin wasan kwallon gora a fili kwata-kwata. Bayan watanni 3 da aukuwar bala'in, a sakamakon goyon baya da bangarori daban daban suka nuna mata, makarantar midil ta Nanxuan ta gina gidajen karatu na wucin gadi domin maido da harkokin karatu, kana kuma, ta kafa wannan filin wasan kwallon gora a fili bisa ma'auni. Bayan aukuwar bala'in, Mr. Kim Chang-back ya ba da kyautar kudi da yawansa ya kai kudin Sin yuan dubu 100. Bayan watanni 8 ko fiye, wasu mambobin kungiyar wasan kwallon gora a fili ta mata ta kasar Sin da shi kansa sun je birnin Mianzhu domin gai da 'yan makarantar cikin halin aminci. Zhang Jingpeng, wani malamin da ke aiki a makarantar midil ta Nanxuan ya gaya mana tare da nuna godiya da cewar,"Zuwanku a makarantarmu ya iya karfafa gwiwarmu tare da kawo mana murna."

Zuwan 'yan kungiyar wasan kwallon gora a fili ta mata ta kasar Sin ya sanya yaran da ke zaune a wuraren da bala'in ya shafa sun ji dadin zamansu a wannan rana sosai.

A lokacin da yake ganin fuskokin yaran da suke yin dariya, Mr. Kim ya nuna cewa, ma'anar wasannin motsa jiki ita ce karawa sosai a tsakanin 'yan wasa a cikin filin wasa, kana kuma, ya iya kawo wa mutane annashuwa a zuciya. A matsayinsa na babban malamin horas da wasanni da ke aiki a kasar Sin, amma asalinsa dan kasar waje ne, Mr. Kim yana fatan yaran da bala'in ya shafa za su iya kara samun fahimta kan ruhun wasanni, za su kuma iya ci gaba da yin gwagwarmaya domin samun karfi.

Mai yiwuwa ne yaran da suke yin wasa da kwallon gora a fili za su iya komawa zaman rayuwarsu ta da bayan da suka kyautata kansu a cikin gajeren lokaci. Amma wasu sun rasa abubuwa da dama har abada a sanadiyyar bala'in. Mummunar girgizar kasa ta Wenchuan ta jawo asarar dimbin rayukan mutane yayin da jikkata da yawa. Mutane da yawa sun kasa amincewa da rasa hannu da kafa nan take, sun yi bakin ciki kwarai da gaske. Li Duan, wanda ya zama zakara a yayin gasar wasannin Olympic ta nakasassu ta Beijing a wasan dogon tsalle da na tsallen nesa na yin dira 3, da Dong Fuli, wadda ta zama zakara a yayin gasar wasannin Olympic ta nakasassu ta Beijing a wasan kwallon tennis kan keken hannu, da Tan Yanhua, wadda ta zama zakara a yayin gasar wasannin Olympic ta nakasassu ta Beijing a wasan kwallon raga wato volleyball tare da zaunawa a kasa da sauran 'yan wasa nakasassu sun yi hira da su da zummar karfafa karfin zuciyar wadannan yaran da suka nakasa a sakamakon bala'in don su maido da burinsu na ci gaba da zamansu da kuma sanin fannonin da za su iya nuna gwanintarsu a kai, bisa abubuwan da suka faru a kansu.

A cibiyar kula da nakasassu ta birnin Deyang, Li Duan da sauran 'yan wasa sun yi taron bita, inda suka bayyana labarunsu dangane da jure wahalar da nakasa ta kawo musu, da fukantar matsalar zaman rayuwa bisa zuciya mai karfi, da kuma gano kimarsu. Li Duan mai shekaru 31 da haihuwa, kafin ya zama makaho a sakamakon wani hadari, wani dan wasan kwallon kwando ne. Kafin ya samu aikin horaswa, ya yi dogon lokaci yana bakin ciki sosai. Amma a karshe dai ya zama wani dan wasan dogon tsalle, ya kuma sami lambobin zinariya 2 a yayin gasar wasannin Olympic ta nakasassu ta Beijing. Li Duan ya ce,"In an rufe maka wata kofa, to, za a bude maka wata taga. A wancan lokaci, na yi bakin ciki sosai, ban iya ci gaba da yin wasan kwallon kwando ba, ba na son ganawa da abokaina. Amma a karshe dai na amince da yanayin nakasa da nake ciki, na bude zuciyata ga saura, daga baya na samu dama. A daidai wancan lokaci, an gano cewa, ina da kwarewar wasannin motsa jiki. Shi ya sa aka wakilta ni in zama wani dan wasa nakasasshe."

Labarin Li Duan ya bawa yara gwiwa sosai. Tare da taba lambobin zinariya da ke gaban kirjin Li Duan, dukkan yaran sun nuna cewa, za su sami jiyya da ake yi musu cikin himma da kwazo, za su yada fifikonsu domin ba da gudummawarsu ga zaman al'ummar kasar a nan gaba.

A zahiri kuma, bayan aukuwar bala'in, wasu zakarun gasannin wasannin Olympic da suka zo daga lardin Sichuan sun sha zuwa wuraren da bala'in ya shafa domin yin jaje ga 'yan makarantar da suka zo daga gari iri daya, inda kuma suka karfafa gwiwarsu da su yi karatu tukuru da motsa jiki yadda ya kamata, don haka za su iya kishin zaman rayuwa da kuma nuna fara'a ga kome da kome.

Zou Kai, dan wasan lankwashe jiki, da Yin Jian, 'yar wasan kwalle-kwalle da suka zama zakaru a cikin gasar wasannin Olympic ta Beijing sun je makarantar midil ta Mianyang da ke birnin Mianyang tare da kyautar murnar shagalin gargajiya na yanayin bazara bisa kalandar gargajiya ta kasar Sin, inda suka raka 'yan makarantar su shiga wasannin motsa jiki. Wadannan zakaru 2 da asalinsu 'yan lardin Sichuan ne suna fatan 'yan makarantar za su iya yin murnar shagalin gargajiya na yanayin bazara na kasar Sin na farko bayan aukuwar bala'in kamar yadda suka yi a da.

'Yan makarantar da yawa sun mayar da Zou Kai tamkar abin koyi ne a gare su. Zuwan wadannan zakarun gasannin wasannin Olympic da suke ganinsu a talebijin kawai a da da kuma raka su domin shiga wasannin motsa jiki dukkansu sun ba da kwarin gwiwar yaran sosai. Zou Kai yana fatan ruhun wasannin Olympic zai iya taimakawa 'yan makarantar da su manta da bakin ciki da girgizar kasar ta kawo musu. Mr. Zou ya ce,"Ina fatan zan zame musu abin koyi bisa karfin kira da nake da shi da kuma aiki tukuru da nake yi. Ina fatan zan iya ba su kwarin gwiwa."

Yau da watanni 9 da suka wuce, a filin wasa da ke makarantar midil ta Mianyang, an gina wa mutane gidajen kwana na wucin gadi. Yau ma yara sun sake yin wasa a filin wasansu, inda suka yi murnar shagalin gargajiya na yanayin bazara na kasar Sin na farko bayan aukuwar bala'in tare da zakarun gasannin wasannin Olympic da suke sha'awa ta hanyar motsa jiki. Bayan da suka bari tunanin da bala'in ya kawo musu, yaran sun nuna fatan alheri ga shekara mai kamawa.

"Ina fatan nan gaba zan iya shiga gasar wasannin Olympic!"

"Ina fatan dukkanmu za mu yi karatu tukuru. Ina son in shiga jami'a!"

"Ina da kakani. Ina fatan za su kasance cikin koshin lafiya!"(Tasallah)