Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-02-23 16:01:10    
Wasu labaru game da kananan kabilun kasar Sin

cri
A wajen taron takaita ayyukan da aka gudanar a shekara ta 2008 da gwamnatin jihar Tibet mai cin gashin kanta ta kasar Sin ta shirya, an bayyana cewa, an riga an kafa wani tsarin bada ilimi na dukkan fannoni a jihar, ciki har da aikin ilmantarwa kafin shiga makaranta, da aikin ilmantarwa ba tare da biyan kudi ba, da aikin ilmantarwa a makarantun sakandare da jami'o'i da dai sauransu.

An ce, akwai makarantu iri daban-daban sama da 1000 a jihar Tibet, adadin daliban makarantun ya tasam ma dubu 550, wanda ya karu da dubu 115 idan aka kwatanta shi da na shekarar 2002. A waje daya kuma, yawan kananan yara wadanda suka cancanci shiga makarantar firamare ya kai kashi 98.5 bisa dari, ana gudanar da aikin bada ilimi har na tsawon shekaru 9 ba tare da biyan kudi ba a gundumomi 70 daga cikin dukkan gundumomi 71 na jihar. Kazalika kuma, aikin bada ilimi a jami'a ya kyautatu kwarai da gaske, wasu fannonin koyarwa masu salon musamman na kabilar Tibet suna cigaba da bunkasa, ciki har da likitanci da magungunan gargajiyar Tibet, da harshen Tibet, gami da kide-kiden Tibet. A halin yanzu, akwai jami'o'i da kwalejojin koyon sana'o'in musamman guda 6 a jihar Tibet, yawan mutanen da suke shiga jami'o'i da kwalejoji ya tasam ma kashi 20 daga cikin dari.