Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-02-23 15:55:09    
Shigar da kasar Sin a WTO ya bayyana yadda kasar Sin ke bude kofata ga kasashen waje

cri
Da misalin karfe 7 saura minti 20 na ran 10 ga watan Nuwamba na shekara ta 2001 bisa agogon Qatar, lokacin da Mr. Yousef Hussain Kamal, ministan sha'anin kudi da tattalin arziki da cinikayya na kasar Qatar ya buga hama irin ta katako kan tebur, wannan hama ta bude kofar kungiyar cinikayya ta Duniya, wato WTO ga kasar Sin. Bayan da aka yi shawarwari har na tsawon shekaru 15, a wannan rana, kasar Sin ta zama memba ta 143 a cikin kungiyar WTO. Wannan shi ne daya daga cikin sakamako mafi muhimmanci da kasar Sin ta samu a fannin tattalin arziki da cinikayya bayan da ta soma aiwatar da manufar yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga kasashen waje. A cikin wadannan shekaru 7 bayan shigar da kasar Sin cikin kungiyar WTO, kasar Sin ta cika alkawuran da ta dauka cikin sahihanci bisa halin da ake ciki a duniya.

Yawan bakakun takardar shigar da kasar Sin a cikin kungiyar WTO da aka amincewa da ita a shekara ta 2001 ya kai kimanin dubu 10. Ma'anarsu mafi muhimmanci ita ce "bude kofa". Da farko dai, a fannin cinikin waje, kasar Sin ta cika alkawarinta na rage harajin kwastan kan kayayyakin da take shigi da fici daga dukkan fannoni a cikin wadannan shekarun da suka gabata. Sannan ta aiwatar da matakai iri daban daban da suka samu amincewa daga kungiyar WTO domin raya cinikin waje. Mr. Shishir Priyadarsh, direktan hukumar neman cigaba ta kungiyar WTO ya ce, "A matsayin wata kasa wadda ke dogara kan kayayyakin da take fitarwa domin neman cigaban tattalin arziki, kasar Sin ta samu babban cigaba wajen raguwar harajin da ake bugawa kan aikin gona da sauran sana'o'in da ba na aikin gona ba. Ta rage kimanin harajin da take bugawa kan aikin gona har ya kai 9.8% kawai, kuma ta rage harajin da take bugawa kan sauran sana'o'in da ba na aikin gona ba har ya kai 8% kadai. Wadannan matakan rage harajin kwastan da kasar Sin ta dauka sun amfanawa karuwar yawan cinikin waje da aka samu a fannonin da abin ya shafa."

Idan an kwatanta su da cinikin kayayyaki, kasar Sin ta fi samun cigaba wajen bude kofarta ga kasashen waje a fannonin kudi da sadarwa. Alal misali, yanzu bankuna masu jarin waje sun iya bai wa bakinsu hidimar kudin Sin a duk fadin kasar Sin. Dukkan kamfanonin inshora masu jarin waje sun iya bude sassansu a kowane gari ko birni. A waje daya, kamfanoni masu jarin waje sun samu izinin tafiyar da harkokin sadarwa a kasar Sin ta hanyar kafa kamfanoni masu hada jarinsu da na kasar Sin. Ya zuwa yanzu kamfanoni masu jarin waje guda 4 sun riga sun samu takardar tafiyar da harkokin sadarwa a kasar Sin. Bugu da kari kuma, kamfanonin saye da sayarwa da ba na sari ba na duniya, kamar su Wal Mart na Amurka da Carrefour na Faransa sun riga sun shigo kasar Sin, kuma suna samun cigaba cikin sauri.

Yanzu Sinawa suna da karin damar zaban kamfanonin da suke ba da hidimomi iri daban daban bayan da aka bude kofar kasuwanni. Sabo da haka, kamfanonin kasar Sin suna fuskantar matsin lamba a fannin yin takara a kasuwa. Amma galibin 'yan kasuwa suna ganin cewa, bayan da aka shigar da kasar Sin a cikin kungiyar WTO, kamfanonin kasar Sin sun samu cigaba kwarai. Mr. Jiang Jianqing, shugaban bankin masana'antu da kasuwanni na kasar Sin ya ce, "Lokacin da muke waiwayen tarihi, muna da tunani da yawa a cikin zukatanmu. Da farko dai, takara ta zama karfi mafi muhammanci wajen ciyar da bankunan kasar Sin gaba. Yin takara a kasuwa ya canja tunanin bankunan kasuwanci na kasar Sin, kuma ya sa kaimi ga yin kwaskwarima kan bankunan kasuwanci na kasar Sin. A waje daya kuma, yin takara a kasuwa ya sa bankunan kasuwanci na kasar Sin sun shiga kasuwannin hada hadar kudi na duniya. Yanzu ana ma'auna aikin bankunan kasuwanci na kasar Sin ne kamar yadda ake ma'auna bankunan kasuwanci na sauran kasashen duniya bisa ma'auni daya da duk duniya suke bi."

Yanzu, manyan bankunan kasuwanci na kasar Sin guda ukku, wato bankin masana'antu da kasuwanni na kasar Sin da bankin gine-gine na kasar Sin da kuma bankin zirga-zirga na kasar Sin suna hada hada kudi a kasuwannin hada hada kudi na duniya. Kamfanin Mobile na kasar Sin, wato China Mobile ya riga ya zama kamfanin sadarwa da ke da masu yin amfani da wayar salula mafi yawa a duk duniya. Bugu da kari kuma, kamfanoni masu zaman kansu na kasar Sin da yawa, kamar su kamfanin kera motoci kirar Chery da kamfanin kera motoci kirar Geely da kamfanin sadarwa na ZTE da kamfanin sadarwa na Huawei suna samun bunkasuwa a kasuwannin kasashen duniya. Wadannan sakamako ne da aka samu bayan shigar da kasar Sin a cikin kungiyar WTO. Mr. Long Yongtu, wakilin farko wanda ya taba kulawa da shawarwarin shigar da kasar Sin cikin kungiyar WTO, kuma babban sakatare na yanzu na dandalin tattaunawa na Asiya na Bo'ao ya ce, lokacin da ake shawarwarin shigar da kasar Sin a cikin kungiyar WTO, gwamnatin kasar Sin ta fi nuna damuwa ko za a kawo illa ga sana'o'in ba da hidima na kasar Sin bayan shigar da kasar Sin cikin kungiyar WTO? Amma yanzu sana'o'in ba da hidima na kasar Sin sun fi samun cigaba fiye da kima. Mr. Long ya ce, "Lokacin da muke shawarwarin shigar da kasar Sin cikin kungiyar WTO, mun fi yi nazari kan wahalolin da mai yiyuwa ne za mu sha. Amma, bayan da aka shigar da kasar Sin cikin kungiyar WTO, mun gane cewa, mun kasa da kiyasta karfin yin takara na kamfanoni da masana'antunmu. Bayan da aka shigar da kasar Sin a cikin kungiyar WTO, mun samu moriya sosai a fannonin da muka dauka cewa za mu sha wahala, kamar a fannin aikin gona. Yanzu mun samu cigaba sosai wajen sanin ma'aunin amfanin gona da ma'aunin tabbatar da ingancin amfanin gona da ma'aunin tabbatar da ingancin muhalli da dai sauransu."

Lokacin da ake bude kofar kasuwannin kasar Sin ga sauran kasashen duniya, kasar Sin tana kuma kokarin kyautata tsarin kare ikon mallakar ilmi. Alal misali, kasar Sin ta yi kwaskwarima kan "Dokar ikon mallakar fasaha" da "Dokar tambarin kayayyaki" da "Dokar mai wallafa litattafai" da dai sauran dokokin da suke da nasaba da ikon mallakar ilmi. Haka kuma, kasar Sin tana kokarin yada ilmin kare ikon mallakar ilmi a duk fadin kasar domin tabbatar da ganin jama'a fararen hula ma sun san kare ikon mallakar ilmi. Mr. Yi Xiaozhun, mataimakin ministan kasuwanci na kasar Sin ya ce, yanzu tunanin da ake bi a cikin kungiyar WTO ya samu karbuwa a kasar Sin. Mr. Yi ya ce, "Kamar ka'idojin rashin nuna bambanci da daidaita harkoki a fili da aka tsara a cikin kungiyar WTO sun riga sun zama ka'idojin da kasar Sin take bi lokacin da take kafa dokoki. Yanzu muna bin ka'idojin kungiyar WTO domin cika alkawuran da muka dauka da kuma sauke nauyin da ke bisa wuyanmu a kai a kai."

Lokacin da kasar Sin take karfafa karfin bude kofar kasuwanni ga kasashen duniya da raya tattalin arziki irin na kasuwanci, kasar Sin tana kuma kokarin yada tunanin yin cinikayya cikin 'yanci a duk fadin duniya. Tun daga shekara ta 2003 zuwa yanzu, kasar Sin ta riga ta kafa unguwannin cinikayya cikin 'yanci guda 12 a kasashe da yankuna 29 da ke nahiyoyin Asiya da Oceania da Latin Amurka da Turai da kuma Afirka. Mr. Yi ya kara da cewa, kasar Sin tana zama wani muhimmin karfi a cikin cinikin waje na duniya. Mr. Yi ya ce, "Lokacin da kasar Sin ke ba da gudummawarta wajen raya tattalin arzikin duniya, tana kokarin neman cigaba cikin lumana da kuma raya wata duniyar da ke cike da jituwa. Bugu da kari kuma, muna kokarin shiga shawarwari na zagaye na Doha da aikin tsara sabbin ka'idojin cinikin waje. Sannan tana ciyar da aikin yin cinikayya cikin 'yanci a duk fadin duniya, kuma tana kokarin kiyaye moriyar kasashe masu tasowa. Yanzu kasar Sin ta riga ta zama wani muhimmin karfin daidaita matsalolin cinikayya na duniya." (Sanusi Chen)