Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-02-23 15:54:58    
An samu sabuwar dama kan warware batun Darfur

cri
A ranar 17 ga watan Faburairu, gwamnatin kasar Sudan da dakaru masu adawa da gwamnatin na kungiyar JEM sun rattaba hannu kan yarjejeniya mai taken 'nuna fatan alheri da shimfida aminci da juna don warware matsalar Darfur', a birnin Doha na kasar Qatar. Sa'an nan yarjejeniyar ta kawo wa jama'a kyakkyawan fata kan ciyar da aikin shimfida zaman lafiya a yankin Darfur gaba, kuma an ce za ta taimaka wajen tabbatar da kwanciyar hankali a kasar Sudan.

Bangarorin 2 sun cimma yarjejeniyar ne bayan kwanaki 8 da suka yi kokarin muhawara da juna. Kuma a wajen shawarwarin, sun gamu da matsaloli da yawa.

Da farko, kungiyar JEM ta ce, kasar Qatar a matsayinta na kasar Larabawa, ba za ta aiwatar da aikin sulhuntawa cikin adalci ba. Shi ya sa ta ki shirya shawarwarin a birnin Doha. Sa'an nan bayan da aka tabbatar da wuri da lokacin da za a shirya taron, Khalil Ibrahim, shugaban kungiyar JEM, wanda ya dade yana zaune a Ndjamena, hedikwatar kasar Chadi, ya nuna kin amincewa kan hanyar da jirginsa zai bi ta ketara sararin sama na kasar Sudan, domin tsoron idan jirgin ya gamu da matsala ya sauka a kasar Sudan ba zata, gwamnatin kasar Sudan za ta samu damar cafke shi. Sa'an nan canza hanyar da aka yi ya sa an samu jinkirin rana daya kan isar da Khalil Ibrahim birnin Doha.

Haka kuma, yayin da ake shawarwari, kungiyar JEM ta zargi gwamnatin kasar Sudan da jibge sojoji a Darfur don neman kai hari kan dakarun JEM. Amma gwamnatin kasar Sudan ba ta yarda da zargin ba.

Bisa kokarin da aka yi na tattaunawa da juna, bangarorin 2 sun cimma ra'ayi daya a karshe, inda suka yarda da saki fursunonin yaki, da tsagaita bude wuta, da komar da masu gudun hijira gidajensu, da ba da taimako wajen jigilar kayayyakin agaji, da dai makamantansu. Ban da wannan kuma, ana neman sake yin shawarwari sauran makwani 2, sa'an nan an yi alkawarin wanzar da zaman lafiya cikin watanni 3 da ke biyo bayan shawarwain da za a yi.

Manazarta na ganin cewa, a wajen shawarwarin da aka yi a tsakanin bangarorin 2 na kasar Sudan, an samu nasarori da yawa.

Da farko dai, an ciyar da aikin shimfida zaman lafiya a yankin Darfur gaba. Domin tun da gwamnatin kasar Sudan da wani rukunin dakaru masu adawa da gwamnatin suka daddale yarjejeniya a birnin Abuja ta kasar Naijeriya a watan Mayu na shekarar 2006, sauran dakarun da ba sa ga maciji da gwamnatin kasar sun ki yarda da yarjejeniyar, kuma ba su yarda da maido da shawarwari da gwamnatin ba. Sai dai yanzu sabuwar yarjejeniya ta zo, ta kuma canja halin da ake ciki.

Na biyu, an ce yarjejeniyar da aka kulla a wannan karo za ta taimaka wajen tabbatar da kwanciyar hankali a yankin Darfur. Domin ana kyautata zaton cewa, kungiyar JEM ka iya dan ja da baya kan aikace-aikacenta a yankin Darfur.

Na uku, ana tsammanin cewa, yarjejeriyar za ta taimaka kan aikin samar da agaji ga jama'ar yankin Darfur da wutar yaki ta ritsa da su. Matsalar masu gudun hijira ta riga ta zama batu mafi haifar da radadi a yankin Darfur.Shi ya sa, sasanta batun nuna kin jinin juna a tsakanin gwamnatin kasar da dakaru zai zama abin alheri ga farar hula da suka rasa gidajen zama.

Na hudu, an ce, yarjejeniyar da gwamnatin kasar Sudan da dakarun kasar suka rattaba hannu a kai za ta sa kotun duniya ta sake la'akari da ko ya dace ta ba da umarnin kama shugaban kasar Sudan, Omar El Bashir. Da ma, kafofin watsa labaru na kasashen yamma sun ce, ana shirya kai karar shugaba El Bashir a gaban kotun duniya kan cewar ya aikata laifukan yaki.(Bello Wang)