Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-02-19 09:46:25    
Gaisuwar musamman ta shiga shekarar saniya ta Sinawa zuwa ga masu sauraronmu

cri

Masu sauraro, a makon da ya gabata, yaya lamura suke gudana gare ku? Muna fatan kuna cikin koshin lafiya kamar yadda muke a nan birnin Beijing. Ga shi yanzu a nan kasar Sin, jama'a na murnar bikin yanayin bazara, wato bikin gargajiya mafi muhimmanci ga Sinawa, kowa na cikin farin ciki da annashuwa. Sabo da haka, ko da yake watakila masu sauraronmu ba ku da al'adar yin wannan biki, amma dukan ma'aikatan sashen Hausa na rediyon kasar Sin muna son isar da gaisuwarmu ta musamman da walwala zuwa gare ku da iyalanku duka.

Wannan biki na yanayin bazara na da muhimmanci sosai ga Sinawa, wato bisa kalandar gargajiya ta Sinawa, lokacin bikin lokaci ne da za a shiga sabuwar shekara ke nan.

Bikin yanayin bazara yana da dadadden tarihi a kasar Sin, wanda har tsawonsa ya kai shekaru fiye da 4000. Ban da wannan, Sinawa suna da dimbin al'adun gargajiya wajen murnar bikin yanayin bazara. Misali, a ran 23 ga wata na 12 bisa kalandar gargajiyar Sinawa, wato mako guda da ya rage a fara bikin bazara, sai aka fara share fagen bikin. Tun daga ran nan, daga birane zuwa karkara, jama'a su kan fara share dakunansu da wanke tufafi, don yin kawar da kazanta, ta yadda za a iya shiga sabuwar shekara cikin yanayi mai kyau. Sa'an nan, a kan sayi kayayyaki iri iri, musamman ma abinci masu dadi, don murnar bikin. Sai kuma ya zuwa ran 30 ga wata na 12, ko kuma mu ce jajiberen bikin yanayin bazara, an shiga wani mataki na koli na murnar bikin. Tun daga ran nan da yamma, jama'a su kan fara kayata gidajensu da zane-zane da fitilu masu launin ja, don nuna fatan alheri ga sabuwar shekara. A ran nan da dare kuma, iyalai su kan hadu a gu daya, su ci abinci tare, wanda ya kasance dina mafi muhimmanci ga Sinawa a ko ina a duniya a duk shekara, ana kuma kira wannan cin abinci tamkar dina na haduwar iyali. Sabo da a ganin Sinawa, ana aiki ne domin zaman alheri, to, amma idan iyalai ba su iya haduwa gu daya a jajiberen bikin bazara su ci abinci tare ba, to, abin takaici ne ke nan.

Bayan cin abincin, iyalai maza da mata, tsoffi da yara, su kan shakata da kide-kide da raye raye har lokacin da gari ya waye. Sa'an nan, yara su kan mika gaishe gaishe ga tsofaffi, kuma tsofaffi za su ba yara kudi, don yi musu fatan alheri su girma cikin koshin lafiya. A kan shafe kwanaki 15 ana bikin bazara, kuma a kan gudanar da shagulgula iri iri.

Wannan sabuwar shekarar da aka shiga ta kasance shekarar saniya, wanda ke da nasaba da al'adar musamman ta Sinawa ta kirga shekaru da dabbobi 12. Hasali ma dai, akwai masu sauraronmu da suka aiko mana wannan tambaya, kuma kamar yadda malama A'isha Salihu daga Maiduguri, jihar Borno, ta ce a cikin sakonta, "Sinawa na amfani da dabbobi wurin kirga shekaru, to, shin shekarar 2009 shekara ce ta wace dabba?"

Dabbobi 12 ne ake amfani da su a wajen kirga shekara a kasar Sin, wato su ne bera da saniya da damisa da zomo da dragon da maciji da doki da dai sauransu. Game da asalin wannan hanyar da ake bi ta kirga shekaru da sunayen dabbobi, akwai bayanai da yawa. Wasu sun ce, shi sakamako ne da aka samu daga wajen hada hanyar da al'ummar kasar Sin ta zamanin da ke bi wajen kirga shekaru da kuma hanyar da kananan kabilun kasar suke bi ta yin amfani da sunayen dabbobi wajen kirga shekaru. Wasu kuma suna ganin cewa, an shigo da wannan al'ada ne daga kasar Indiya. A kalla dai, jama'ar kasar Sin sun soma kirga lokatu na duk yini ne daga zamanin daular Han, wato a karni na uku kafin haihuwar Annabi Isa, (A.S), kuma A lokacin, akwai wani babban malami mai suna Wang Chong, wanda ya yi bayani a kan dabbobin nan 12 da ake amfani da su a wajen kirga lokatai. Game da yadda aka zabi dabbobin nan da kuma jera su, akwai wani bayani da ke nuni da cewa, an zabi wadannan dabbobi da kuma yi musu layi ne bisa ka'idojin aikace-aikacensu a kowace rana. An ce, daga karfe 11 na dare zuwa karfe daya na asuba, lokaci ne da beraye ke fitowa fili sosai, shi ya sa aka sa su a matsayi na farko. Sa'an nan, ta wannan hanyar ne aka jera sauran dabbobi, misali, daga karfe 7 zuwa karfe 9 na dare, kare ya kan soma aikinsa na tsaro, shi ya sa an jera shi a matsayi na 11. Daga baya, an kuma fara amfani da wannan dabara a wajen kirga shekaru, kuma ana zagaya duk dabbobin sau daya cikin shekaru 12.

Ga shi, tun daga ran 26 ga wata, muka shiga shekarar saniya, kuma dukan yaran da aka haife su a shekarar, a kan ce, saniya ce za ta alamanta shekarunsu na haihuwa.

Ba shakka, wannan shekarar saniya za ta kasance shekarar da ke cike da alheri a gare mu, sabo da kusan a duk duniya, ana daukar saniya a matsayin dabbar da ke kawo wa jama'a alheri. Kamar yadda wani mai sauraronmu ya fada a cikin sakonsa, wato Husseinistan Lawal Yakubu, da ya ce, "A madadin kaina da fahimta ta kuma a matsayina na BAHAUSHE kuma MUSULMI, zan taya Sinawa murnar shekarar saniya, wadda a fahimtata kuma amusulunce, tana nufin shekarar albarka, domin haka ALLAH Ya fada a cikin AL-QUR'ANI mai tsarki,wato ita saniya albarka ce don tana nuni da albarka. Wannan ma tun a zamanin annabi yusuf(joseph)A.S. kafin zuwan ANNABINMU (SAW), kuma har duniya ta nade ita saniya alama ce ta albarka."

Da fatan saniyar bana ta Sinawa za ta kawo wa jama'ar duniya albarka da alheri. Akwai kuma Shehu Abdullahi Dandume, daga Funtua, jihar Katsina, tarayyar Nijeriya, wanda ya aiko mana wasikar da ke cewa, "Ina mai farin cikin ganin Sinawa a cikin akwatin telebijin suna komawa garuruwansu kamar yadda muke zuwa gida a karshen shekara don bukin salla. Wannan shekara shekara ce ta shanu, shanu kuwa na da kirari kamar haka, nagge dadi goma dadi, Allah ya albarkace mu a cikin wannan shekara."

Bayan haka, mun kuma sami sakonnin masu sauraronmu da suka taya mu murnar shiga sabuwar shekara ta saniya, kamar dai Shugaba Abdullahi Baji na Mobaji Radio Club ya ce, "mu 'yan Mobaji Radio Club Muna taya dukan ma'aikatan sashen Hausa murnar shiga sabuwar shekara ta Sinawa da dukan jama'ar kasar Sin baki daya." Kuma Mamane Ada daga Yamai, jamhuriyar Nijer ya aiko mana wasikar da ke cewa, "wannan al'ada ta ku kun fi ba ta mahimmanci, kuma ina tayaku murna da kuma yi maku fatan alheri."

Dukan ma'aikatan sashen Hausa na rediyon kasar Sin, muna sake mika fatan alheri da gaisuwarmu ta musamman ta shiga sabuwar shekara ta saniya zuwa ga masu sauraronmu da iyalanku baki daya, da fatan Allah ya sa mu ga karshenta lafiya, ya kuma ba mu dukan alheran da ke cikinta. (Lubabatu)