Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-02-18 17:49:52    
Ziyarar da shugaba Hu Jintao ya kai wa kasashe 5 na Asiya da Afirka ta haifar da sakamako da yawa

cri
Ran 17 ga wata, shugaba Hu Jintao na kasar Sin ya kammala ziyarar aikin da ya yi a kasashen Saudiya da Mali da Senegal da Tanzania da kuma Mauritius. A kan hanyar Mr. Hu ta dawowa kasar Sin, Yang Jiechi, ministan harkokin waje na kasar Sin da ya raka Mr. Hu ya nuna wa 'yan jarida cewa, ziyarar da shugaba Hu ya yi a wannan karo tamkar wani muhimmin matakin diplomasiyya ne da kasar Sin ta dauka domin inganta dangantaka a tsakaninta da kasashe masu tasowa a sabon halin da ake ciki. Ziyararsa ta sami sakamako da yawa.

Mr. Yang ya bayyana cewa, bisa ajandar ziyararsa da aka tsara, a cikin kwanaki 7 kawai shugaba Hu ya halarci harkoki fiye da 50, wadanda suka hada da ganawa da dama tare da shugabannin kasashen da ya kai musu ziyara da kuma tuntubar mutane na rukunoni daban daban na wadannan kasashe. An sami sakamako da yawa a sakamakon yin mu'amala sosai.

Da farko, bangarorin da abin ya shafa sun sami sabon ra'ayi daya kan tinkarar matsalar hada-hadar kudi ta duniya tare. A lokacin ziyararsa, shugaba Hu ya yi cikakken bayani kan ra'ayi da matsayin kasar Sin game da tinkarar matsalar. Ya kuma nuna cewa, kasar Sin tana son inganta hada kai da kasashen duniya da suka hada da kasashe masu tasowa domin daukar matakai tare. Ban da wannan kuma, shugaba Hu ya nuna goyon baya ga bai wa kasashe masu tasowa karin wakilci da ikon bayyana ra'ayoyinsu a kan batun yin gyare-gyare kan tsarin kudi na duniya, ya kuma yi kira ga kasashen duniya da su taimaka wa kasashe masu tasowa, musamman ma kasashen Afirka domin jure wahala. Sa'an nan kuma, ya yi alkawarin cewa, kasar Sin za ta aiwatar da matakan mara wa Afirka baya da aka tabbatar da su a taron koli na Beijing na dandalin tattaunawar yin hadin gwiwa a tsakanin Sin da Afirka. Za ta yi iyakancin kokari domin ci gaba da bai wa Afirka karin taimako da yafe musu basussuka, da kara yin ciniki da zuba jari ga Afirka da inganta hadin gwiwa a tsakaninta da Afirka. Shugabannin kasashen 5 dukkansu sun nuna babban yabo kan bayanin da shugaba Hu ya yi.

Na biyu kuma, wannan ziyara ta raya dangantaka a tsakanin Sin da kasashen Asiya da Afirka zuwa sabon mataki. Mr. Yang ya nuna cewa, a cikin kasashe 5 da shugaba Hu ya kai musu ziyara a wannan karo, akwai kasashe 4 na Afirka. A cikin jawabinsa a Tanzania, shugaba Hu ya bayyana ra'ayi kan raya dangantaka a tsakanin Sin da Afirka a fannoni 6 a sabon hali, inda kuma ya jaddada cewa, ko a can da da kuma yanzu har ma zuwa nan gaba, jama'ar Sin na darajanta zumunci mai danko a tsakaninsu da jama'ar Afirka. Har kullum suna mayar da jama'ar Afirka tamkar abokan arziki da suke iya gaskata su sosai. Kasar Sin tana son gama kai da Afirka wajen ciyar da dangantakar abokantaka ta sabon salo a tsakaninsu bisa manyan tsare-tsare yadda ya kamata.

Na uku kuma, dukkan kasashe 5 da shugaba Hu ya kai ziyara kasashe ne masu tasowa. Kasar Sin ta zurfafa hadin gwiwa tare da wadannan kasashe a fannoni daban daban a sakamakon wannan ziyara. A lokacin ziyarar shugaba Hu, kasar Sin da wadannan kasashe 5 sun daddale yarjejeniyoyi fiye da 20 kan yin hadin gwiwa, ta haka sun kara zurfafa da habaka fannonin yin hadin gwiwa a tsakaninsu. Sa'an nan kuma, shugaba Hu ya yi rangadin aiki da kansa domin dudduba wasu ayyukan ba da taimako da kasar Sin ke yi domin aiwatar da sakamakon da aka samu a gun taron koli na Beijing.

Na hudu kuwa, wasu abubuwan musamman da suka faru a kan hanyar shugaba Hu a wannan karo sun jawo hankali sosai, sun kuma nuna cewa, zumunci a tsakanin jama'ar Sin da Saudiya da kuma Afirka sun shiga zukatan mutane sosai. Jama'ar wadannan kasashe 5 sun zura ido kan ziyarar shugaba Hu, sun kuma nuna masa marhabin da hannu biyu biyu. Shugaba Hu ya shiga a tsakanin jama'ar kasashen 5, ya yi mu'amala da su a filin jirgin sama da dakin taro da filin wasa da wuraren gine-gine da asibiti da dakin karatu, inda aka samu abubuwa da yawa da suka burge mutane.(Tasallah)