Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-02-18 15:30:32    
"Bari mu kara shigar da zumunci cikin zukatan jama'ar Sin da Afirka", in ji shugaba Hu Jintao

cri
A ranar 17 ga watan Faburairu, Hu Jintao, shugaban kasar Sin, ya gama rangadinsa kan kasashen Asiya da na Afirka 5, inda ake da nufin sada zumunci da inganta hadin kai. Sa'an nan ya bar Port Louis,hedikwatar kasar Mauritius, ya kama hanyar zuwa gida. Haka kuma, kafin dawowarsa, zango na karshe na rangadinsa shi ne cibiyar al'adun kasar Sin da ke kasar Mauritius, inda ajandar ta nuna muhimmancin da gwamnatin kasar Sin ta dora wa aikin musanya al'adu tsakanin Sin da Afirka.

"Ana ganin tabkin Xihu kamar kyakkyawar mace, kome kwaliya ko ado za su kara kayatarwa." Jimlar na daga cikin wakar da wani shahararren mawaka na kasar Sin ya rubuta, a shekaru kimanin dubu daya da suka wuce.Kuma abin da daliban ke karantawa ke nan,cikin cibiyar al'adun kasar Sin da ke Port Louis na kasar Mauritius. Cibiyar, inda shugaba Hu na kasar Sin ya kai ziyara, ta kasance cibiyar al'adu ta farko da kasar Sin ta kafa a ketare, a shekaru 20 da wani abu da suka wuce. A wurin ana samun azuzukan koyar da Sinanci, da rawa, da fasahar Kongfu, inda mailamai masu kwarewa ke kula da aikin koyarwa. Cikin ajin koyon Sinanci, shugaba Hu ya yi hira da wata 'yar Indiya ko Pakistan mai suna Mulan.

Shugaba Hu ya tambayi Mulan kan shekaru nawa take koyon yaren Sin,kuma iko yaya take ji a rai,yayin da Mulan ta amsa cewa, ta yi shekaru 4 tana koyon Sinanci, kuma abun ya ba ta jin dadi, da canza zaman rayuwarta. Domin ta samu sanin mijinta a kasar Sin, sa'an nan ta shiga aikin koyar da yaren Sin a kasar Mauritius.

Daliban sun ce, koyon yaren Sin ya ba su damar mua'mala da Sinawa kai tsaye. Wani daga cikinsu ya yi wa shugaba Hu bayani kan abubuwan da ya gani yayin da yake kallon wasannin Olympics a Beijing. Jin hakan ya sa shugaba Hu farin ciki, ya ce,

"Kwarewar da kuka samu ta ba mu damar kara musanya ra'ayoyinmu. Ina muku maraba da zuwa kasar Sin."

Bayan haka, shugaba Hu ya shiga ajin Kongfu, ya yi kallon nune-nunen fasaha da daliban suka yi.Sa'an nan ya ce,

"Nune-nunenku sun burge ni sosai.A hakika, koyon fasahar Kongfu da kuke yi, da farko,zai taimaka wajen inganta lafiyar jiki, na biyu,zai sa a kara sanin al'adun Sin, na uku, zai inganta zumunci a tsakanin jama'ar kasashenmu 2. Na gode muku kwarai."

Daga baya,shugaba Hu ya kai rangadi a ajin koyon fasashar rawa, inda daliban ajin suka nuna wani shirin rawa mai suna 'lokacin da furanni suka sheki'. Bayan da ya yi kallon nunin rawar, shugaba Hu ya yi hira da daliban, kuma ya tambaye su kan raye-raye na wadanne kabilun Sin aka taba koya, yayin da daliban suka amsa da cewa,

"Akwai raye-raye na kabilun Dai, da Yi, da Wa, da Tibet" shugaba Hu ya kara da tambaya 'ko akwai rawar kabilar Mongoliya',sa'an nan ya dan nuna yadda ake rawar mongoliya, hakan ya samu tafi da yawa.

Cikin rangadin da shugaba Hu ya yi, ya yi jawabi a kasar Tanzania kan yadda za a inganta zumunci tsakanin Sin da Afirka, haka kuma ya nanata kan habaka mua'mala, da karfafa hadin gwiwa a fannin ilimi da al'adu. Ya ce,

"Raya dangantakar tsakanin Sin da Afirka, makasudin aikin shi ne amfana wa jama'armu. Muna so mu kara hada kai da kasashen Afirka a fannonin al'adu, da ilimi, da kiwon lafiya, da wasanni, da yawon shakatawa, da dai sauransu, ta yadda za mu kara shigar da zumunci cikin zukatan jama'armu."(Bello Wang)