Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-02-18 14:10:47    
Shawarwarin shimdida zaman lafiya a Darfur na yin tafiyar hawainiya

cri

Aminai 'yan Afrika, ko kuna sane da cewa, a ranar 17 ga wata, a birnin Doha na kasar Qatar, wakilan gwamnatin Sudan da na kungiyar 'yan tawaye mafi karfi dake yankin Darfur na kudancin kasar sun rattaba hannu kan wata yarjejeniyar manyan tsare-tsare don tabbatar da samun sulhu tsakaninsu duk bisa kokarin shiga tsakani da kasa da kasa suka yi. Ra'ayoyin bainal jama'a sun yi hasashen cewa, daddale wannan yarjejeniya da suka yi ya shaida cewa, har ila yau dai shawarwarin shimfida zaman lafiya a Darfur na yin tafiyar hawainiya duk da kasancewar matsalolin da ake fama da su.

An labarta cewa, tawagar gwamnatin Sudan dake karkashin jagorancin mashawarcin shugaban kasar Sudan, Nafi Ali Nafi da tawagar 'yan tawaye mafi karfi da ake kira ' Harkar Neman Adalci da Zaman Daidaici' wadda Kahlil Ibrahim ke shugabanta son soma shawarwari tsakaninsu tun daga ran 10 ga wata. Bayan da suka shafe kwanaki 7 suna ta yin tattaunawa tsakaninsu, sai suka amince da rattaba hannu kanyarjejeniya ta manyan tsare-tsare don kawo karshen yakin da ya ki ci ya ki cinyewa a yankin na Darfur. A cikin yarjejeniyar, bangarorin biyu suk yi alkawarin soma shawarwari na mataki na biyu nan da watanni uku masu zuwa.

' Harkar Neman Adalci da Zaman Daidaici', wata muhimmiyar kungiya ce dake yin adawa da gwamatin Sudan, wadda kuma ta sha yin gumurzu tare da gwamnatin kasar. Saboda haka, gwamnatin Sudan ta bada umurnin cafke jagoran wannan kungiya Kahlil Ibrahim. Har kullum wannan kungiya tana kin yin shawarwari tare da gwamnatin kasar. A watan Mayu na shekarar 2006, gwamnatin Sudan da wata kungiyar daban mai adawa da gwamnatin kasar da ake kira 'kungiyar sojojin 'yantar da jama'ar Sudan' sun rattaba hannu kan ' Yarjejeniyar shmfida zaman lafiya a Darfur' a kasar Nigeria. Amma kungiyar neman adalci da zaman daidaici ta ki sa hannu kan yarjejeniyar bisa dalilin cewa ba a cimma burinta ; Ban da wannan kuma, gwamnatin Sudan ta taba yin shawarwarin shimfida zaman lafiya tare da masu yin adawa a kasar Libya, amma kungiyar neman adalci da zaman daidai ba ta halarci shawarwarin ba. Saboda haka, ra'ayoyin bainal jama'a sun dauka cewa, daddale yarjejeniya da aka yi a wannan gami tsakanin gwamnatin Sudan da kungiyar neman adalci da zaman daidaici na da muhimmiyar ma'ana ga ingiza yunkurin shimfida zaman lafiya a yankin Darfur. Khalil Ibrahim shi ma ya shiga shawarwarin.

Amma duk da haka, akwai doguwar tafiya da za a bi wajen daidaita batun Darfur a karshe yayin da ake samun wasu matsaloli a gun shawarwarin, domin da farko, kungiyar neman adalci da zaman daidaici ita kadai ta shiga shawarwarin da aka yi a wannan gami, wato ke nan sauran kungiyoyi masu yin adawa da gwamatin kasar ba su samu shiga shawarwarin ba. Wata muhimmiyar magana da har yanzu ke kasancewa a gun shawarwarin shimfida zaman lafiya a yankin Darfur ita ce neman sauran kungiyoyi masu yin adawa da su dawo kan teburin shawarwari. An labarta cewa, jim kadan bayan da aka daddale yarjejeniyar zaman lafiya a wannan gami, sai nan da nan mai shiga tsakani na yunkurin shiimfida zaman lafiya a Darfur Mr. Djibril Bassole, wanda Majalisar Dinkun Duniya da kuma kungiyar tarayyar Afrika, AU suka nada shi ya jaddada musamman cewa, zai tuntubi sauran kungiyoyin 'yan tawayen da ba sa ga maciji da gwamnatin kasar da zummar shawo kansu da su shiga shawarwarin ,ta yadda za a tabbatar da samun zaman lafiya mai dorewa a kasar Sudan.

Ban da wannan kuma, An gudanar da wannan shawarwari ne ba da sauki ba domin tun da farko bangarorin biyu sun yarda da sa hannu kan yarjejeniyar amincewa juna kawai duk da kokarin da kasar Qatar mai shiga tsakani ta yi na fatan za su rattaba hannu kan yarjejeniyar tsagaita bude wuta ; Sai dai a rana ta karshe ta shawarwarin ce suka amince da daddale yarjejeniya ta manyan tsare-tsare. Wannan dai ya shaida cewa, ya kasance da bmbancin ra'ayi tsakanin bangarorin biyu a kan wasu takamaiman batutuwan da suka shafi shirin tsagaita wuta. ( Sani Wang )