Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-02-17 16:54:51    
Sin da Afirka za su kasance aminai har abada

cri
"Kasar Sin za ta kasance kamar aminiyar jama'ar Afirka har abada." Shugaba Hu Jintao na kasar Sin ya fadi haka ne kan dangantakar da ke tsakanin Sin da Afirka lokacin da yake yin jawabi a Dares Salaam, babban birnin kasar Tanzania a ran 16 ga wata da safe bisa agogon wurin. A farkon sabuwar shekara ta 2009 bisa kalandar gargajiya ta kasar Sin, shugaba Hu Jintao ya je kasashen Mali da Senegal da Tanzania da kuma Mauritius don kaddamar da ziyararsa ta farko a sabuwar shekara. Kuma ta wannan ziyara da ake kiranta "Ziyarar hadin gwiwa ta karfafa zumunci", an iya gano cewa, lalle ana yin hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka ne a fannoni da matakai daban daban, kuma jama'ar Sin da jama'ar Afirka su aminai ne da ke nuna amincewa ga juna sosai.

"Aminai" wani takaitaccen bayani ne kan tarihin sada zumunci tsakanin Sin da Afirka.

Dankon zumunci tsakanin Sin da Afirka na da dogon tarihi. Yau da shekaru 30 da suka gabata, nagartattun Sinawa dubu 50 sun hada gwiwa tare da jama'ar Tanzania da Zambia sun haye dimbin wahalhalu wajen shimfida wata hanyar dogo da ta ratsa gabashin Afirka da kudu maso tsakiyar Afirka. Wannan hanyar dogo wata kyakkyawar shaida ce ta dankon zumuncin da jama'ar Sin suka nuna wa jama'ar Afirka.

Haka kuma a shekaru da dama da suka gabata, har kullum kasashen Afirka su kan nuna goyon baya ga kasar Sin a kan al'amuran da ke da nasaba da babbar moriyar kasar Sin, wanda kuma ya shaida amincin da jama'ar Afirka suka nuna wa jama'ar kasar Sin. A ran 25 ga watan Oktoba na shekara ta 1971, babban taro a karo na 26 na MDD ya zartas da daftarin kudurin mayar da kujerar Jamhuriyar Jama'ar Kasar Sin a cikin MDD, an samu wannan kyakkyawan sakamako ne sakamakon goyon bayan dimbin kasashen Afirka da Asiya da kuma Latin Amurka.

Domin irin wannan goyon bayan da su kan nuna wa juna da kuma hadin gwiwa tsakaninsu cikin dogon lokaci, an kulla dangankar 'yan uwantaka tsakanin Sin da Afirka.

A yayin taron koli na Beijing na dandalin tattaunawa tsakanin Sin da Afirka da aka kira a shekara ta 2006, Sin da Afirka sun tabbatar da raya dangantakar abokantaka ta sabon salo bisa manyan tsare-tsare, wato yin zama daidai wa daida da samun amincewar juna a fannin siyasa, da hadin gwiwa a fannin tattalin arziki don samun nasara tare, da kuma yin cudanya kana da koyi da juna a fannin al'adu. Ban da wannan kuma shugaba Hu Jintao ya sanar da matakai 8 da kasar Sin za ta dauka wajen goyon bayan bunkasuwar Afirka. A shekaru biyu da suka gabata, ana aiwatar da wadannan matakai 8 yadda ya kamata, kuma an riga an samu kyawawan sakamako.

Ban da wannan kuma, "Aminai" ya shaida alhakin da kasar Sin ke dauka a kanta a matsayinta na wata babbar kasa.

Yanzu matsalar kudi tana ta samun yaduwa a duk duniya. Sakamakon haka, wasu kasashe sun rage yawan taimakon da za su bai wa Afirka, haka kuma sun dakatar da ayyukan tallafawa Afirka da suka yi alkawarin yinsu a da. Shekarar bana shekara ce ta karshe da kasar Sin ke aiwatar da matakai 8 na tallafawa Afirka. Yaya kasar Sin za ta yi kan batun a cikin wannan hali mai tsanani da ake ciki yanzu?

Game da wannan, shugaba Hu Jintao ya nanata cewa, idan hadu da yawan karuwar wahalhalu, sai a kara yawan goyon baya da hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka domin haye wahalhalun. A matsayinta na sahihiyar aminiyar Afirka, kasar Sin za ta aiwatar da matakan tallafawa Afirka daban daban a tsanake da aka tabbatar da su a gun taron koli na Beijing domin ci gaba da kara samar da taimako ga Afirka bisa karfinta, da soke yawan basussukan da ake bin Afirka, da kara yin cinikayya da zuba jari a Afirka, da kuma inganta hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka a hakikanin fannoni.(Kande Gao)