Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-02-16 18:38:18    
Sin da Afirka suna kokarin bude sabon shafi na sada zumunci mai danko a tsakaninsu

cri
Ran 16 ga wata, a birnin Dares Salaam, hedkwatar kasar Tanzania, shugaba Hu Jintao na kasar Sin ya halarci babban taron yin marhabi da shi da rukunnoni daban daban na Tanzania suka shirya. A yayin taron, shugaba Hu ya yi wani muhimmin jawabi kan dangantaka a tsakanin Sin da Afirka, inda ya jaddada cewa, ko a can da da kuma yanzu har kuma nan gaba, jama'ar Sin na sa muhimmanci kan zumuncin gargajiya a tsakaninsu da ta Afirka. Har kullum suna mayar da jama'ar Afirka abokai ne da suka iya gaskata da su kuma yi dogaro da su daga dukkan fannoni, za su mayar da su tamkar 'yan uwa da aminai har abada.

A cikin wannan jawabi mai lakabi haka 'a yi kokari domin bude sabon shafi na sada zumunci mai danko a tsakanin Sin da Afirka', Mr. Hu Jintao ya waiwayi zumuncin da ke tsakanin Sin da Afirka a cikin shekaru fiye da 50 da suka wuce. Sa'an nan kuma, a gun taron koli na Beijing na dandalin tattaunawar yin hadin gwiwa a tsakanin Sin da Afirka a shekarar 2006, shugabannin Sin da Afirka sun tabbatar da kafa dangantakar abokantaka ta sabon salo a tsakaninsu bisa manyan tsare-tsare, wato yin zaman daidai wa daida da amincewa da juna a siyasa, da yin hadin gwiwa domin samun nasara tare a fannin tattalin arziki, da kuma yin mu'amala da yin koyi da juna a fannin al'adu. Ta haka sun bude sabon shafi na raya dangantaka a tsakaninsu. Bayan taron kolin, gwamnatin Sin ta karfafa yin hadin gwiwa da Afirka a hakikakan fannoni, ta aiwatar da matakai 8 na nuna wa kasashen Afirka goyon baya wajen samun ci gaba, wadanda suka kawo wa jama'ar Afirka alheri sosai. Dan haka an sami makoma mai kyau wajen yin hadin gwiwa a tsakanin Sin da Afirka.

Shugaba Hu ya kuma kara da cewa, a halin yanzu da matsalar hada-hadar kudi ta addabar duk duniya, kasashe masu tasowa sun fi kasancewa cikin matsayi maras kyau. Shi ya sa a cikin irin wannan mawuyacin hali, Sin da Afirka suna bukatar kara mara wa juna baya da hada kansu sosai domin warware matsalolin da suke fuskanta.

Shugaba Hu ya nuna cewa, kasar Sin tana son inganta hadin gwiwa tare da kasashen Afirka a fannoni 6. Da farko, kasar Sin za ta kara hada kai da kasashen Afirka domin taimakawa juna wajen tinkarar kalubalen da matsalar hada-hadar kudi ta duniya ke kawo musu. Na biyu, kasar Sin tana son kyautata amincewa da juna a tsakaninta da kasashen Afirka a harkokin siyasa da kuma inganta harsashi ta fuskar siyasa da Sin da Afirka suka aza domin sada zumuncin gargajiya a tsakaninsu. Na uku kuma, kasar Sin tana son ci gaba da daga matsayin yin hadin gwiwa tare da Afirka a hakikakan fannonin tattalin arziki da ciniki. Na hudu, kasar Sin tana son habaka yin mu'amala a tsakaninta da Afirka domin zurfafa hadin gwiwa a tsakaninsu kan al'adun mutane. Sa'an nan na biyar, kasar Sin tana son tuntubar kasashen Afirka sosai domin inganta batun taimakawa juna a kan al'amuran duniya. Na shida kuwa, kasar Sin tana son kara hada kai da Afirka domin ciyar da aikin kafa dandalin tattaunawar yin hadin gwiwa a tsakanin Sin da Afirka gaba, ta haka za a iya yayata rawar da dandalin ke takawa, wato ba da jagoranci ta fuskar siyasa kan bunkasa dangantaka a tsakanin Sin da Afirka.

Kazalika kuma, shugaba Hu ya yi nuni da cewa, yau Sin da Afirka sun kulla dangantakar aminci a tsakaninsu a sakamakon zuriyoyinsu da suka yi kokari tare. Nan gaba matasa na Sin da Afirka za su dauki nauyin ci gaba da raya irin wannan kyakkyawar dangantaka. Ya ce, gwamnatin Sin ta tsai da kudurin gayyatar matasa dalibai 50 'yan Tanzania da su kawo wa kasar Sin ziyara a shekarar da muke ciki. Kasar Sin za ta gama kanta da kasashen Afirka domin ci gaba da sa kaimi da kuma nuna goyon baya sosai ga matasa na Sin da Afirka da su yi mu'amala da hadin gwiwa a tsakaninsu.

A karshen jawabinsa, cikin sahihanci ne shugaba Hu ya yi wa mahalarta taron fiye da 1200 da suka hada da takwaransa na Tanzania Jakaya Kikwete da sauran jami'an Tanzania bayani da cewa, kasar Sin tana son hada kanta da kasashen Afirka wajen yin kokarin raya dangantakar aminci ta sabon salo a tsakaninsu bisa manyan tsare-tsare, ta haka za su iya bude sabon shafi na kyautata zumunci a tsakaninsu tare.(Tasallah)