Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-02-16 16:37:05    
Shugaba Hu Jintao ya halarci bikin kammala aikin gina filin wasa na kasar Tanzania, wanda kasar Sin ta bayar da taimakon kudin gina sa

cri
A ranar 15 ga wata, shugaban kasar Sin Hu Jintao, da takwaransa na kasar Tanzania Jakaya Kikwete sun halarci bikin kammala aikin gina filin wasa na kasar Tanzania, wanda kasar Sin ta bayar da taimakon kudin gina sa.

A cikin shawarwarin da aka kammala a ranar 15 ga wata da safe, shugaba Hu Jintao da shugaba Kikwete sun samu ra'ayi iri daya kan inganta zumunci na al'ada, da zurfafa hakikanin hadin kai, da kuma kai dangantakar abokantaka ta hadin gwiwa a tsakanin kasashen biyu zuwa wani sabon matsayi. Bayan shawarwarin ba da dadewa ba, shugabannin kasashen biyu sun halarci bikin kammala aikin gina filin wasa na kasar Tanzania.

Filin wasa na kasar Tanzania, wani aikin ne da ya fi girma da kasar Sin ta ba da taimakon gina sa bayan da aka shimfida hanyar dogo a tsakanin Tanzania da Zambia bisa tallafin da kasar Sin ta bayar. Wannan filin wasa na da sigar zamani, kuma na iya daukar 'yan kallo dubu shidu, na'urori na zamani da aka sanya a ciki suna iya biya bukatun shirya wasanni na Afrika, da wasannin na hadaddiyar kungiyar wasan kwallon kafa ta duniya, da na hadaddiyar kungiyar wasan tsalle-tsalle da guje-guje ta duniya. An soma gina wannan filin wasanni a watan Janairu na shekarar 2005, kuma an kammala shi a watan Disamba na shekarar 2008. Shi ne filin wasanni na zamani da ya fi girma a nahiyar Afrika. A gun bikin kammala aiki, a madadin gwamnati, da jama'ar kasar Tanzania, shugaba Kikwete ya nuna godiya ga jama'ar kasar Sin bisa taimako maras son zuci da suka bayar. Ya ce,

'Na yi alfahari da kasar Sin da jama'arta, Sin da jama'arta su samar mana da gaba. Sabo da babu wata kasa kamar kasarmu wadda ta mallaki filin wasanni na zamani kamar haka a yankin bakaken fata na Afrika, ko ma a nahiyar Afrika gaba daya.'

A shekarar 2008, ko da yake ba a kammala aikin gina wannan filin wasanni ba, amma kasar Tanzania ta riga ta shirya wasanni da yawa a nan, ciki har da gasar share fage ta wasannin kwallon kafa na cin kofin duniya, da ta kofin Afrika. Kungiyar 'yan wasa ta kasar Tanzania ta yi ta samu sakamako mai kyau a nan, haka kuma, jama'ar kasar Tanzania suna kaunar wannan filin wasanni sosai.

A gun bikin kammala aiki da aka shirya a ranar 15 ga wata, shugaba Hu Jintao ya bayyana cewa, filin wasanni na kasar Tanzania sakamako ne na zumunci al'ada tsakanin 'yan uwa na Sin da Tanzania. Tun bayan da aka kulla huldar diplomasiya, kasashen biyu Sin da Tanzania suna nuna goyon baya ga juna, da hada kai tare, ta yadda zumuncin da ke tsakanin jama'ar kasashen biyu zai kara karfi. Bisa manufar zaman daidai wa daida da samun moriyar juna, da kuma samun bunkasuwa tare, kasar Sin tana sa himma domin hada kai tare da kasar Tanzania a fannoni daban daban, da kawo hakikanin moriya ga jama'ar kasashen biyu, lallai hadin kai na sada zumunci a tsakanin Sin da Tanzania abin koyi ne wajen hadin kai a tsakanin kudu da kudu. Ya ce,

'Kasar Sin za ta ci gaba da bayar da taimako ga kasar Tanzania bisa gwargwadonta, kazalika kuma tana nuna goyon bayan kasar Tanzania bisa kokarin da take yi wajen bunkasa tattalin arziki, da kyautata zaman rayuwar jama'a. Na yi imani cewa, a karkashin kokarin da bangarorin biyu suke yi tare, ko shakka babu za a samu sakamako mafi kyau kan hadin gwiwar sada zumunta tsakanin Sin da Tanzania, da kuma kawo alheri ga jama'ar kasashen biyu.'