Yau ne ran 4 ga watan farko bisa kalandar gargajiya ta kasar Sin. Kuma bisa al'adun gargajiya na Sin, a kan yi tafiya a kan tituna don sayen kayayyaki da kuma jin halin annashuwa na bikin bazara. To, da farko dai, ina son in taya ku masu sauraronmu fatan alheri, da kuma na takar sa'a a cikin sabuwar shekara. Daga baya kuma zan ja ku zuwa titin Niujie na birnin Beijing inda aka fi samun yawan musulmai domin ganin yadda musulmai na kasar Sin suke taya murnar wannan bikin bazara.
"Ko da yake bikin bazara ba bikin gargajiya ba ne na 'yan kabilar Hui masu bin addinin Musulunci, kuma halinsa na annashuwa bai iya kai na babbar salla ba, amma a matsayinsa na wani bikin gargajiya na al'ummar Sin, 'yan kabilar Hui mu ma mu kan sanya sabbin tufafi da sayen kayayyaki iri daban daban da kai ziyara ga abokai da iyali da kuma nuna wa juna gaisuwa don jin dadin bikin bazara." Ma Guoqiang da ke zaune a titin Niujie ya fadi haka ne lokacin da yake zantawa da wakilinmu. E, gaskiya ne, masu sauraro, a kan titin Niujie, mun ga dimbin 'yan kabilar Hui suna sanya sabbin tufafi da fararen huluna tare kuma da abinci da kayayyaki iri daban daban a cikin hannayensu. Haka kuma mun ji su fadi "Assalam" da kuma sauran nau'o'in gaisuwa ga juna, lalle suna jin dadin bikin bazara sosai.
Yayin da muke tafiya a kan titin Niujie, sai muka ga wani babban kantin cike da mutane, ashe wannan babban kantin farko ne na sayar da kayayyaki na musulmi a kan titin, sabo da kayayyakin da ake sayarwa a kantin na da halin musamman na musulmi sosai, shi ya sa ya samu karbuwa kwarai daga mazauna 'yan kabilar Hui na titin Niujie.
Ping Guodong, manaja na kantin ya gaya mana cewa, domin bikin bazara, kantin ya shigo da abinci da kayayyaki iri dabab daban don biyan bukatun mutane. Kuma ya gaya mana cewa,
"A 'yan kwanakin nan da suka gabata, dimbin musulmai da ke kashe kudade a Beijing da na sauran wurare na kasar Sin suna zuwa kantin musulmi na Niujie don sayen kayayyakin musulmi da suke so. Kantinmu ya shirya kayayyaki iri 4500 da ke da alamar Halal wadanda suke samun karbuwa sosai daga musulmai. Kuma a lokacin bikin bazara na shekarar da muke ciki, jimillar kudaden da kantin ya samu ta karu da kashi 10 cikin kashi dari bisa na shekarar da ta gabata, har ma mun samu kudin Sin wato Yuan fiye da dubu 56 a jiya."
Ma Qi da shekarunsa suka kai 30 da haihuwa wani musulmi ne da ke zaune a titin Niujie, ba da jimawa ba, ya sayi namun shannu da awaki da sauran abinci da darajarsu ta kai Yuan dari biyu daga kantin, kuma ta gaya mana cewa,
"Na fi son sayen abinci a wannan wuri, dalilin da ya sa haka shi ne sabo da da farko kantin ya yi kusa da gidana, na biyu shi ne sabo da kantin na musulmi ne sosai, mu musulmai muna iya kwantar da hankalinmu wajen sayen abinci."
E, gaskiya ne, kamar yadda Ma Qi ya ce, wannan kantin musulmi na sa muhimmanci sosai kan samar da kayayyakin musulmi ga masu kashe kudade. Manaja Ping Guodong ya kara da cewa,
"Kantin musulmi yana mai da hankali sosai kan zabar kayayyakin musulmai, har ma mu kan je masana'antun samar da kayayyakin don yin bincike kan cewa, kayayyakin na halal ne ko a'a. Sabo da haka dimbin musulmai masu kashe kudi suna nuna yabo ga kantinmu da cewa, sayen kayayyaki a kantin ba a bukatar zabarsu, sai dai a dauka kawai."
Masu sauraro, sakamakon kyautatuwar zaman rayuwar Sinawa, yawansu su kan zabi su ci abinci a dakunan cin abinci a lokacin bikin bazara. Sabo da haka domin biyan bukatun musulmai, dakunan cin abinci daban daban da ke titin Niujie su kan shirya abincin da ke da halin musamman na musulmi sosai. Hong Guanghua, manajar shahararren dakin cin abinci na musulmi da ake kiransa "Deshunlou" ta gaya mana cewa,
"A rana ta farko da ta uku da kuma ta hudu ta watan Janairu bisa kalandar gargajiya ta kasar Sin, muna bai wa baki waina a matsayin kyauta, dalilin da ya sa muke yin haka shi ne sabo da bisa al'adun gargajiya na kabilar Han, ma'anar cin waina a sabuwar shekara ita ce ana fatan za a iya samun babban ci gaba a sabuwar shekara. Ban da wannan kuma mu ma mun samar da 'Tangjuanguo' na kabilar Hui da ake yi da daddatsattsen dabino da doya da kuma sukari, domin fatan zaman rayuwar baki za su samu kayatarwa kamar sukari."
Masu sauraro, bisa al'adun gargajiya na al'ummar Sin, a kan ci Jiaozi, wani irin abinci ne da ko da yaushe a kan ci a jajibirin sabuwar shekara. Amma bisa al'adar gargajiya ta kabilar Hui ta kasar Sin, a kan ci Jiaozi a rana ta biyu ta watan farko bisa kalandar gargajiya ta Sin a maimakon jajibirin sabuwar shekara. Game da wannan al'ada, akwai wani labari mai ban sha'awa sosai. Wang Caiyue, wata ma'aikaciyar dakin cin abinci na Deshunlou ta gaya mana cewa,
"A zamanin da a kasar Sin, akwai wani Janar musulmi, a wani karo ya shugabanci sojoji don yaki da abokan gaba, amma sun gamu da cikas a jajibirin sabuwar shekara, shi ya sa mu musulmai ba mu sa muhimmanci sosai kan jajibirin sabuwar shekara ba. Daga baya kuma bayan da Janar ya ci Jiaozi a rana ta biyu ta watan farko, ya sake tada yaki da abokan gaba, kuma ya cimma nasara sosai. Domin bin wannan al'adar gargajiya ta kabilar Hui, mu musulmai mu kan ci Jiaozi a rana ta biyu ta watan, kuma a kan kira Jiaozi da suna 'Jiaozi masu kawo nasara'."
|