Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-02-12 17:04:46    
Za a inganta hadin kan kasar Sin da kasar Saudiyya don amfana wa jama'ar kasashen 2

cri

Ranar 11 ga watan Faburairu ta kasance rana ta 2 da Hu Jintao, shugaban kasar Sin, ke ziyarar aiki a kasar Saudiyya, kuma a ran nan, shugaba Hu ya yi rangadi kan wani aikin hadin kai a tsakanin kamfanoni da cibiyoyin binciken kimiyya na kasar Sin da bangaren Saudiyya.

A ran 11 da safe, jerin gwanon motocin shugaba Hu na kasar Sin ya kai wani wurin da ke da tazarar kilomita 75 daga yammacin birnin Riyadh, inda wani kamfanin gini na kasar Sin mai suna Sinoma ke gina wata ma'aikatar sarrafa garin siminti a can. Cikin dakin kula da harkokin ma'aikatar, shugaba Hu ya yi tambaya kan halin da ake ciki a wajen aiwatar da aikin gine-gine.

Kasashen gabas ta tsakiya na shigo da kayayyakin gine-gine da yawa daga kasahen waje, shi ya sa kasashen, ciki har da Saudiyya, suna mai da hankali sosai kan inganta fasaha, ta yadda za su iya kirkiro kayayyakin da kansu a nan gaba. Karkashin wannan halin ne, kamfanin Sinoma wanda ke da ci gaba kan fasaharsa ya kulla yarjejeniya da kasar Saudiyya kan shimfida nau'rorin sarrafa garin siminti 7, sa'an nan 5 daga cikinsu aka fara amfani da su. Bayan da aka kammala gina dukkan nau'rorin, yawan siminti da suke samarwa zai kai kashi 40% cikin dukkan simintin da ake samar da shi a kasar Saudiyya. Naseeruddin Siddiquie, mataimakin manajan kamfanin sarrafa siminti na Riyadh, wanda ya yi rakiya ga shugaba Hu a ziyarar, ya nuna yabo kan himma da kwazon da ma'aikata Sinawa suka nuna, inda ya ce ,

"Hadin gwiwarmu na tafiya lami lafiya.Yanzu shekaru 4 da muke hada hannayenmu, a hakika aikin ya riga ya zama abin koyi ga ayyukan sauran fannoni. Muna aiki tare kamar kungiya daya, wannan babban dalili ne da ya haifar da nasara."

Ban da wannan kuma, hadin gwiwar tsakanin Sin da Saudiyya ba ta tsaya kan cinikayya, da makamashi, da ayyukan gini, da zuba jari ba, har ma ta shafi fannin binciken kimiyya. A ranar 11ga watan Fabrairu, bayan da shugaba Hu ya yi rangadi a ma'aikatar sarrafa simintin, ya kuma kai ziyara ga wurin da bangarorin Sin da Saudiyya ke aikin hadin gwiwa na binciken irin dabino.

Dabino ya kasance amfanin gona mafi muhimmanci a gabas ta tsakiya da arewacin Afirka, kuma yawan dabinon da kasar Saudiyya ke samarwa ya kai kashi 15% cikin dabinon da da aka samu a duk duniya. Yanzu cibiyar binciken iri ta Beijing ta kasar Sin ta hada hannu da bangaren Saudiyya wajen aiwatar da aikin binciken irin dabino, wanda ya samu kudi da yawa daga gwamnatin Saudiyya, domin ya dace da manufar kasar Saudiyya ta inganta ilimin kimiyyar binciken halittu. Makasudin aikin shi ne neman samun kawar da cututtuka da kwari, da kyautata yanayin dabino, da kara yawan samar da dabino, ta hanyar binciken kwayoyin halin dabino. Tun daga shekarar bara, ma'aikata Sinawa 11 na jerin farko sun yi rabin shekara suna aiki a Saudiyya, bisa ajandar aikin da aka tsara ta shekaru 3, wato bayan shekaru 3 bangarorin 2 za su gabatar da sakamakon binciken kan yadda ake tsara kwayoyin dabino.

Bayan da shugaba Hu ya saurari bayanin da masu binciken kimiyya suka yi dangane da aikin, ya yi yabo kan kokarin aikin da suka nuna. Haka kuma ya yi magana kan hadin gwiwar da kasahen 2 suke yi, inda ya ce,

"Gwamnatin kasar Sin da gwamnatin Saudiyya dukkanmu na mai da hankali sosai kan raya kimiyya da fasaha, da hadin gwiwarmu a wannan fanni. Ina fata masu binciken kimiyya na kasashenmu 2 za su samu nasara kan aikin hadin gwiwarsu na binciken kwayoyin halin dabino, kuma ina fata kasashenmu 2 za mu kara hada hannu a fannin kimiyya da fasaha."(Bello Wang)