Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-02-12 17:29:55    
Labaru masu ban sha'awa na kasar Sin

cri
Tabarbarewar tattalin azrki ta haifar da illa ga aure.Bisa labarin da aka samu daga yanar gizo ta internet a wani shafinta cewa yawan ma'auratan da suka kashe aurensu sai karuwa suke a watannin baya bayan nan da suka shige. Madam Zhang Mei tayi aure da mijinta na tsawon shekaru sama da ashirin. Tana da kamfanoni da ma'aikata sama da metan. Ya zuwa yanzu takardun neman yin odar kayayyakin kamfaninta sun yi raguwa sosai sabo da tabarbarewar tattalin arziki na duniya.har ta kasa mun kudin da take bukata wajen tafiyar da harkokinta. Da ganin haka,mijinta ya yi fushi,ya fita waje,ya yi abin nasa. Aurensu ma ya mutu.

Wata mace ta samu rashin lafiya saboda ta sumba da masoyinta. Bisa wani labarin da aka buga a cikin jaridar Guangzhou daily ta kwanan baya, an ce wata mace ta kurma bayan da ta sumbata masoyoyinta a yankin Zhuhai na lardin Guangdong. Macen tana da shekaru sama da ashirin da haihuwa,yayin da take sumbata da masoyinta ta sume, sai nan da nan aka kai ta asibiti. Bayan da likitan ya yi mata bincike, ya gano cewa macen ta kurma ta kasa jin abubuwan da ake fada. Dalili kuwa shi ne yayin da take sumbata da masoyi,iskar dake cikin bakinta ta yi karanci ta kasa yin balas da iskar waje da kunnenta, wannan ya haddasa ta kasa jin abubuwa yadda ya kamata. Likitan ya ce wannan ba matsala ce mai tsananni ba, nan gaba za ta koma yadda ya kamata sabo da jikin mutum na iya daidaita shi da kansa.

Wani miji ya ki rabuwa da matarsa da jikinta ya shaye. Bisa labarin da aka buga a jaridar Dahe News ta lardin Henan dake tsakiyar kasar Sin kwanan baya, an ce matsayin da wani mijin ya dauka na kin rabuwa da matarsa wadda jikinta ta shanye ya girgiza zukatan mutanen kauyen Gengtang a cikin yankin Xinmi na lardin Henan.Matar da jikinta ya shanye tana neman yin rabuwa da mijinta saboda jikinta ya shanye a shekara ta 1972. ba ta so ta zama matsala ga mijinta. Amma mijin ya dage zama tare da ita ba ya so rabuwa. Sabo da haka mutane masu dimbin yawa suka yaba da matakin da ya dauka kan auratayya.

Wata mace mai kishin dabbobi ta yi hayar daki domin karnukanta guda hudu. Bisa labarin da aka buga a jaridar Dongfang Jinbao News ta lardin Henan kwanan baya, an ce an sami wata mace da take kula da karnukan da suka rasa gidajensu na zama a asirice cikin shekaru hudu da 'yan kai a birnin Zhengzhou, babban binin lardin Henan. Domin samar da daki mai kyau ga karnukan da ta tsinta a tituna, mace mai suna Bai ta yi hayar wani daki, kowace rana ta je dakin nan da keken hawa cikin minti goma ta ba su abinci da tsabtace dakin. A halin yanzu ta biya kudin dakin da ta yi haya da kudin Sin Yuan metan kowane wata. Ban da wannan kuma ta biya kudin wutar lantarki da na ruwan sha domin karnukan. Macen Bai ta bayyana cewa ta yi hayar daki ne ba domin mijinta da iyayenta suna son dabbobi ba. Da fatan samar da yanayi mai kyau na zama, Macen Bai tana fatan sauran masu kishin dabbobi da su dauki dabbobin da take tanada.

Wata mace ta yi wa wani saurayi zamba. Bisa labarin da aka buga a cikin jaridar Nanning evening News ta jihar Guangxi dake kudancin kasar Sin kwanan baya, an ce wani saurayi manomi ya kai karar wani ofishin kula da auratayya a gaban kotu sabo da ya kasa gano takardun jabu na wata mace har ya bayar da takardar shaida ta aure. Bayan da saurayi ya yi aure da macen, macen ta tsere daga gidansa tare da kudi mai yawan gaske. Sunan saurayi shi ne Huang yana da shekaru 27 da haihuwa, ya tarar da macen da ta yi masa zamba ne a ofishin kula da harkokin auratayya a shekarar bara. Bayan da macen ta dau alkwarin aure shi, saurayin ya mika daukacin kudin da ya ajiye a banki. Bayan da suka yi rajista a ofishin kula da harkokin auratayya na gwamnati, macen ta bace nan take.. Yayin da Mr Huang yake neman rabuwa da macen a kotun, kotun ta yi watsi da bukatunsa, dalili kuwa shi ne dukkan takardun da macen ta samar na jabu ne.Daga bisani Mr Huang ya kai ofishin kula da harkokin auratayya a gaban kotu saboda ta kasa gane takardun jabu na macen nan kwanakin baya kotun jama'a na Yankin Jiangna ta yanke hukunci cewa a dasa aya ga wannan auratayya.

Masu aiki a ofisi suna huce haushinsu ta sabbin hanyoyi. An samu wata sabuwar sana'a a nan birnin Beijing, babban birnin kasar Sin, wadda ta samar da kayayyakin wasa da makamantasu ga mutanen dake aiki a ofishinsu da aikin ya zama gagarbadau gare su,su yi wasa da wadannan kayayyaki yadda suka ga dama, kome su fasa su ko kuma su bata su,kuma su karya su, da akwai irin kayayyakin wasa da siffarsu ta yi kama da 'ya 'yan itatuwa,to da masu shiga suna wurin,suna iya matsa su har ma sun fita kamaninsu,jin kadan su koma yadda suke da farko. Wata mata dake aiki a ofisi ta ce ba na iya yin fushi da masu aiki tare da ni maimakon haka na zo shagon nan na bata kayan wasa yadda na ga dama,daga bisani hankalina ya kwanta.

Wani namiji da ya yi amfani da diyarsa wajen yin sata. An sami wani manomi a birnin Xi'an,babban birni na lardin Shaanxi na kasar Sin.shi da matarsa suka yi satar baskur a unguwa, dukkansu biyu suka sha kwayoyi,shi ya sa ba su da isashen kudin da ya biya bukatunsu,har ma sun shiga sata.amma ba su da gida a birnin, sukan shiga burtun 'yan birni suke tare da diya. Ta haka suka yi satar basukur sama da dari, duk da haka an kama su a yayin da suke cikin satar baskur, aka kai su ofishin caji, aka yi musu bincike. Daga baya kotu ta yanke musu hukunci.(Ali)