Sunan kwamandan din shi ne Liu Xiangyang,shi wani hafsa ne a rundunar soja ta kasar Sin,wani mataimakin shugaban rukunin sojoji ma'aikata na sashen sojoji na beijing,kuma mataimakin babban jagorar kungiyar ba da agaji ta duniya ta kasar Sin wajen ba da agaji.
Jama'a masu sauraro, muryar da kuka ji dazun nan,murya ce da muka samu yayin da kungiyar ba da agaji ta duniya ta kasar Sin ta yi atisayen ba da agaji a wani filin horaswa.A ran 12 ga watan Mayu na bana,an yi girgizar kasa mai tsananin digiri takwas bisa ma'aunin Richter a yankin Wenchuan na lardin Sichuan dake kudu maso yammacin kasar Sin. A kashegari da safe kungiyar ba da agaji ta kasa dake karkashin jagorancin Mr Liu Xiangyang ta gaggauta zuwa yankin da bala'in girgizar kasa ya wakana. A wurin da asibitin samar da maganin gargajiya na kasar Sin a birnin Dujiangyan na lardin Sichuan, kungiyar ba da agaji dake karkashin jagorancin Liu Xiangyang ta kubutar da wani mutum mai rai da buraguzan gidajen suka danna shi,wanda shi ne mutumin na farko da kungiyar ta fitar da shi daga hadari bayan da kungiyar ta yi gwagwarmaya cikin sa'o'I uku. Mutumin nan ya yi sa'ar samun fita daga hadari ba tare da samun launi mai tsanani ba saboda matakan daidaicin da kungiyar an ta dauka cikin lokaci. Mr Liu Xiangyang ya ce mutumta rayuka shi buri daya tak mai tsarki na kungiyar ba da agaji ta duniya ta kasar Sin.
" bayan da muka gano wani mutum da ke rai da buraguzan gini suka rufe shi,sai mu yi iyakacin kokarinmu wajen kubutar da shi daga hadari kome wahalar da muka sha a cikin yunkurin da muke yi,ko kusa ba tare da bata lokaci ba wajen fitar da shi,haka kuma ko kusa ba mu so ba ga wani mai rai ya rasa ransa yayin da muke kokarin cetonsa.Yayin da muke yunkurin ceton wadanda suke da rayuka,idan wani daga cikinsu ya mutu,a ganinmu mun aikata laifi."
A cikin kokarin ba da agajin da suka yi cikin gaggawa,'yan kungiyar sukan kamu da matsalolin da ba su taba gani ba a cikin atisayen da suka yi yau da kullum wadanda suka zama kalubale. A cikin yunkurin ceton wadanda bala'in girgizar kasa ya ritsar da su a daren ranar 13 ga watan Mayu a wurin kamfanin kera janaraita na gabas a garin Hanwang da ke yankin Wenchuan,nan take Mr Liu Xiangyang ya gano wata bakuwar hanyar ba da agaji,da haka ya warware matsalar da suka kamu da ita wajen kawar da barazanar ragargazar gidajen da aka rushe a cikin girgizar kasa da ta biyo bayan babbar girgizar kasa.Wannan dabarar da ya samo ta sami yabo daga masanin ilimin girgizar kasa na kasar Sin Mr Yi Guanghui.
"A wannan lokaci wasu kwararru na kamafanin suna karkashin burabugan gine gine,mun yi nazari tare don gano hanyoyoyin da za mu bi wajen ba da agaji,Mr Liu Xiangyang ya kawo shawarar shimfida hanyar dake da tsaro wajen ba da agaji,idan raguwar girgizar da ta biyo ta wakana,ko ma gine ginen da suka rushe sun sake ragargaza ba za su iya raunana 'yan kungiyarmu ta agaji ba,a sa'I daya kuma ta kawo kariya ga wadanda suke neman ceto. Sa'ad da mu ma'aikatan ba da agaji na kashe gobara da ba da taimako a hadarurrukan ramukan haka ma'adinai ke tattaunawa hanyoyoyin da za a bi wajen ba da taimako,muna masu ra'ayin cewa dabarar da Mr Liu Xiangyang ya kawo tana da amfani kwarai da gaske.A watan Afrila na shekara ta 2001 ne aka kafa kungiyar ba da agaji ta duniya ta kasar Sin.Kasar Sin ta makara wajen kafa kungiyar musamman ta ba da taimako a cikin aikin ceton wadanda da girgizar kasa ta rutsa da su,ita bakuwa ce a wannan fanni, ba ta da littattafan karatu a wannan fanni,da ma'aunin da suke amfani da shi,da fasahohin da suke bukata wajen ba da agaji.Mr Liu Xiangyang yana daya daga cikin ginshikan da suka kafa kungiyar ba da agaji ta kasar Sin.shi jami'I ne mai kula da harkokin horaswa na wannan kungiyar da tafiyar da harkokinta na yau da kullum.
Daga nan Mr Liu Xiangyang ya nace ga yin wasannin motsa jiki domin kara koshin lafiya da karo ilimin ba da agaji da samo fasahohin da suke bukata kuma ya yi koyi da harshen turanci. Ya kuma wallafa littafin da ke kunshe da bayanan da yake bukata a cikin aiki da na turanci,ya kana karanta su in ya sami dma. Ya kuma kan tuntuba masana da kwararru na kasar Sin da suka yi fiffiko a fannin girgizar kasa da ilimin kimiyya na kasa.Bisa jagorancin da kwararru na hukumar kula da harkokin girgizar kasa ta kasar Sin suka yi masa,Mr Liu Xiangyang ya shirya kwararrun da abin ya shafa wajen wallafa littattafan karatu guda sha daya game da ayyukan ba da agaji,ya cika gibin da ke akwai a kasar Sin na rashin littafi mai amfani a wannan fanni. Ban da wannan kuma kungiyar ba da agaji ta duniya ta kasar Sin ta horas da karnuka guda 12 da suka samu takardun shaida na manyan karnuka mafi amfani wajen ayyukan cigiya daga majalisar dinkin duniya,da haka kasar Sin ta kama gaba wajen horar da irin karnuka cikin lokaci guda,har wa yau dai karnukan da suka samu horo sun yi aiki yadda ya kamata ba su yi kuskure ba tukuna a cikin ayyukan ba da agaji. A cikin ayyukan sama da talatin da suka yi a kasashen ketare na karo ilimi da shiga gasa da atisaye,'yan kungiyar ba da agaji da Mr Liu Xiangyang ya yi mata jagora ta gano sabbin hanyoyin sama da goma na ba da agaji. Masanin ilimin kimiyyar girgizar kasa na kasar Sin Mr Yi Guanghui ya dauka cewa ana iya cewa Mr Liu Xiangyang wakili ne na kungiyar ba da agaji ta tuniya ta kasar Sin.
"Mr Liu Xiangyang ya gwammance nazarin ilimin fasahohin cigiya da ayyukan kungiyar ba da agaji da shirye shiryen da ta sa a gaba da kuma kayayyakin musamman da ake amfani da su wajen aikin ba da agaji. A cikin kokarin nazarin ilimi dangane da ba da agaji da ayyukan taimako da suka yi,Mr Liu Xiangyang ya kan kama gaba,ya ja ragamar sauran abokan aikinsa wajen yin aikin wurjanjan na ba da agaji,shi fitacen wakili ne na kungiyar ba da gaji ta duniya ta kasar Sin."
A cikin aikin ba da agaji da aka yi yayin da girgizar kasa ta wakana a kasar Aljeriya a shekara ta 2003, karo na farko ne da kungiyar ba da agaji ta shiga dandalin duniya na ba da taimako,kungiyar kasar Sin tana daya daga cikin kungiyoyi 38 na duniya da suka ba da agaji a yunkurin da aka yi wajen ba da taimako ga wadanda girgizar kasa ta ritsar da su a kasar Aljeriya.kuma tana daya daga cikin kungiyoyi biyu na duniya da aka tabbatar da su su ceci wadanda girgizar kasa ta ritsar da su. A cikin kokarin da aka yi na ba da taimako bayan tsunamar tekun Indonesia a shekara ta 2004, kungiyar ba da agaji ta duniya ta kasar Sin ta samu yabo mai yawan gske daga mutanen da suka sha wahalar bala'in saboda halin da suka nuna na hadin kan kasa da kasa da na jin kai. Da ya waiwayo aikin ba da agajin da kungiyar kasar Sin ta yi a kasar Pakistan a shekara ta 2005 bayan girgizar kasa ta wakana,Mr Liu Xiangyang ya ce kungiyar ba da agaji ta duniya ta kasar Sin tana daya daga cikin kungiyoyi 44 na duniya da suka isa wuri tun farko a kasar Pakistan. Bisa al'adar duniya, kungiyar ba da agaji ta farko da take da cikakkun bayanai na daidaici da kuma rawar da ta taka,cibiyar daidaituwa ta majalisar dinkin duniya ta mai da kungiyar kasar Sin kungiya mai daidai ayyukan ba da agaji tsakanin kungiyoyin ba da agaji na duniya.
Kwanaki biyu ke nan da muka isa kasar Pakistan bayan girgizar kasa,mutanen Pakistan ba su da abinci a wannan lokaci,duk da haka sun yi mana kirari cewa "da kyau sosai,kasar China", sun mika abincin da jiriginmu ya kawo musu ga 'yan kungiyarmu,sun kama hannayenmu sun rungume mu,lalle mun jiku kwarai da gaske. Mutanen sun yi dafifi a gefunan hanya sun yi mana maraba da hannu bibbiyu suna kirarin China,China.
Kamar yadda sauran 'yan kungiyar suke, Mr Liu Xiangyang shi ma ya kamu da matsaloli da dama a cikin ayyuka,cututtuka. Saboda atisayen da suka yi a dazuzzuka da duwatsu a lokacin sanyi da ceton mutanen da bala'in ya ritsar da su,wani sa'I ba su da lokacin yin barci,ba su iya cin abinci cikin lokaci,shi ya sa su kan fama da cututtuka kamar ciwon gabobbi da na ciwon ciki, gajiya da yunwa kamar abincinsu ne na yau da kullum. Mr Wei Qingfeng,wani dan kungiyar ba da agaji ta kasar Sin ne ya ce
"mutane da dama dake cikin kungiyarmu suna fama da ciwon ciki,ciwon tumbin da Mr Liu Xiangyang,shugabanmu ya ke fama da shi ya fi tsanani,duk da haka ya yi hakuri,ba ya so ya bayyana zafin ciwon cikin da ya ji ba. Wani lokaci yini daya ba ya ci abinci saboda aikin ceto,wani lokaci ya ci abinci na saukakke amma ya sadaur da kansa ga aikin ceton wadanda da bala'I ya ritsar da su."
|