Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-02-11 20:59:45    
Yawan CPI na kasar Sin ya cigaba da raguwa a watan Janairun shekarar bana

cri
Bisa alkaluman da hukumar kididdiga ta kasar Sin ta bayar a ranar 10 ga wata, an ce, a watan Janairu na shekarar da muke ciki, yawan CPI wato ma'aunin farashin kayayyakin da mazauna kasar suke saya ya karu da kashi 1 bisa dari idan an kwatanta da makamancin lokacin shekarar bara, wanda ya cigaba da raguwa a cikin jerin watanni 9. A waje guda kuma, farashin da ake amfani da shi na da bisa ma'aunan kayayyakin da masana'antu ke sarrafawa wato PPI ya sauka da kashi 3.3 bisa dari bisa na makamancin lokaci na shekarar bara. Kwararru sun bayyana cewa, ga alama tattalin arzikin kasar Sin na kara samun matsin lamba, amma hakan ba zai haddasa karancin kudaden da ake musaya a kasuwannin kasar ba.

Kididdigar ta kuma nuna cewa, a watan Janairu na wannan shekara, farashin kayayyakin abinci na kasar Sin ya karu da kashi 4.2 bisa dari, sakamakon zuwan lokacin hutu na bikin bazara. Mataimakin shugaban sashin nazarin hada-hadar kudi da hannayen jari na jami'ar Renmin ta kasar Sin Mista Zhao Xijun ya ce:

"Jama'a sun kara sayen abubuwa a lokacin bikin bazara, wanda ya yi sanadiyyar hauhawar farashin kayayyakin abinci. Karuwar farashin kayayyakin abinci a watan Janairun shekarar bana ta nuna cewa, a yayin bikin bazara, adadin kudaden da Sinawa suka kashe a fannin sayen abinci ya yi yawa."

A ganin wadannan kwararru, kila ma ma'aunin CPI zai cigaba da raguwa har sai abun da hali ya yi.

A wannan rana kuma, ma'aunin PPI wato farashin da ake amfani da shi na da bisa ma'aunan kayayyakin da masana'antu ke sarrafawa na watan Janairu da aka fitar ya nuna cewa, wannan ma'auni ya ragu da kashi 3.3 bisa dari idan an kwatanta bisa na makamancin lokaci na shekarar da ta gabata, wanda ya zarta hasashen da kwararru suka yi, inda Mista Zhao Xijun ya cigaba da cewa:

"Raguwar yawan PPI ta nuna cewa, farashin manyan hajojin da ake sayarwa a kasuwannin duniya ya ragu ainun, ciki har da makamashi, da danyun kayayyaki. A daya bangaren kuma, sakamakon mummunan tasirin da rikicin hada-hadar kudi na duniya ya jawo, harkar sayar da kayayyakin da masana'antu ke sarrafawa ba ta bunkasa ba sosai."

Ko da yake a halin da ake ciki yanzu, tattalin arzikin kasar Sin ya sami farfadowa, amma raguwar yawan CPI da na PPI a cikin wani tsawon lokaci ta yi barazanar haddasa karancin kudade da ake musaya a kasuwannin kasar. Dangane da wannan batu, Mista Zhao Xijun ya ce, bisa ga la'akari da hakikanin halin da ake ciki, ba za'a samu karancin kudade a kasuwanni ba, inda ya ce:

"Alkaluman da aka bayar sun shaida cewa, rancen kudi da bankunan kasar Sin suka bayar a watan Disamban shekarar bara da watan Janairun shekarar bana ya yi yawa, wannan ya nuna cewa, bankin tsakiya na kasar Sin yana kokarin bada tabbaci a fannnin samar da isassun kudade a kasuwanni."

A nasa bangare kuma, wani kwararre kan harkokin tattalin arziki daga sakateriyar bankin raya kasashen Asiya dake nan kasar Sin Mista Zhuang Jian ya ce, tattalin arzikin Sin na fuskantar matsin lamba a cikin wani kankanin lokaci, amma ba za'a samu karancin kudade a kasuwanni a tsawon dukkan shekara ba.

Dadin dadawa kuma, kwararru sun bayyana cewa, shirin farfado da tattalin arziki wanda ya kunshi kudin Sin Yuan triliyan 4 da gwamnatin kasar ta bullo da shi, zai kara taka rawar a-zo-a-gani a fannin zaburar da tattalin arzikin kasar nan gaba kadan.(Murtala)