Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-02-11 16:38:15    
Sang Gege da littafinta na "yayin da nike kanana"

cri
Kwanan baya, a shaguna na sayar da littattafai na kasar Sin, an fara sayar da wani littafi mai suna "yayin da nike karama".Kuma masu karantawa za su iya karanta wannan littafi daga ko wane shafi, sabo da bayan da ka karanta dukkansu, za ka iya gane abubuwan da mai rubuta wannan littafi take son bayyanawa a ciki. A cikin wannan littafi, marubuciya Sang Gege ta yi zane-zane da yawansu ya kai 89, sabo da haka, masu karatu za su iya sake jikinsu yayin da suke karantawa. An mayar da wannan littafi a matsayin wani littafin da aka wallafa ga baligai masu sha'awar lokacin da suke kanana, kuma lalle wannan littafi ya sami karbuwa tsakanin masu karatu, musamman ma matasan da aka haife su a shekarun 1970 zuwa shekarun 1980 na karnin da ya wuce. Acikin shirimmu na yau, za mu gabatar muku da marubuciyar wannan littafi.

Sang Gege , wata yarinya ce ta kabilar Tibet, ko da yake ba ta da tsayi sosai, amma tana da kyan gani. A karshen shekarun 1970, an haife ta a birnin Chengdu da ke kudu maso yammacin kasar Sin, kuma ta ji dadin zaman rayuwarta ta yarantaka a yankunan mahakar kwal, inda mahaifanta suka yi aiki. Yayin da take yarinya, sabo da kullum mahaifanta suna kan yi cacar baki, sun kashe aurensu, lalle, wannan batu ya yi babban tasiri a kan rayuwarta. Bayan da ta girma, ta sami wani saurayi, amma, abin bakin ciki, sun rabu, daga bisani kuma Sang Gege ta bar Sichuan, ta zo Beijing da Shanghai da Guangzhou don neman aikin yi, lalle ta ji dadin zaman rayuwarta a wadannan wurare, sabo da ta fi son yawon shakatawa a birane da dama. Da ma, ta taba zaman 'yar wasan kwaikwayo da Model da 'yar jarida haka kuma ta taba sayar da giya, yanzu ta yi aiki a mujallar "biranen Sin"

Littafin "yayin da nike karama", wani littafi ne da Sang Gege ta wallafa, a cikin wannan littafi an rubuta wata yarinya ta birnin Chengdu da dukkan zaman rayuwarta. Bayan karanta dukkan labaru da ke kunshe a ciki, za a iya sanin, yayin da wannan yarinya take karama, ta yi sha'awar abubuwa. Ala misali, yayin da take shiga shaguna don sayen abubuwan wasa, sai ta zabi duk wanda ba shi da kyaun gani, sabo da a ganinta, idan ba ta zabe su ba, babu wanda zai zabe shi. Haka kuma a cikin wannan littafi, mun samu wani labari cewa, yayin da take wanke kafafunta a gabar kogi, sabo da ruwa ya tafi da takalminta daya, sai ta jefar da dayan, ta bar shi, sabo da tana son wadanan takalma su zama a tare.

A cikin wannan littafi, Sang Gege ta rubuta wata jimla kamar haka: "Lokaci na da , tamkar wata halawa ce, sabo da na cinye ta, sai ba ma kawai ta more ni ba, haka kuma ta more sauran mutane. A cikin wannan littafi, akwai abubuwa da dama da ta waiwaye baya, amma ta ce, ya fi kyau, masu karantawa za su iya mayar da wannan littafi kamar wani littafi don tunawa da zaman rayuwa ta da, sabo da haka za su iya samu wasu abubuwa daga zukatanta. Ta bayyana cewa,

Ina son in bayyana juyawar zamani a cikin littafina, sabo da haka, na sanya wasu abubuwa a ciki. Alal misali, ban rubuta dalla-dalla kan sauyawar tsarin mulkin kasar ba, amma a maimakon haka, na rubuta sauye-sauye a cikin rayuwata. Ni ma ina so in bayyana zaman rayuwata ga kowa da kowa, don mutane su iya gane sauye-sauyen da muka samu a kasar Sin.

Wasu masu ba da sharhi sun ce, an rubuta wannan littafi a karkashin wani lokaci, watau a shekarun 1970 da 1980, kuma cikinsu, an bayyana mana dukkan labaru masu ban dariya sosai, haka kuma an canja odar wasu abubuwa, sabo da bai kamata a manta ba yayin da lamarin ya faru, mai rubuta wannan littafi ita ma tana yarinya. Lalle, a cikin wannan littafi, masu karantawa za su iya jin yadda yaran Sin suke girma bayan da Sin ta aiwatar da tsarin yin gyare-gyare da bude kofa ga kasashen waje.

Yayin da ake tamabayi Sang Gege, ko dukkan labarun da ta rubuta, ita da kanta ta kirkiro, ko kuma lalle dukkansu ainihin batun da ya faru ne, ta amsa cewa,

"A ganina, ana yin irin wannan tambaya ga ko wane marubuci, sabo da lalle wannan tambaya tana da wuya in amsa, sabo da wani lokaci, labarun da na rubuta, na ainihin batutuwan da suka faru ne, amma idan ka ce dukkansu ta rubuta, wannan ba zai yiyu ba. A ganina, ko wane labari mutum ko wane ko wane lokaci, ba shi ne muhimmanci ba, amma abin da ya fi muhimmanci shi ne abubuwan da marubuta suke so su bayyana a cikin wannan littafi"

Sang Gege ba ta son sauran mutane su kira ta kamar mawallafiya matashiya a kasar Sin, haka kuma yayin da ta gamu da bako, ta kan ji kunya, a sakamakon haka, kullum take cikin daki, kana kuma, ba ta cika son kayayyaki masu daraja ba, a ganinta, wadannan abubuwa kamar kitse ne a jikin mutum, kalilan ne zai isa, da ma, tana zaune ne a gida mai girman muraba'in kilomita 10, amma ga shi yanzu, ya kai 20, sai ta ji dadi da farin ciki, Sang Gege ita ma, tana da wata karamar rumfa, kuma cikinta, akwai dukkan tufafi da kayayyakin kwalliya da ta taba saya, idan tana so, za ta iya zuwa tare da shi ko ina, ban da wannan, ba ta son sauran kayayyaki, ta bayyana cewa,

"na gamsu da lokacin da nike yarinya, sabo da ba na so na zama wata gimbiya, lalle na sha wahala sosai, amma a ganina wannan ba kome, sabo da ni na girma tare da shan wahalhalu, ga shi yanzu, na iya fuskanta kome da kome, idan yau ban ji dadi ba, sai gobe, zan iya jin dadi. Haka kuma ni wata mutumiya ce da ke sha'awar kome da kome, yayin da nike yarinya, sai ina sha'awar dukkan duniya waje, sabo da haka, ina so in gwada dukkan abubuwa, sabo da haka, idan aka kwatanta ni da sauran yara, za a iya gane cewa, na samu abubuwa da yawa".

Sang Gege ta gamsu da rayuwata ta yanzu, sabo da yanzu, ba ta so ta zama wata marubuciya a kasar Sin, watakila ma, za ta iya daukar film ko yin sauran abubuwa. "Lalle ba a san inda rana za ta fadi ba"! Bai kamata sabo da ta rubuta wannan littafi ba, a mayar da ita kamar marubuciya, sabo da ba ta so kowa da kowa su mayar da ita kamar wata mai sanin ko wace sana'a, ita ma tana so ta zama wata mai saurin canjawa, za ta iya yin dukkan abubuwan da take so cikin sauki.

A shekarun 1980, an sami wani kalami, kidult a kasar Amurka, kuma an samu shi ne daga kalmomi kid wata yara, da adult baligai, ma'anarta ita ce, baligai masu kuruciya, a shekaru 1 ko 2 da suka shige, wannan kalami ya yi yayi a kasar Sin, kuma an yi amfani da wannan kalma don bayyana halin da wasu baligai ke ciki, Sang Gege tana kamar daya daga cikinsu, ba ta so ta girma, kullum tana so a dauke ta kamar yarinya.(Bako)