Sallar Yuan Xiao Jie na da suna na daban, wato sallar haduwa, inda iyalai da abokai kan hadu cikin yanayin murna, su ci kayan abincin da ake kira 'Yuan Xiao', su kunna fitilu, su yi gasar kacici-kacici tare da jin dadin kallon nune-nunen wasanni na gargajiya daban daban. A shekarar bana, a yayin da aka yi murnar sallar Yuan Xiao Jie, titin kasuwanci mafi shahara da ke da tarihin tsawon shekaru dari 6 da kasancewa a kasar Sin, wato titin Qian Men Da Jie ya sake shirya nune-nunen wasanni na gargajiya. Yau ma zan jagorance ku domin zagayawa wannan titi.
Titin Qian Men Da Jie wani tsohon titi ne da ke da dogon tarihi. Tsawonsa ya wuce mita 840 gaba daya, wanda a gefunansa akwai shaguna da yawa. A cikin daruruwan shekaru da suka wuce, ana adana salon gine-gine na gargajiya irin na Beijing a yankin da ke kewayen wannan titi. Titin Qian Men Da Jie shi ne alamar birnin Beijing, haka kuma shi daya ne daga cikin tituna mafi wadata a kasar Sin, inda kuma ake iya kara sani kan al'adu gargajiya masu nau'o'i daban daban, da kuma muhallin al'adun kasar Sin masu armashi. A ko wace shekara matafiya masu tarin yawa kan ziyarci wannan titi. Li Bo, wani jami'in kwamitin kula da harkokin titin Qian Men Da Jie ya gaya mana cewa, "Titin Qian Men Da Jie na kudancin babbar kofar Zheng Yang Men, yana kuma dab da fadar sarakuna ta kasar Sin wato Forbidden City ko kuma Gu Gong ta bakin Sinawa. A ko wane karon da sarakuna suka kai rangadin aiki, kamar zuwa wani wuri na daban domin nuna girmamawa ga kakanin-kakaninsu, tabbas ne su kan wuce ta wannan titi, shi ya sa a kan kira shi 'titin Tian Jie', wato titin da sarakuna suka bi. Titin Qian Men Da Jie ya sami ci gaba a karni na 16 da na 17, a zamanin daular Qing wato a karni na 17 zuwa farkon karni na 20, wadatuwar wannan titi ta kai matsayin koli. Tun can da har zuwa yanzu, wannan titi na matsayin titi mai ci gaban kasuwanci, inda jama'a su kan yi ciniki da shirya gangami da yawa."
A shekaru 1920 zuwa 1930, a sakamakon shigowar al'adun kasashen yammacin duniya, an yi koyi da salon gine-gine na yammacin duniya wajen yin gine-gine a titin Qian Men Da Jie. A gefuna 2 na titin, an iya ganin gine-gine irin na yammacin duniya a tsakanin gine-ginen gargajiya irin na kasar Sin. Domin sake bullo da yadda titin Qian Men Da Jie ya taba kasancewa a da, hukumar kiyaye abubuwan tarihi ta Beijing ta yi kwaskwarima kan wannan titi ta hanyar da ta dace. Mr. Li Bo ya gaya mana cewa,
"Tun daga shekarar 2002, mun gayyaci masana da yawa da su tattauna yadda za a iya nuna darajar titin ta fuskar al'adu da kasuwanci. A karshe dai, mun tsai da kudurin yi masa kwaskwarima domin maido yanayin da yadda ya taba kasancewa a shekarun 1920 zuwa shekarun 1930. Titin da kuka gani a yau titi ne da muka kafa shi bisa hotunan da aka dauka a wancan lokaci. Ta haka matafiya sun iya kasancewa cikin yanayi na kamar yadda aka taba kasancewa yau da shekaru da dama da suka wuce, har ma shekaru dari 1 da suka wuce, sun iya kara saninsu kan tarihin birnin Beijing na wancan lokaci da al'adunsa da kuma wadatuwar titin Qian Men Da Jie."
Titin Qian Men Da Jie mai sabuwar sura ya sake ganin matafiya a gabannin gasar wasannin Olympic ta Beijing a watan Agusta na shekarar bara, inda gine-gine irin na gargajiya da dadaddun shaguna suke jawo masu yawon shakatawa da yawa daga sassa daban daban na duniya a ko wace rana. Yanzu titin Qian Men Da Jie ya zama titin kasuwanci da aka hana zirga-zirgar motoci a ciki. Duk da haka, yanzu matafiya na iya ganin wata motar musamman mai suna 'Diang Diang Che', wadda ta taba kasancewa a matsayin daya daga cikin muhimman ababan hawa a Beijing a shekaru 1920. Dalilin da ya sa ake kiranta 'Diang Diang Che' shi ne domin a lokacin da take tafiya, direba kan kada kararrawa kamar Diang Diang domin yi wa masu wucewa gargadi. Yanzu wannan mota mai dogon tarihi ta sake dawo da zirga-zirga a titin Qian Men Da Jie, bayan da aka yi mata gyare-gyare domin kiyaye muhalli. Matafiya na iya shiga cikinta tare da jin dadin zaman rayuwar mazauna Beijing na wancan lokaci.
Titin Qian Men Da Jie ya zama kyakkyawan tunani a zukatan wadanda suka dade suna zaune a nan Beijing, kana ya samu gindi zama a zukatan dimbin mazauna Beijing da ke zaune a sauran wuraren kasar Sin. Wang Xinlu ya zo titin Qian Men Da Jie tare da abokansa da suka zo daga sauran sassan kasar Sin domin kara sani kan wadatuwar da aka taba samu a titin a zamanin da. Mr. Wang ya ce,
"A can da, manyan motocin al'umma suna iya kaiwa da kawowa a wannan titi, kana kuma akwai shaguna da yawa. A lokacin da nake karami, na taba zuwa nan. Yanzu an hana zirga-zirgar motoci a titin, ta haka, titin ya kara nuna halin musamman. Gani ya kori ji. Ina farin ciki da kawo wannan titi ziyara da kaina."
A sallar Yuan Xiao Jie, an gayyaci kungiyoyin wasanni masu zaman kansu daga sassa daban daban na kasar Sin da su nuna wasanni a titin Qian Men Da Jie, inda suka sake fito da kasaitaccen muhallin da aka taba kasancewa da shi a da, suna yin murnar sallar Yuan Xiao Jie ta hanyar shirya nune-nunen wasanni na gargjiya, kamar kide-kide da wake-wake da kuma nuna fasahohi na abubuwan tarihi na al'adu ba kaya ba.
A ran 9 ga wata, a titin Qian Men Da Jie, wato wani budadden dandamalin wasanni, matafiya sun more idonsu da wasannin fasaha da kungiyoyin nune-nunen wasanni na gargajiya suka nuna a cikin fareti. Zhang Wei, mataimakin daraktan cibiyar kula da harkokin fasaha da al'adu ta hukumar kula da harkokin al'adu ta Beijing ya yi karin bayanin cewa,
"Mun zabi titin Qian Men Da Jie dan nuna wasanni ne domin yada al'adun gargajiya, saboda wannan titi na da dogon tarihi. Mun kuma gayyaci wasu kungiyoyin nuna wasannin gargajiya, ta haka mutane sun iya yin murnar sallar Yuan Xiao Jie a titin."
Ban da wannan kuma, mai shiryawa ya kafa wani dandamalin din din din domin nuna wasu fasahohin gargajiya da ke nuna halin musamman na kasar Sin, kamar fasahar yin wasa da mutum-mutumin da aka yi da fatar dabba da kuma katako. Abin da aka fi lura da shi shi ne masu gadon abubuwan tarihin al'adu ba kaya ba na kasar Sin 8 sun nuna fasahohin gargajiya kai tsaye a dandamalin. Mr. Zhang ya kara da cewa, "Fasahohin da wadannan masu fasaha wadanda tsoffin hannu ne ke da su an gada ne daga zuriya zuwa zuriya. Mun shirya hotuna kan wasu abubuwan tarihin al'adu ba kaya ba na kasarmu da na duniya. Sa'an nan kuma, masu yawon shakatawa sun ji dadin kallon wasu abubuwan tarihi na al'adu ba kaya ba da kuma nune-nunen wasanni da masu gadon wadannan abubuwan tarihi na al'adu suka nuna."
A sallar Yuan Xiao Jie wato ran 15 ga watan Janairu bisa kalandar gargajiya ta kasar Sin, a titin Qian Men Da Jie, ana shirya gasar kacici-kacici domin taimakawa matafiya da su kara saninsu kan al'adun gargajiya na kasar Sin da kuma jin dadin shiga cikin harkokin nishadi ta hanyar gasar kacici-kacici mai ban sha'awa.
|