Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-02-10 15:50:22    
Yagaggiyar wainar da aka tsoma a cikin romon naman tunkiya a birnin Xi'an

cri
in kun sami damar kawo ziyara ga birnin Xi'an mai dogon tarihi da ke yammacin kasar Sin, to, bayan da ka ziyarci mutum-mutumin soja da dawaki da aka kera a zamanin daular Qin na kasar Sin wato yau shekaru fiye da dubu 2, kuma sarki Qin Shi Huang ta kasar Sin ya binne su a cikin kushewarsa, da kuma kushewar wannan sarki Qin Shi Huang, wajibi ne ku dandana cincin mai nau'i daban daban na wurin. Yagaggiyar wainar da aka tsoma a cikin romon nama, da ruwan lemon tsami, da sanyayyar taliya da dai sauransu dukkansu sun sanya miyau ya biya a bakin mutane, a ciki kuma, kayan abinci na Yang Rou Pao Mo, wato yagaggiyar wainar da aka tsoma a cikin romon naman tunkiya ya fi shan bamban da saura, kuma ya fi ba da tasiri. Yanzu bari mu shiga gidan abinci na Tong Sheng Xiang da ke birnin Xi'an, wanda ya yi suna ne saboda wannan kayan abinci na Yang Rou Pao Mo.

Wakilinmu ya shiga wannan gidan abinci na Tong Sheng Xiang ne a daidai lokacin cin abincin rana. Babban zauren wannan gidan abinci ya cike da mutane. Masu cin abincin suna hira, suna yaga waina da hannunsu bisa yadda suke so. Irin wannan yanayi mai kyau yana kwantar da hankulan mutane sosai.

"Gafara dai, malam, ko ka iya gaya mini daga ina ne ka zo?

Na zo ne daga birnin Shanghai.

Shin wannan shi ne karo na farko da ka ci wannan kayan abinci na Yang Rou Pao Mo?

E, haka ne.

Amma a ganina, ka iya yaga waina sosai?

Abokaina sun koya mini fasahar yaga waina. Wannan kayan abinci yana kara dadin ci, in yagaggiyar waina ta kara zama karama. Ina matukar son cin wannan kayan abinci. Dukkan mazauna arewancin kasar Sin suna sonsa."

Akwai wani labari mai ban sha'awa game da asalin kayan abinci na Yang Rou Pao Mo. An ce, yau da shekaru dubu 1 ko fiye da suka wuce, Zhao Kuangyin, wanda shi ne sarki na farko na zamanin daular Song na kasar Sin, bai taki sa'a ba a lokacin kuruciyarsa, shi ya sa ya taba gudun hijira a Chang'an a wancan lokaci, wato birnin Xi'an na yanzu. Wata rana, Zhao Kuangyin ya ji sanyi sosai tare da matukar yunwa, a cikin aljihunsa sai busassun waina guda 2. A daidai wancan lokaci, a cikin shagon sayar da naman tunkiya da ke gefen hanya, mai shagon ya dafa naman tunkiya. Mai shagon ya tausaya masa dan haka ya gaya wa Zhao Kuangyin ya yagi wainarsa da hannunsa, ya zuba miyar da ya dafa da naman tunkiya a kan yagaggiyar waina. Zhao Kuangyin ya cinye wainar, har ma ya daina jin sanyi da yunwa.

Bayan shekaru 10, wato a shekarar 960, Zhao Kuangyin ya zama sarki. A lokacin da yake rangadin aiki, ya wuce ta wannan shagon sayar da naman tunkiya, ya waiwayi abubuwan da suka faru a da, ya umurci mai shagon ya dafa masa wani kwano na kayan abinci na Yang Rou Pao Mo na daban. Ya cinye, ya nuna babban yabo, ya kuma bawa mai shagon kudade da yawa.

Wannan labari ya bazu, har ma kayan abinci na Yang Rou Pao Mo ya zama alamar Chang'an a fannin abinci. Bayan shekaru fiye da dubu guda, wannan kayan abinci ya ci gaba da wakiltar abinci irin na Xi'an.

Masu sauraro, a zamanin yau, a cikin wannan gidan abinci na Tong Sheng Xiang mai tsawon shekaru 88 da kasancewa a kusa da babban filin Zhong Gu Lou a Xi'an, kuna iya dandana wannan kayan abinci mai dadi, wanda kasar Sin ta tanade shi a cikin takardar sunayen kayayyakin tarihi na al'adu da ba na kaya ba a watan Yuni na shekarar 2008.

Yaya ake dafa irin wannan kayan abinci mai dadin ci? Bayan da wakilinmu ya sami iznin mai gidan abincin, ya shiga dakin dafa abinci. Ga wasu kananan tukwane da suka yi jerin gwano, wadanda suka fi kwano girma da kadan. Mr. Ma, wato babban kuku na wannan gidan abinci, wanda ke sanye da fararen tufafi da farar hula irin na Musulmai, yana rike da wata karamar tukunya a hannunsa na hagu, a hannunsa na dama kuwa, akwai wani cokalin karfe, ya sa abubuwan kamshi a cikin miya. Mr. Ma ya fayyace wa wakilinmu sirrin dafa kayan abinci na Yang Rou Pao Mo.

"Abu mafi muhimmanci shi ne tabbatar da ganin dandanon miya ya yi kyau. Tilas ne a mai da hankali sosai kan lokaci na saka kayan kamshi, kamar gishiri, a cikin miyar."

Dalilin da ya sa kayan abinci na Yang Rou Pao Mo da ake sayarwa a gidan abinci na Tong Sheng Xiang yake da dadin ci kwarai da gaske shi ne domin kuku-kuku sun sha dukufa wajen dafa wannan kayan abinci. Mr. Wu, wani kuku na daban ya yi karin bayani ba tare da boye kome ba da cewa,

"Mu kan yi awoyi misalin 10 muna tsoma kashin tunkiya a cikin ruwan da ke gangara domin kawar da warinsa. Daga baya, mu kan dafa kashin tunkiyar har na tsawon awoyi 12 a kan karamar wuta, daga baya, mu ci gaba da dafa shi a kan babbar wuta har na tsawon awoyi 4, daga baya, mu sa nama a cikin miyar yadda ya kamata."

Akwai sirri kan dafa kayan abinci na Yang Rou Pao Mo, haka kuma, akwai sirri kan cin wannan kayan abinci. Bai Jianbo, mataimakin shugaban kungiyar nazarin al'adun sarrafa kayan abinci ta lardin Shaanxi, ya san hanyar cin wannan kayan abinci sosai da sosai. Ya ce,

"A kan bi hanyoyi 4 wajen cin kayan abinci na Yang Rou Pao Mo. Musulmai mazauna Xi'an ba su son romon nama da yawa, ya kan kasance tun daga farko har zuwa karshe, babu romon nama a cikin kwanoninsu. Wasu kuma, bayan da suka ci waina, sauran romon nama kadan da ya rage a gindin kwano, sai su shanye. Sa'an nan kuma, mutane da yawa suna son romon nama da yawa a cikin kwanoninsu. Bugu da kari kuma, wasu suna son cin wainar da aka ajiye nama a ciki, kuma ba a tsoma ta a cikin romon nama ba, ta haka suna iya cin wainar tare da shan romon naman."

Kayan abinci na Yang Rou Pao Mo da a kan ci ta hanyoyi 4 ya riga ya zama wani bangare na zaman rayuwar mazauna Xi'an. Bari mu ji kalaman da Mr. Zheng, wani mazauni Xi'an ya fada, yadda za mu iya fahimtar kaunar da mazauna Xi'an ke nunawa wannan kayan abinci.

"A lokacin da nake karami, iyayena da dan uwana da ni mu kan je kallon sinima tare. A gaban gidan sinima, akwai wani gidan sayar da kayan abinci na Yang Rou Pao Mo. Muna saya waina, kuma muna iya kallon sinama tare da yaga wainar da hannu. Bayan kammala kallon sinaman, ba mu bukatar yin jerin gwano, sai kuku ya dafa mana yagaggiyar wainar a cikin romon nama, daga baya, mu ci, muna hira cikin farin ciki."

A kwanan baya, wani kamfanin wallafa jaridu na Xi'an ya shirya wani aikin bincikar ra'ayoyin jama'a kan alamar Shaanxi. Abu mai sha'awa shi ne a karshe dai, Chen Zhongshi, wani shahararren marubuci na Shaanxi da kayan abinci na Yang Rou Pao Mo sun zama na farko duka. Game da wannan, Mr. Chen Zhongshi yana ganin cewa,

"In an tabo magana kan Xi'an, da farko a kan tuna da kayan abinci na Yang Rou Pao Mo. Na taba karbar abokai marubuta da yawa daga sassa daban daban na kasar Sin a Xi'an. Abin da ya burge ni shi ne, wasu abokaina sun fi son cin kayan abinci na Yang Rou Pao Mo a maimakon shirya musu wata liyafa. Suna matukar son cin wannan kayan abinci kusan kamar yadda nake yi. A takaice dai, kyan dandanon kayan abinci na Yang Rou Pao Mo yana iya jawo hankulan mutane har abada."