Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-02-09 21:07:19    
Kasar Sin tana daukar matakai don bada tabbaci ga jama'a da su samu guraben aikin yi

cri
A halin da ake ciki yanzu, rikicin hada-hadar kudi da ya dabaibaye duniya yana kara matsa lamba kan kasar Sin a fannin samar da guraben aikin yi ga jama'arta. Domin tinkarar wannan matsala yadda ya kamata, hukumomi na wurare daban-daban a kasar Sin suna daukar matakai iri-iri, a wani kokarin bada cikakken tabbaci ga jama'a da su sami guraben aikin yi.

Lardin Guangdong dake kudancin kasar Sin, yana daya daga cikin lardunan kasar wadanda suka fi cigaban masana'antu, wanda kuma ya kasance lardin da ya fi yin hasara sakamakon rikicin kudi. An rufe kamfanoni da dama a lardin, kuma manoma 'yan ci rani masu tarin yawa sun rasa guraben aikin yi. Saboda haka, abun da lardin Guangdong ya ba fifiko yayin da yake daukar matakai shi ne, a nuna goyon-baya ga kamfanoni da su gudanar da harkokinsu yadda ya kamata, ta yadda za'a samar da karin guraben aikin yi ga mutanen da suka rasa ayyukansu.

A birnin Dongguan na lardin Guangdong, hukumar wurin ta kafa asusun musamman da ya kunshi kudin Sin Yuan biliyan 2, don bada kwarin-gwiwa da goyon-bayan kamfanonin kere-kere da su yi kwaskwarima. Sakataren kwamitin birnin Dongguan Mista Liu Zhigeng ya ce:

"A bangare guda, kamata ya yi a farfado da imanin kamfanoni a birnin Dongguan. A daya bangaren kuma, ya kamata a jawo kamfanonin duniya masu karfi da su zo nan lardinmu. A waje daya kuma, ya kamata mu yi kokarin bunkasa sana'o'in da suke kunshe da sabbin fasahohi na zamani."

A lardin Anhui dake tsakiyar kasar Sin kuma, hukumomi da sassa daban-daban suna maida hankalinsu kan tallafawa kamfanoni, da samar da guraben aikin yi ga jama'a, inda darektan kwamitin kula da harkokin tattalin arziki na lardin Mista Zhao Bingyun ya ce:

"A halin yanzu, an himmatu wajen taimakawa muhimman kamfanoni guda 51, wadanda suke karancin kudade."

Dangane da manoma 'yan ci rani wadanda suka koma kauyukansu sakamakon rashin aikin yi, sassa daban-daban suna daukar matakai don samar musu da guraben aikin yi. A lardin Sichuan da ya fi fitar da ma'aikata a kasar Sin, akwai manoma 'yan ci rani da adadinsu ya zarce miliyan guda wadanda suka rasa aikin yi a sanadiyyar rikicin kudi. Hukumomin wurin suna daukar matakai iri-iri don samar da mafita ga wadannan manoma 'yan ci rani.

A birnin Ziyang na lardin Sichuan, gwamnatin wurin tana daukar matakai da dama don sake samar da guraben aikin yi ga jama'a. Madam Yu Shiying ta sake samun aikin yi a wani kamfanin kera takalma na wurin, bayan da ta halarci kwas din samun horo a fannin fasaha daga gwamnatin wurin, inda ta ce:

"Na dawo daga lardin Jiangsu a karshen watan Nuwamban shekarar bara, na sake samun aikin yi a wannan kamfani bayan da na sami horaswa, yawan kudin albashin da nake samu a kowane wata ya kai akalla Yuan 1200."

A halin yanzu, a cikin manoma 'yan ci rani sama da miliyan daya a lardin Sichuan, wadanda suka koma gida sakamakon rashin aikin yi, akwai mutanen da yawansu ya tasam ma dubu 600 wadanda suka sake samun aikin yi. Mataimakin shugaban hukumar bada tabbaci ga samun guraben aikin yi ta lardin Sichuan Mista Liu Jiaqiang ya ce:

"Yanzu muna rubanya kokarinmu wajen horas da manoma 'yan ci rani don inganta kwarewarsu, ta yadda za su sake samun guraben aikin yi."(Murtala)