Lokacin da ake aiwatar da manufofin yin gyare-gyare a gida da bude kofarta ga kasashen waje a kasar Sin a cikin shekaru 30 da suka gabata, ba a iya manta da wata kalma ba, wato "yankin musamman na tattalin arziki". Ya kasance tamkar wata gonar yin gwaje-gwaje wajen yin gyare-gyare, kuma wata tagar da ke bayyana wa kasashen duniya yadda kasar Sin ke bude kofa, "yankunan musamman na tattalin arziki" da aka kafa a nan kasar Sin sun dora muhimmanci sosai ga cigaban tattalin arzikin kasar Sin. Idan babu wadannan yankunan musamman na tattalin arziki, mai yiyuwa ne kasar Sin ba za ta iya samun cigaba a dukkan fannoni kamar yadda aka samu yanzu ba. Cigaban da aka samu a yankunan musamman na tattalin arziki ya kuma bayyana yadda kasar Sin ke samun cigaba.
Jama'a masu sauraro, akwai wata wakar mai suna "labarin da ya auku a lokacin bazara"da ta shahara sosai a nan kasar Sin, imda aka rera cewa, "a lokacin bazara na shekarar 1979, akwai wani dattijo ya tabbatar da wani wurin da ke kan bakin tekun kudancin kasar Sin??" Dattijon da aka kira a cikin wannan waka shi ne marigayi Deng Xiaoping, wato babban mai tsara shirin yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga kasashen waje na kasar Sin. Wurin da ya tabbatar a kan taswira shi ne yankin musamman na tattalin arziki, wato birnin Shenzhen na yanzu. A wancan lokaci, me ya sa marigayi Deng Xiaoping ya mai da hankalinsa sosai kan yankin musamman na tattalin arziki? Yanzu da farko dai bari mu bayyana muku halin da kasar Sin ke ciki a wancan lokaci.
Lokacin da ake karshen shekaru 70 na karnin da ya gabata, an yi kome, kamar kayayyaki da yawansu da hanyar kera su da ake bi ne bisa shirin da gwamnatin tsakiyar kasar Sin ta tsara. Sakamakon haka, 'yan kwadago da wadanda suke tafiyar da masana'antu ba su mai da hankalinsu kan aiki ba. Amma a sauran yankunan duniya, an soma samun cigaban fasahohin zamani a karo na 3. Tattalin arzikin yawancin kasashe masu arziki ya kuma samu cigaba cikin sauri sosai. A waje daya kuma, kasashen da ke makwabataka da kasar Sin, kamar su kasashen Japan da Koriya ta kudu sun kuma samu cigaban tattalin arzikinsu. Irin wannan bambancin da ke kasancewa a tsakanin kasar Sin da sauran kasashen duniya ya sa shugabannin kasar Sin da su gane cewa, ba a iya rabawa da kasar Sin da sauran kasashen duniya ba lokacin da take son neman cigaba, dole ne a bude kofarta ga kasashen waje domin neman cigaba.
Amma daga ina ne aka iya soma aiwatar da manufar bude kofa ga kasashen waje? A watan Nuwamba na shekara ta 1977, Mr. Deng Xiaoping, babban mai tsara shirin yin gyare-gyare da bude kofar kasar Sin ga kasashen waje ya yi rangadin aiki a lardin Guangdong, inda ya sanya idonsa a wani kauye mai suna Shenzhen. A shekarar 1977, yawan kudin shiga da kowane manomi ya samu a kowace rana ya kai kudin Sin yuan daya kawai, wato bai kai kobo hamsin ba a wancan lokaci. Amma kowane manomin yankin Hongkong da ke makwabtaka da kauyen Shenzhen ya iya samun dalar Hongkong fiye da sittin a kowace rana. Sakamakon haka, dole ne an nemi hanyar rage irin wannan bambancin da ke kasancewa a tsakaninsu. Wannan kuma ya sa gwamnatin tsakiya ta kasar Sin ta sa niyyar tsai da kudurin kafa yankunan musamman na fitar da kayayyaki zuwa kasashen waje a Shenzhen da Zhuhai da Shantou da birnin Xiamen a watan Yuli na shekarar 1979. Sannan wadannan yankuna sun zama yankunan musamman na tattalin arziki. Daga baya, a shekarar 1988, gwamnatin kasar Sin ta tsai da kudurin kebe duk lardin Hainan da ya zama wani yankin musamman na tattalin arziki.
Yankunan musamman na tattalin arziki da aka kafa sun bayyana yadda kasar Sin ta yi taka tsan-tsan wajen aiwatar da manufar yin gyare-gyare a gida da bude kofarta ga kasashen waje. A wancan lokaci, kasar Sin ba ta da isashen kasafin kudi da kayayyakin da ake bukata wajen raya tattalin arziki, kuma ba ta da cikakken tsarin shari'a da na dokoki. Har ma kasar Sin tana rashin fasahohin yin mu'amala da sauran kasashen duniya a fannin tattalin arziki. Irin wannan halin musamman da kasar Sin ke ciki a wancan lokaci ya sanya a soma aiwatar da manufar yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga kasashen waje a wasu yankuna kawai. Bisa shirin da aka tsara, an iya yin gwaje-gwajen da ke dacewa bisa halin musamman da kasar Sin ke ciki a wadannan yankunan musamman. Sannu a hankali ne kasar Sin ta yi kokarin yin ban kwana da tsarin raya tattalin arziki bisa shiri zuwa tsarin raya tattalin arzikin kasuwanni.
Bayan an kafa yankunan musamman na tattalin arziki, a watan Fabrairu na shekarar 1984, Mr. Deng Xiaoping ya sake zuwa birnin Shenzhen. Bayan da ya gano yawan kudin shiga da kusan kowane gidan masunta na kauyen Shenzhen ya samu ya kai fiye da kudin Sin yuan dubu 10 a kowace shekara. Lokacin da ake gina wani babban gini, an gina hawa 3 a kowane kwanaki uku uku. Sabo da haka, Mr. Deng Xiaoping ya tabbatar da cewa, manufar kafa yankunan musamman na tattalin arziki ta yi daidai. Sannan a shekara ta 1992, dattijo Deng Xiaoping ya sake koma birnin Shenzhen, inda a fili ne ya nuna cewa, yankunan musamman na tattalin arziki suna bin tsarin gurguzu, ba su bi tsarin jarin hujja ba.
A cikin shekaru 30 da suka gabata, yankunan musamman na tattalin arziki sun bayar da gudummawarsu a fannonin samar da sabbin ilmi da fasahohin zamani da raya tattalin arziki da bayyana wa kasashen waje manufofin da kasar Sin ke dauka.
Mutanen yankunan musamman na tattalin arzikin sun yi kokari sosai wajen kirkiro sabbin hanyoyin neman cigaba. Sakamakon haka, a cikin shekaru 30 da suka gabata, birnin Shenzhen, wato wani karamin garin da ke kan iyakar kasar Sin ya zama wani birnin zamani wanda jimlar GDP ta hau kan matsayi na 4 a cikin dukkan manyan biranen kasar Sin. Birnin Xiamen ya zama wani birnin zamani da ya shahara a duniya a fannonin yawon shakatawa da masana'antu. A waje daya kuma, biranen Zhuhai da Shantou ma sun samu kyawawan fasahohi wajen bude kofa ga kasashen duniya.
Mukasudin aiwatar da manufar yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga kasashen waje a nan kasar Sin shi ne zamanintar da kasar Sin da jama'a su samu arziki. Bisa wannan shiri, tun daga shekarar 1979 zuwa shekara ta 2007, matsakaicin saurin karuwar tattalin arzikin kasar Sin ya kai fiye da kashi 9 cikin kashi dari. Kuma matsakaicin yawan kudin shiga na kowane Basine ya samu a kowace shekara ya kai dalar Amurka dubu 2 da dari 3 da sittin a shekara ta 2007 daga dalar Amurka dari 1 da casa'in kawai a shekarar 1979. Yawan matalautan da ke zama a kauyuka ya rage zuwa kimanin miliyan 20 a shekara ta 2007 daga miliyan 250 na shekarar 1979.
Bayan da kasar Sin ta shiga lokacin bude kofarta a duk fadinta gaba daya, ko yankunan musamman na tattalin arziki za su iya ci gaba da daukar manufofi da matakai na musamman? A watan Oktoba na shekara ta 2003, a gun cikakken zama a karo na 3 na kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin ta 16, an tabbatar da cewa, yankunan musamman na tattalin arziki za su iya ci gaba da kasancewa a matsayin tagogi da gonakin gwaji da ke nuna wa kasashen waje yadda kasar Sin ke cigaba da yin gyare-gyare a gida da bude kofarta ga kasashen waje. Sabo da haka, yankunan musamman na tattalin arziki suna neman cigaba bisa hakikanin halin da ake ciki yanzu.
Ya zuwa shekara ta 2008, matsalar hada hadar kudi da ta auku a Amurka ta girgiza kasar Sin. Lokacin da wasu masana'antu da kamfanoni suke cikin mawuyancin hali, masana'antu da kamfanoni na birnin Shenzhen sun samu damar kyautata tsarin kayayyakin da suke yi, kuma da kirkiro sabbin fasahohin zamani. Sabo da haka, sun samu damar tinkarar matsalar hada hadar kudi.
Shugaban kasar Sin Hu Jintao ya ce, yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga kasashen waje muhimmin zabi ne da aka yi lokacin da ake shakkar makomar kasar Sin, ita kuma wajababbiyar hanya ce da ake bi domin raya zaman al'ummar gurguzu bisa halin da ake ciki a kasar Sin da sake bunkasuwar al'ummar Sinawa. (Sanusi Chen)
|