Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-02-06 18:48:53    
Shugaban kasar Sin zai kai ziyara a kasashe 5 na Asiya da Afirka

cri

Zhai Jun, mai ba da taimako ga ministan harkokin waje na kasar Sin

Tun daga ran 10 zuwa ran 17 ga wata, shugaba Hu Jintao na kasar Sin zai kai ziyarar aiki ga kasashen Saudiyya da Mali da Senegal da Tanzania da Mauritius. A ran 6 ga wata, Zhai Jun, mai ba da taimako ga ministan harkokin waje na kasar Sin ya zanta da wakiliyarmu a nan Beijing a kan ziyarar aiki da shugaba Hu zai yi a Afirka.

Mr. Zhai ya bayyana cewa, an sami sakamako da yawa a yayin taron koli na Beijing na dandalin tattaunawa kan yin hadin gwiwa a tsakanin Sin da Afirka, inda kuma bangarorin 2 suka sami muhimmin sakamako a fannoni 2. Da farko, sun tabbatar da huldar abokantaka ta sabon salo a tsakaninsu bisa manyan tsare-tsare, wato suna yin zaman daidai wa daida da amincewa da juna a fannin siyasa, su yi hadin gwiwar neman samun nasara tare a fannin tattalin arziki da kuma yin mu'amala da yin koyi da juna a fannin al'adu. Na biyu kuma, a madadin gwamnatin Sin, shugaba Hu ya sanar da matakai 8 kan yin hadin gwiwa tare da Afirka. A cikin shekaru 2 ko fiye bayan wannan taron kolin, a sakamakon dora muhimmanci da Sin da Afirka ke yi kan hadin gwiwa a tsakaninsu, suna gudanar da karin ayyuka ba tare da wata matsala ba amma ba tare da samun sakamako mai kyau. Ban da wannan kuma, Sin da Afirka sun kara kyautata hulda a tsakaninsu a fannin siyasa, sun zurfafa hadin gwiwarsu a hakikanan fannoni, sun kuma kara mara wa juna baya da kuma taimakawa juna a al'amuran duniya.

A watan Oktoba na shekarar da ta gabata, a yayin taron manyan jami'ai a karo na 6 na dandalin tattaunawar yin hadin gwiwa a tsakanin Sin da Afirka da aka yi a kasar Masar, an kimanta halin da ake ciki game da gudanar da karin ayyuka bayan taron koli na Beijing a matsakaicin lokaci. Dukkan sassan wato Sin da Afirka sun gamsu da ci gaban da suka samu. Bangaren Afirka kuwa ya nuna babban yabo ga kasar Sin bisa sahihancinta da kuma ayyukan da take yi. Shekarar bana shekara ce ta karshe ta aiwatar da sakamakon da aka samu a yayin taron koli na Beijing. A watanni 4 na karshe na wannan shekara, za a yi taron ministoci a karo na 4 na dandalin tattaunawa a Masar. Kasar Sin tana son ci gaba da inganta tuntubar juna da daidaita matsayi a tsakaninta da kasashen Afirka wajen aiwatar da sakamakon da aka samu a yayin taron koli na Beijing da shirya taron ministoci a karo na 4 da kuma ciyar da huldar abokantaka bisa manyan tsare-tsare ta sabon salo a tsakaninta da Afirka gaba, ta haka za a iya kawo wa jama'ar sassan 2 dukkan alheri.

Zhai Jun, mai ba da taimako ga ministan harkokin waje na kasar Sin ya zanta da wakiliyarmu a nan Beijing

Mr. Zhai ya kuma yi mana bayani kan burin shugaba Hu na yin wannan ziyara a Afirka. Ya ce, tun can da har zuwa yanzu, Sin da Afirka na da dankon zumunci a tsakaninsu. Har kullum kasar Sin na dora muhimmanci kan raya irin wannan kyakkyawar dangantaka a tsakaninta da kasashen Afirka. Bayan da Hu Jintao ya zama shugaban kasar Sin, ya kai ziyara a Afirka har sau 3, inda ya ziyarci kasashe 14 na wannan nahiya. Ziyarar da shugaba Hu zai kai wa wadannan kasashe 4 na Afirka ziyara ce ta karo na 2 da ya yi bayan samun nasarar shirya taron koli na Beijing na dandalin tattaunawar yin hadin gwiwa a tsakanin Sin da Afirka a shekarar 2006. Shugaba Hu yana fatan ziyararsa za ta sa kaimi kan aiwatar da sakamakon da aka samu a yayin taron koli na Beijing a mataki na karshe, da kara zurfafa huldar abokantaka ta sabon salo a tsakanin Sin da Afirka bisa manyan tsare-tsare, da inganta hadin gwiwar aminci a tsakanin Sin da wadannan kasashe 4 domin samun bunkasuwa tare.

A lokacin da Mr. Zhai yake amsa tambayar wakiliyarmu dangane da dalilin da ya sa aka kara zurfafa zumunci a tsakanin Sin da Afirka, Mr. Zhai Jun ya bayyana mana cewa, abu mafi muhimmanci shi ne Sin da Afirka suna nacewa ga bin ka'idar nuna wa juna zuciya daya da zumunci da yin zaman daidai wa daida da mara wa juna baya da samun bunkasuwa tare a lokacin da suke raya hulda a tsakaninsu.

A karshen zantawar da ya yi tare da wakiliyarmu, Mr. Zhai ya nuna cewa, kasar Sin ta yi imani da cewa, bangarorin Sin da Afirka za su ci gaba da tsayawa tsayin daka kan nuna wa juna sahihanci da aminci da yin zaman daidai wa daida da nuna wa juna goyon baya da kuma samun bunkasuwa tare da inganta hadin kai da hadin gwiwa a tsakaninsu. Tabbas ne za su iya daga matsayin huldarsu zuwa sabon mataki.(Tasallah)