Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-02-05 17:08:57    
Kasar Sin ta bayar da shirin farfado da masana'antun saka da na kera injuna

cri
A ranar 4 ga wannan wata, majalisar gudanarwa ta kasar Sin ta zartas da shirin farfado da masana'antun saka da na kera injuna, ya zuwa yanzu, gwamnatin kasar Sin ta riga ta tanadi shirye-shirye guda 4 da ke cikin shirye-shiryenta goma na farfado da manyan masana'antu don shawo kan rikicin hada hadar kudi. Bisa shirin da aka tsai da, an ce, yanzu yawan kudin harajin da ake bugawa kan fitar da kayayyakin saka da tufafi kuma aka riga aka yi rangwame don da su ya kara karuwa zuwa kashi 15 cikin dari daga kashi 14 cikin dari da aka yi a da. Amma an bayyana cewa, kodayake kudin harajin da aka yi rangwamn komar da su ya yi kasa da adadin da aka kimanta a kai , wato kashi 17 cikin dari ke nan, amma zai iya kara wa masana'antun saka ribar da yawanta zai kai kudin Sin Yuan biliyan daya.

Masan'antun saka na kasar Sin sun zama daya daga cikin wadanda suke gamuwa da rikicin kudi mai tsanani . Daga watan Janairu zuwa watan Nuwamba na shekarar da ta shige, manyan masana'antun saka na kasar Sin a karo na farko sun samun raguwar karuwarsu ta cin riba a cikin shekaru 10 da suka wuce, kashi biyu cikin kashi uku na masana'antu na kasar Sin sun gamu da hasara ko ma  sun yi hasara mai tsanani.

Kakakin kungiyar masana'antun saka na kasar Sin ya bayyana cewa, a cikin shirin farfado da masana'antun saka, an bayar da cewa, za a ba da taimakon lamuni ga wasu masana'antun saka da suke tafiyar da harkokinsu yadda ya kamata tare da fama da wahalhalu cikin gajeren lokaci, sa'anan kuma, za a ba da karin taimako ga masana'antun saka matsakaita da kanana wajen biyan harajin da aka buga musu. Wannan ne labari mai kyau ga wadannan masana'antu. Kakakin ya ci gaba da bayyana cewa, aikin nan zai ba da taimakon sa kaimi ga masana'antun wajen kubutar da su daga wahalhalun da suke gamuwa sakamakon rikicin kudi. Ya kamata a aiwatar da manufar kudi da haraji wajen bayar da rancen kudin ga masana'antu ta hanyar banki, ta yin hakan mai yiyuwa ne masana'antu za su iya cim ma burinsu na samun isasshen kudin aiwatar da harkokinsu na yau da kullum.

Mataimakin shugaban kungiyar masana'antun saka ta kasar Sin Mr Zhang Yankai ya bayyana cewa, kodayake kudin harajin da aka komar da su bai kai wanda ake so ba, amma kashi daya cikin kashi dari na kudin harajin da aka komar da su ga masana'antun wadanda suke samun riba kadan na da amfani sosai. Ya bayyana cewa, dayake an daidaita farashin kudin Sin, kuma albashi ga ma'aikata ya kara karuwa, wasu masana'antu ba su sami riba da yawa wajen fitar da kayayyakinsu ba , shi ya sa ko kara kashi daya cikin dari shi ma na da amfani sosai ga wadannan masana'antu.

Wani mai binciken masana'antun saka na kasar Sin malama Ma Li ta bayyana cewa, gwamnatin Sin za ta kara ba da taimako ga manyan masan'antun da suke mai da hankali ga kiyaye muhalli, amma game da wadansu masana'natun da ke gurbatar muhalli, za a kara saurin kawar da su. Ta bayyana cewa, a cikin shirin, da akwai wasu abubuwan da aka tanada a cikinsa na da fa'ida ga masana'natu, amma za a mai da hankali ga kara ba da taimako ga wadanda suke tafiyar da harkokinsu da kyau.

Masanan ilmin tattalin arziki sun bayyana cewa, kasar Sin ta bayar da wannan shiri ne don sassauta matsin da ta samu wajen samar da aikin yi, ba da dadewa ba, wani babban jami'in kasar Sin ya bayyana cewa, yanzu a kasar Sin da akwai manoma 'yan ci rana da suka rasa aikin yi kuma suka riga suka koma kauyukansu da yawansu ya kai miliyan 20, amma masana'natun saka suna bukatar 'yan kwadago da yawa, shi ya sa in ana iya farfado da masana'natun saka, to za a iya kyautata halin da kasar Sin take ciki na samar da aikin yi.(Halima)