Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-02-04 08:35:19    
Sakamakon da 'yan wasan iyon kasar Sin suka samu a shekarar 2008

cri

Kamar yadda kuka sani, a shekarar 2008 da ta shude, 'yan wasan iyon kasar Sin sun samu babban sakamako mai faranta ran mutane. A yayin gasar wasannin Olympic ta Beijing, koda yake kungiyar wasan ninkaya ta kasar Sin ba ta samu lambobin zinariya 8 kamar yadda aka kimanta ba, amma ta samu lambobin zinariya 7 da lambar azurfa 1 da kuma lambobin tagulla 3, haka ya sa kungiyar ta rike da matsayinta na 'fitacciyar kungiya' a yayin wannan gasa. Kungiyar wasan iyon kasar Sin ita ma ta samu sabon ci gaba a yayin gasar, 'yan wasan iyon kasar Sin sun samu lambar zinariya ta farko ta gasar iyon maza a yayin gasar wasannin Olympic a tarihi. Ban da wannan kuma, 'yan wasa samari da yawan gaske sun kara nuna gwaninta bayan da suka shiga gasar wasannin Olympic ta Beijing. A cikin shirinmu na yau, bari mu yi muku bayani kan wannan.

Masu sauraro, kafofin watsa labarai na kasa da kasa su kan mayar da filin wasan motsa jiki mai siffar `tafkin wanka` wato `water cube` wuri mai ban mamaki, dalilin da ya sa haka shi ne domin 'dan wasan iyon kasar Amurka Michael Phelps ya samu sakamako mai ban mamaki, wato ya samu zama zakaran gasar wasannin Olympic bayan da ya yi nasara har sau 8 a nan. Wurin shi ma ya nuna wa duk duniya sakamako mai ban mamaki da kungiyar wasan ninkaya ta kasar Sin ta samu. A cikin gasannin ninkaya da aka shirya a yayin gasar wasannin Olympic ta Beijing, gaba daya kungiyar kasar Sin ta samu lambobin zinariya 7 da lambar azurfa 1 da lambobin tagulla 3, koda yake ba ta samu dukkan lambobin zinariya 8 ba, amma 'yan wasan Sin sun yi kokari. Game da wannan batu, mai jagorancin kungiyar Zhou Jihong ta nuna gamsuwarta ga sakamakon, ta ce, "Kungiyar wasan ninkaya ta kasar Sin ta samu lambobin zinariya 7 da lambar azurfa 1 da lambobin tagulla 3, wannan ya nuna mana cewa, 'yan wasanmu sun yi kokari, koda yake mun ji bakin ciki kadan, amma ana iya cewa, muna jin dadin sakamakon haka."

Game da kungiyar wasan iyon kasar Sin kuwa, ta samu lambar zinariya 1 da lambobin azurfa 3 da lambobin tagulla 2 ne kawai, sakamakon kungiyar wasan iyon Sin bai kai na kungiyar wasan ninkayan Sin ba, amma ta riga ta samu babban ci gaba. A shekarun 1990, kungiyar wasan iyon kasar Sin ta taba zama daya daga cikin kungiyoyi uku mafiya karfi a duniya tare da kungiyar kasar Amurka da ta kasar Australia. Daga baya kuma a kai a kai matsayinta ya dinga samu koma baya, dalilin da ya sa haka shi ne domin dabarar horaswa ba ta samu kyautatuwa ba. Ya zuwa shekarar 2007, abin bakin ciki shi ne halin nan bai canja ba. Amma a yayin gasar wasannin Olympic ta Beijing, 'yan wasan iyon kasar Sin sun ba da mamaki a filin wasan motsa jiki mai siffar 'tafkin wanka' wato 'water cube'. A yayin zagaye na karshe na gasar iyon da ake kira 'mallam-bude-littafi' na mata na mita 200, 'yar wasan kasar Sin Liu Zige ta samu zama zakara da minti 2 da dakika 4 da 18, ita ma ta karya matsayin bajimtar duniya na wasan. A yayin zagaye na karshe na gasar iyon 'free style' na maza na mita 400, 'dan wasa daga kasar Sin Zhang Lin ya samu lambar azurfa, wannan lambar yabo ta farko ce da 'yan wasan iyon kasar Sin bangaren maza suka samu a tarihin wasannin Olympic. Bayan gasa, Zhang Lin ya ce,  "Koda yake ban samu damar zama zakara ba, amma na yi namijin kokari, matsayina bai kai koli ba tukuna, na gamsu da sakamakon da na samu."

Amma babban malami mai horaswa na kungiyar wasan iyon kasar Sin Zhang Yadong yana ganin cewa, yanzu lokacin jin dadin cin nasara bai yi ba tukuna inda ya ce,  "A halin da ake ciki yanzu, 'yan wasan kasashen waje sun yi ta karya matsayin bajimtar duniya bi da bi. 'Yan wasanmu sun yi ta karya matsayin bajimtar Asiya ne da kasar Sin kawai, koda yake mun riga mun samu babban ci gaba, amma a takaice dai, matsayinmu bai kai na wasu kasashen ketare ba, shi ya sa dole ne mu ci gaba da yin kokari."

Lallai yanzu mun riga mun shiga shekarar 2009, sabon kalubale yana gabanmu, kungiyar wasan iyon kasar Sin ta riga ta fara yin aikin share fage domin shiga sabbin gasannin da za a shirya. Shahararriyar 'yar wasan ninkayar kasar Sin Guo Jingjing wadda ta taba samun damar zama zakara har sau biyu na gasar wasannin Olympic ta Beijing ta riga ta kai shekaru 27 da haihuwa yanzu, amma ana sa rai cewa, za ta sake shiga gasar wasannin Olympic mai zuwa wato gasar da za a shirya a birnin London na kasar Britaniya a shekarar 2012. Game da wannan, Guo Jingjing ta bayyana cewa,  "Da, ban san mene ne wasan ninkaya ba ko kadan, daga baya kuma na fara kaunarsa, yanzu dai ina jin dadin wasan sosai da sosai, ba na son daina wasan, in Allah ya yarda, zan ci gaba."

Game da kungiyar wasan iyon kasar Sin kuwa, ana sa ran fatan alheri gare ta, saboda yawancin 'yan wasanmu matasa ne. Alal misali, Zhang Lin yana da shekaru 21 da haihuwa ne kawai. Liu Zige ita ma tana da shekaru 19 da haihuwa ne kawai, za su dinga samu sabon ci gaba kuma makomarsu tana da haske. Babban mai horaswa Zhang Yadong ya ce,  "Dukkan 'yan wasanmu matasa ne, ko shakka babu, a shekarar 2012, za su kara samu babban sakamako, amma, kullum wasan iyon duniya yana samun ci gaba, sabbin 'yan wasa suna kara karuwa a duk duniya, saboda haka, kamata ya yi mu kara yin kokari."

A sa'i daya kuma, Zhang Yadong ya hakkake cewa, nan gaba, fitattun 'yan wasan iyo za su kara karuwa a kwana a tashi, musamman a nahiyar Asiya. Ya ce,  "A da, 'yan wasan iyo daga Amurka da Australia sun fi karfi kan wasan, amma yanzu halin nan ya fara canjawa a kai a kai, alal misali, 'yan wasa daga Japan da Korea ta kudu da kasar Sin su ma suna nuna ci gabansu ga duk duniya."

Kamar yadda za a ji: wakar nan tana da taken 'fiffiken da aka boye', a cikin wakar, 'yan wasan ninkayan kasar Sin wadanda suka taba samu zama zakarun duniya kamarsu Guo Jingjing da Wuminxia da Qin Kai da sauransu sun rera cewa, "A karshe dai, na ga sakamakon mafarkina, na rera waka da babbar murya, ba zan ji tsoro ba, kuma zan tashi sama tare da iska koda yake ba ni da fiffike."

A nan, bari mu nuna fatan alheri ga 'yan wasan iyon kasar Sin, muna fatan za su kara samun ci gaba kuma za su ci gaba da nuna karfinsu a dandalin wasan iyon duniya har abada.(Jamila Zhou)