Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-02-03 21:52:26    
Ba a tabbatar da amincewar da kungiyar Hamas za ta yi a kan dakatar da bude wutar yaki cikin shekara daya ba

cri

A ranar 2 ga wannan wata, kakakin kungiyar Hamas ya bayyana cewa, kungiyar Hamas ta riga ta amince da yarjejeniyar dakatar da bude wutar yaki da kasar Isra'ila cikin shekara daya, amma a wannan rana kuma, kakakin kungiyar Hamas da ke kasar Lebanon ya musunta yarjejeniyar, a sa'I daya kuma, shugaban hukumar ikon al'ummar Palesdinu Mr Abbas da shugaban kasar Masar Mubarac da ministan harkokin waje na kasar Saudi Arabiya Feisar sun yi shawarwari a tsakaninsu, abubuwan da suka yi shawarwari a kansu suna da nasaba da sake neman sulhuntawa a cikin Palesdinu da sauran batutuwa. Manazartan al'amarin sun bayyana cewa, ko za a iya cim ma buri na dakatar da bude wutar yaki cikin dogon lokaci a Zirin Gaza na da babban tasiri ga gudanar da ayyukan shimfida zaman lafiya a tsakanin Palesdinu da Isra'ila.

A ranar 1 ga wannan wata, kungiyar Hamas ta tura kungiyar wakilanta zuwa Alkahira don yin shawarwari da jami'an kasar Masar, inda suka yi shawarwari kan batun daddale yarjejeniyar dakatar da bude wutar yaki da kasar Isra'ila. A ranar 2 ga wannan wata, kakakin kungiyar Hamas da ke zirin Gaza ya bayyana cewa, Kungiyar Hamas za ta amince da yarjejeniyar dakatar da bude wutar yaki cikin shekara daya. Ya ce, idan za a kau da kangiyar da aka gitta a Zirin Gaza, da kuma bude kofofin dukkan tashoshin kwastan wadanda ke kunshe da tashar Rafah, to za a iya tattaunawa kan batun dakatar da bude wutar yaki cikin watanni 18. Amma yanzu ana bukatar ganin abun da zai faru a nan gaba, duk saboda kasar Isra'ila ba ta son ta yi rangwame a kan kokarin da kasar Masar ta yi ba. A wannan rana kuma, kakakin kungiyar Hamas da ke kasar Lebanon ya musunta yarjejeniyar dakatar da bude wutar yaki cikin shekara daya da kasar Isra'ila ba,

A ranar 27 ga watan Disamba na shekarar bara, kasar Isra'ila ta soma yin aikin soja a Zirin Gaza da ke karkashin mallakar kungiyar Hamas, ta hakan, Palesdinawa da yawansu ya kai 1400 ko fiye sun mutu a yayin da mutane 5500 suka ji raunuka. A ranar 18 ga watan Janairu na shekarar da muke ciki, bi da bi ne kasar Isra'ila da kungiyar Hamas suka yi shelar dakatar da bude wutar yaki a tsakaninsu a Zirin Gaza. Amma dakarun Palesdinu ba su dakatar da kai wa kasar Isra'ila hari ba.

Bayan da kasar Isra'ila da kungiyar Hamas suka yi shelar dakatar da bude wa juna wutar yaki, kasar Masar wadda take yin shawo kai a tsakanin kasar Isra'ila da kungiyar Hamas ta yi shawarwari da wakilan bangarorin biyu bi da bi ta yadda za a daddale wata yarjejeniyar dakatar da bude wutar yaki a tsakaninsu, amma kasar Isra'ila da kungiyar Hamas suna da sabani sosai a tsakaninsu, shi ya sa ba a iya daddale yarjejeniyar ba.

A ranar 1 ga watan Fabrairu na shekarar da muke ciki, shugaban hukumar ikon al'ummar Palesdinu Abbas da shugaban kasar Masar da ministan harkokin waje na kasar Saudi Arabbiya sun yi shawarwari a birnin Alkahira, bangarorin uku sun yi shawarwari kan batutuwan da suka shafi matakan da za a dauka don dakatar da bude wutar yaki cikin dogon lokaci a Zirin Gaza da sauran batutuwa, amma bangaren Abbas da kungiyar Hamas sun sami sabani sosai a tsakaninsu, saboda haka suna bukatar yin dogon tafiya a tsakaninsu wajen cim burin samun sulhuntawa.

A ranar 2 ga wannan wata, an kira taron Herzliyya, inda shugaban kasar Isra'ila Peris ya yi jawabi cewa, kasar Isra'ila da bangaren Palesdinu sun riga sun yi shawarwarin shimfida zaman lafiya a tsakaninsu cikin shekaru 16 da suka wuce,ana bukatar nuna karfin kagowa wajen warware gardamar da ke tsakanin kasar Isra'ila da Palesdinu. Ya bayyana cewa, dole ne gwamnatin Isra'ila ta ci gaba da kokarinta na sa kaimi ga shimfida zaman lafiya a Gabas ta tsakiya. In hakan za a yi, to babbas ne za a sami makoma mai kyau wajen gudanar da shimfida zaman lafiya a Gabas ta tsakiya.(Halima)