Yanzu a wurare daban-daban na kasar Sin, jama'a suna bukukuwan taya murnar shigowar sabuwar shekara bisa kalandar gargajiya ta kasar Sin. Bisa al'adar gargajiya ta Sinawa, yayin da suke taya murnar sallar bazara, Sinawa su kan sayi abubuwa da dama, da kaiwa gidajen dangogi da abokan arziki bakunci domin nuna fatan alheri a cikin sabuwar shekara.
A birnin Zhengzhou na lardin Henan dake tsakiyar kasar Sin, wani tsohon ma'aikaci wanda ya yi ritaya Mista Liu Jinli yana taya murnar sallar bazara tare da dansa a wannan shekara. A cikin 'yan shekarun baya, dan Mista Liu Jinli wanda ke shan aiki a lardin Guangdong dake kudancin kasar Sin ba ya komawa gida a lokacin sallar bazara. A shekarar da muke ciki, dansa tare da matarsa sun koma garinsu dake lardin Henan. Mista Liu Jinli ya ce, dansa ya yi watsi da karin albashin da zai samu idan zai yi aiki a lokacin sallar bazara, ya koma gida domin haduwa da iyayensa, inda Mista Liu Jinli ya ce:
"A lokacin sallar bazara, diyata, da dana, gami da jikokina dukkansu sun komo gida. Na shirya abinci iri daban-daban a jajibirin sabuwar shekara bisa kalandar gargajiya ta kasar Sin, kuma mun ji dadinsa kwarai da gaske."
Ko da yake a halin yanzu rikicin hada-hadar kudi na cigaba da addabar kasashen duniya da dama, amma Sinawa ba su sauya al'adarsu ba ta sayen abububuwa a lokacin sallar bazara. A birnin Guangzhou dake kudu maso gabashin kasar Sin, kasuwanni daban-daban suna shirya ayyuka iri-iri domin jawo hankalin masu sayayya. Wata mazauniyar birnin mai suna Jiang Chaochang ta ce:
"Na sayi wasu tufafi da takalma, da abinci iri-iri. Na kashe Yuan dubu daya ko biyu don sayen kayan sutura, wanda ya fi na shekarun baya."
A waje daya kuma, shirya bikin yin baje-koli cikin dakunan ibada, da yin yawon-shakatawa a lambun shan iska, muhimman ayyuka ne da Sinawa suke yi domin taya murnar sallar bazara. A lokacin sallar bazara ta wannan shekara, an shirya bukukuwan yin baje-koli cikin dakunan ibada a wurare daban-daban na birnin Beijing, irin bikin baje-koli da ake yi a Changdian da Ditian sun fi jawo hankalin jama'a. A lokacin sallar bazara kuma, Sinawa su kan yi amfani da kayayyaki masu sigar musamman ta al'adun gargajiya ta kasar Sin a fannin kawata gidaje, ciki har da jajayen takardun da ake mannawa a gefunan kofa don isar da sakon alheri, da manyan fitilu masu launin ja da dai sauransu. Mai kantin sayar da kayayyaki da tsarabobin al'adun gargjiya ta kasar Sin dake yammacin birnin Beijing, Madam An Jing ta ce:
"Galibin abubuwan da jama'a suka fi saya su ne zane-zanen da akan manna a jikin bango, da takardun da akan yanyanka dake da hotuna iri-iri don mannawa a tagogi da kofofi, da dai sauran kayayyaki masu sigar musamman na al'adun gargajiya."
A ranar 12 ga watan Mayu na shekarar da ta gabata, an yi girgizar kasa a gundunar Wenchuan ta lardin Sichuan da kewayenta. Sakamakon taimakon da gwamnati da bangarori daban-daban suka bayar, mutanen da suka rasa matsugunansu sun yi kaura zuwa sabbin gidajen kwana kafin karshen shekarar bara, ta yadda za su iya yin sallar bazara cikin annashuwa. Daliba Wang Jinxiang ta jami'ar koyon aikin malanta ta Sichuan ta bayyana fatanta a sabuwar shekara, inda ta ce:
"Ina fatan iyayena za su samu koshin lafiya a sabuwar shekara. Haka kuma ina fatan zan sami aikin yi mai gamsarwa don kwantar da hankalin iyayena."(Murtala)
|