Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-01-28 15:40:10    
Matan gidan Manoma Zhu Zhanxiang da rayuwarta

cri
Gidanta yana cikin kauyen Fushan na mallakar garin Zhujia na gundumar Linkou ta lardin Heilongjiang da ke arewa maso gabashin kasar Sin.A shekara ta 1978,Zhu Zhanxiang ta yi aure da mijinta tare da kudin Sin RMB Yuan hamsin da ta yi aro daga hukumar garin.Wata ka'idar da hukumar garin ta kafa a wancan lokaci ta bayyana cewa idan ka dasa itatuwa a tsaunuka,ka iya biyan bashin hukuma, rancen kudin da za ka iya samu gwargwadon yawan itatuwa da ka dasa.Da haka Zhu Zhanxiang da namijinta sun kuduri aniyar dasa itatuwa domin biyan bashin.Daga nan ta fara rayuwarta ta dasa itatuwa.

"Da na fara dasa itatuwa,na ga itatuwa na girma da sauri,itace na kara tsawonta da centimeter 80 ko 90 a shekara guda.Ina sha'awa,daga nan na dasa itatuwa a duk wani wurin da ke da bushe."

Tun daga shekara ta 1985 aka fara tafiyar da wata "munufar raba ganduna bisa kwangila" a kauyen Fushan na mallakar garin Zhujia.Daga nan manoma na iya yin aikinsu a gonakansu ko wace rana,Zhu Zhanxiang tana dasa itatuwa a tsaunuka.A yanayin bazara na shekara ta 1988,Zhu Zhanxiang ta ba gonakan da ta ke yin kwangila ga makwabtanta ta bar kauyen da take zama cikin shekaru goma tare da iyalinta sun tsunguna a wurin da take dasa itatuwa cikin duwatsu,babu dakin kwana a can,sai ta da namijinta sun haka ramuka guda biyu domin zamansu,babu wutar lantarki,babu rediyo,babu waya,zamansu a saukakke.Daga nan Zhu Zhanxiang da iyalinta suna zama rakuman,suna tare da itatuwan da iyalinta suka dasa.

Yanayin bazara gajeri a arewancin kasar Sin.Zhu Zhnxiang ta kan tashi daga barci yayin da zakara ta fara cara,bayan da ta shirya abinci domin danta,sai ta je wurin da ake bukata domin kula da kanana itatuwa.Da magariba ta dawo gida.Bisa aikin tukuru da ta yi da iyalinta cikin shekaru da dama,,itatuwan dake cikin duwatsu na kara yawa,kuma suna girma sosai.amma lafiyar Zhu Zhanxiang ta fara lalacewa.

A wani yanayin bazara,Zhu Zhanxiang ta fara jin zafi a cikinta,amma yanayi ne na dasa itatuwa,sai ta yi hakuri da zafin da take ji ta cigaba da dasa itatuwa har zuwa lokacin da ta kasa hakuri da zafin,sai ta je asibit.Bayan an yi mata bincike,ashe an gane cewa tana fama da sankarar tumbi.Da samun labarin nan,Zhu Zhanxiang ta buga waya zuwa ga mijinta daga asibiti nan da nan,kuma ta bar wasiya.

"Ni ce na dasa itatuwa a kan tsauni.Ni ce nake zama a kan tsauni lokacin da nake da kuruciya.Bayan mutuwata ina so a baza tokar gawata a kan tsaunin nan.Wannan yana nufin cewa ina kare wannan tsauni a rayuwata ko bayan mutuwata.

Daga baya aka sake dudduba lafiyar jikinta,likitan ya yanke magana cewa ba ciwon sankaro ya kame ta ba ciwon ciki ne ya same ta..Da samun wannan labari,hankalinta ya kwanta,ta sake koma tsaunin da ta dasa itatuwa,ta ci gaba da aikinta.Kamar yadda ta fada cewa ba ta so ta bata minti daya.renon tsiran itatuwa ba aiki ne mai sauki ba yana bukatar fasahohi da yawa,haka kuma ba aiki mai sauki ba ne ga wannan manomiyar wadda ba ta yi karatu ba.Da haka Zhu Zhanxiang ta gayyaci kwararren ilimin itatuwa zuwa gidanta da ya koyar mata da ilimin renon tsiran itatuwa.Kan kare tsiran itatuwa,Zhu Zhanxiang ta kago wata dabarar kare tsiran ta akwatin dumama yanayi.Ta haka ta kiyaye tsiran itatuwa yadda ake bukata ko a lokacin kankara.A yanayin bazara mai zuwa,ta dasa tsiran itatuwa,suna girma sosai.

Daga bisani kananan itatuwan da aka samu daga gandun renon tsirai tsira na gidan Zhu Zhanxiang ba ma kawai sun biyan bukatun gidanta na dasa itatuwa ba har ma an sayar da su ga sauran mutanen da ke bukatar dasa itatuwa na garuruwa.Mr Mei Jianzhi,shugaban gandun dasa itatuwa na gundumar Linkou ya fada cewa:

"nau'o'in bishiyoyin da aka samu daga gandun renon tsirai tsiran itatuwa na Zhu Zhanxiang sun kara yawa,ribar da ta samu na karuwa."

Ban da wannan akwatin dumama yanayin da ta kago,ta kuma kage wasu cikakkun kayayyakin fesa ruwa.ta kera bakin kayan fesa ruwa ne da abin torcila da ba a yi amfani da shi ba,ta kuma sanya kayan a kan dutse mafi tsayi,daga nan ruwan na iya kwarara.Mijinta Liu Zhongxiang ya kira kayan fesawa da sunanta.Da Zhu Zhanxiang ta samu fasahar renon tsiran itatuwa,zaman iyalinta na kara kyautatuwa.Bayan da ta samu wadata,ba ta gamsu da abin da ta samu ba,tana so ta ba da taimako ba tare da biyan kudi ba ga 'yanuwnta dake cikin kauyen,su mai da busasun tsaunuka wurin bishiyoyi da ciyawa da furanni,zamansu ma na kara inganta.Manomi Yu qinjiang ya ce:

"Ta taimake ni sosai,ta ba ni tsiran bishiyoyi dubu biyu ba tare da biyan kudi ba,sai na dasa itatuwa in samu riba.na yi mata godiya.Ta isa abin koyi gare ni. "

A karkashin jagorancin Zhu Zhanxiang,ko wane iyali a kauyen Fushan yana da nasa gandun itautwa,fadin filin dasa itatuwa ya kai kashi 83 bisa kashi dari na daukacin filayen garin Zhujia.Bisa kimtan da wani sashen kula da dazuzuwan kasar Sin ya yi,an ce A cikin shekaru 29 da suka shude,Zhu Zhanxiang ta dasa bishiyoyi kimanin dubu dari uku a fadin tsauni kadada 150,darajar itattuwan da ta dasa ta kai kudin Sin RMB miliyoyi. (Ali)