Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-01-28 15:34:18    
Motsa jiki da shan abinsha da ke kunshe da sinadarin caffein za su iya shawo kan sankarar fata

cri
Bisa sakamakon wani bincike da kasar Amurka ta bayar, an ce, shan abinsha da ke kunshe da sinadarin caffein kamar yadda ya kamata, da kuma motsa jiki za su iya yin rigakafi kan illar da hasken rana ke yi wa fatar dan Adam, ta yadda za a iya rage yiyuwar kamuwa da sankarar fata.

Manazarta na jami'ar Rutgers ta jihar New Jersey ta kasar Amurka sun bayar da rahoto a cikin jaridar kwalejin ilmin kimiyya na kasar, cewa wani irin sinadarin ultraviolet da ke cikin hasken rana wanda ake kiransa UVB muhimmin sanadi ne wajen haifar da sankarar fata. Irin wannan sinadarin ultraviolet zai iya lalata DNA da ke cikin kwayoyin jikin dan Adam, ta haka za su zama munanan kwayoyi wajen haddasa sankara. Ban da wannan kuma binciken ya gano cewa, watakila motsa jiki da kuma shan abinsha da ke kunshe da sinadarin caffein kamar yadda ya kamata za su iya ba da taimako wajen kashe wadannan munanan kwayoyi.

Manazarta sun zabi beraye da ba su da gashi domin yin musu gwaji, dalilin da ya sa haka shi ne sabo da idan ba su da gashi, to fatunsu za su fi saukin jin raunuka sakamakon hasken rana. An kasa wadannan beraye cikin rukunoni hudu. Beraye na rukunin farko sun shan ruwan da ke kunshe da sinadarin caffein, wanda yawansa ya yi daidai da kofi na kwafi guda ko biyu da dan Adam yake sha a ko wace rana. Beraye na rukuni na biyu sun motsa jiki a cikin kejin da ke aka iya jure shi. Beraye na rukuni na uku kuwa sun sha ruwan da ke kunshe da sinadarin caffein da kuma motsa jiki, na rukuni na hudu ba su yi kome ba.

To, wane irin bambanci ne da za a sha a tsakanin wadannan rukunonin hudu bayan da aka yi gwaji gare su? Masu sauraro, yanzu sai ku shakata kadan, daga baya kuma za mu ci gaba da yin muku bayani kan batun.

Bayan da suka yi gwaji ga wadannan beraye, manazarta sun ajiye berayen cikin wani dakin da ke da fitilu na UVB, kuma sun gano cewa, lallatattun kwayoyin beraye na DNA nasu sun mutu bisa mataki daban daban. Dalilin da ya sanya mutuwar kwayoyi shi ne sabo da kwayoyin sun kashe kansu domin kiyaye lafiyar jiki.

Kuma manazarta sun nuna cewa, idan kwayoyin da suka ji raunuka sakamakon hasken rana suka kashe kansu, to ba za su zama kwayoyin sankara ba. A cikin binciken da aka yi, an gano cewa, idan an kwatanta da beraye na rukunin da ya zama ma'aunin bincike, yawan kwayoyin da suka mutu na rukuni na farko ya yi yawa har ya karu da kashi 95 cikin dari, kuma wannan jimla ta karu da 120 cikin dari ga rukuni na biyu, haka kuma jimlar ta karu kusan kashi 400 cikin dari ga rukuni na uku.

Manazarta sun bayyana cewa, ya zuwa yanzu ba a san dalilin da ya sa motsa jiki da kuma shan abinsha da ke kunshe da sinadarin caffein suke iya yin rigakafi kan sankarar fata ba, shi ya sa ake bukatar ci gaba da yin nazari.

Bisa kididdigar da cibiyar nazarin sankara ta kasar Amurka ta bayar, an ce, sankarar fata da hasken rana ya haddasa wani irin sankara ne da Amurkawa su kan kamu da ita, kuma yawan mutanen da suka gamu da sankarar ta zarce miliyan daya a ko wace shekara.

To, jama'a masu sauraro, shirinmu na yau na ilmin zaman rayuwa ke nan. Da fatan kun karu, da haka Kande da ta shirya muku wannan shiri kuma ke cewa a kasance lafiya, sai mako gobe war haka idan Allah ya kai mu.(Kande Gao)