Ko da yake a halin yanzu, lokacin tsananin sanyi ya yi a yawancin kasar Sin, amma a birnin da ke kuriyar kasar Sin ta kudu, wato birnin Sanya na lardin Hainan, ya zuwa yanzu dai ana rana sosai, kuma sanyi bai iso ba, yawan zafi ya kai digiri 20 ko fiye bisa ma'aunin sentigrade, shi ya sa mutane na sassa daban daban suka zo wannan birni da ya tilo da ke yankin zafi a bakin teku a kasar Sin domin gudun sanyi.
Madam Yang da kuma iyalinta sun je Sanya ziyara ne daga garinsu na lardin Jiangxi da ke yankin tsakiya na kasar Sin. Saukarta ke da wuya a Sanya, sai ta ji bambancin da ke tsakanin wurin da garinsu. Ta ji dadin sakin jiki bayan da ta cire tufafin maganin sanyi. Ta ce,
"Na zo nan ne ina sanye da tufafi da yawa, amma isowata ke da wuya, sai na cire tufafi da yawa. Ni'imtattun wurare a nan na da kyan gani a tare da muhalli mai kyau. Mutane kan ji farin ciki sosai a nan."
A wajen mutanen da suka kai wa Sanya ziyara a karo na farko, wurin yawon shakatawa mai suna "Tian Ya Hai Jiao", wato kuriyar duniya da ke da ma'anar musamman. Wurin yawon shakatawa mai suna "Tian Ya Hai Jiao" shi ne alamar kuriyar duniyarmu a idon Sinawa bisa al'adun gargajiya ta kasar. Tun can da yana kasancewa tamkar alamar kaunar da ke kasancewa har abada. A zamanin da mutanen Sin sun saka kalaman "Tian Ya" da kuma "Hai Jiao" kan duwatsu 2 da ke makwabtaka da juna.
Yanzu wannan wurin yawon shakatawa ya zama wuri ne da ya ga soyayya a kansa. A ko wace shekara, a kan yi bikin aure na duniya a wajen, inda amare da angwaye na sassa daban daban na gida da na waje su kan yi aure tare.
A kusa da wurin yawon shakatawa na "Tian Ya Hai Jiao", akwai wani wurin yawon shakatawa na daban, inda aka nuna al'adun addinin Buddha da na neman tsawon rai tare a wurin gargajiya mai kyan gani irin na yankin zafi da ke bakin teku, sunansa shi ne shiyyar yawon shakatawa ta Nanshan. Gunkin Avalokiteshvara, wato Kuan Yin a bakin Sinawa mai tsayin mita 108 a bakin kudancin teku na kasar Sin na matsayin alamar shiyyar yawon shakatawa ta Nanshan, wadda ta kan nuna basira da kuma burin samun jituwa.
Kullum ana iya ganin dimbin masu yawon shakatawa da suke yin ziyara a shiryyar yawon shakatawa ta Nanshan, da yawa daga cikinsu iyali-iyali ne. Liu Yongxue tare da iyalinsa dukkansu 8 sun zo nan Sanya ziyara daga Beijing, suna farin ciki sosai. Mr. Liu ya ce,
"Shekaruna sun kai 86 da haihuwa. Dukkanmu 8 mun zo nan ne ziyara."
Li Xiuluan, matar wani dansa ta yi karin bayani da cewa,
"Babana bai taba zuwa Hainan ba, kuma yana kasancewa cikin koshin lafiya, shi ya sa muka zo nan ziyara tare da shi a daidai lokacin hutu. Ya kan ji kadaici saboda yana zama shi kadai a gida kullum. Mun zo nan ne tare da shi, inda muka more wa idonmu da kyawawan wurare a Sanya. Muna farin ciki kwarai da gaske."
Liu Bo, wani da ne na Mr. Liu Yongxue, ko da yake ya sha zuwa nan Sanya, amma ya kan nuna sha'awa sosai kan ni'imtattun wurare a wajen. Ya ce,
"In mun tsaya a kan gindin babban dutse na Nanshan, iska na busawa, ga kyakkyawan teku da ni'itattun wuare da tsire-tsire, to, za mu iya gane me ya sa aka kwatanta tsawon ran mutum da tsawon kasancewar babban dutse na Nanshan. Duk wanda ya zo nan yana son yada zango a wajen cikin karin lokuta a sakamakon kyan muhalli. In mun sami dama ta daban, tabbas ne za mu kawo ziyara nan."
A duk bukukuwan gargajiya na kasar Sin, a kan shirya harkokin musamman don neman samun alheri da zaman lafiya a babban dutse na Nanshan a Sanya. Zheng Rui, manajan sashen tsara shiri kan tafiyar da kamfanin raya aikin yawon shakatawa da al'adu na babban dutse na Nanshan ya yi mana karin bayani cewa, a gabanin sabuwar shekara, a kan buga kararrawar gidan ibada na wurin, idan aka buga kararrawar sau 108 da zummar kawar da matsaloli masu nau'o'i 108 da mutane kan fuskanta, ta haka za a iya samun alheri.
Baya ga wadannan shahararrun wuraren yawon shakatawa, a shekarar bara, Sanya ta fito da sabon wurin yawon shakatawa wato kungurmin daji na Ya Nuo Da. A kungurmin daji na Ya Nuo Da, ana iya ganin dogayen itatuwa da yawa. Kasancewa cikin wannan kungurmin daji da ke kusa da birnin Sanya ya iya nisantar da mutane daga hayaniyar da ake samu a birane, mutane kan iya hutawa sosai da kuma barin bacin zuciya da matsalolin ayyuka a cikin muhalli mai kyau.
Hasken rana da rairayin bakin teku da koren tsire-tsire da kuma iska mai kadawa, a Sanya ana iya samun albarkatu da yawa da ke iya kiwon lafiya, kuma za su iya jawo dimbin mutane da su yi bulaguro a wannan birni. Ban da wannan kuma, kyan ganin Sanya ya zaunar da shahararrun otel-otel din na duniya da yawa a wurin, wadanda suke bai wa masu bulaguro hidimomi daga kananan fannoni da kuma masu nau'o'i daban daban. A cikin dakin kwanansu, mutane ba safai su kan tashi daga barci da wuri wuri ba kullum. Bayan da suka ci abinci mai dadi da safe, su kan kwanta a rairayin bakin teku a karkashin haske rana, ko kuma su shiga cikin ruwan dumi ko kuma su yi ninkaya, ta haka suna jin dadin zamansu a duk rana.
A shekarun baya, birnin Sanya ba ma kawai ya yi suna ne a gida da kuma waje a matsayin wurin hutawa ba, sa'an nan kuma, ya zama gari ne na daban da mazauna yankunan tsakiyar kasar suke neman samuwa. A halin yanzu, a wannan birni, ana fitowa da dimbin tsoffafin da su kan zo Sanya a lokacin hunturu, sun kuma koma gida a lokacin zafi. A titunan birnin, ana iya ganin tsoffaffi mata da maza masu amfani da yaren sauran sassan kasar Sin suna sayen kayan lambu a kasuwa, su kuma yi yawo a bakin teku.
Fan Zheng, mai shekaru 80 ko fiye da haihuwa, wani mazauna lardin Sichuan ne da ya yi ritaya daga aiki. A shekarar 2006 da ta gabata, ya kawo wa Sanya ziyara a karo na farko da zummar hutawa kadan. Amma hasken rana da kyakkyawan muhalli sun sa shi ya saki jiki sosai, ya kuma samu sassaucin ciwon da ya dade yana fama da shi. Yanzu ya shiga rukunin tsoffafin da su kan zo Sanya a lokacin hunturu, su kuma koma gida a lokacin zafi. A ko wane lokacin hunturu, ya kan yi watanni da dama yana zaune a Hainan. Mr. Fan ya gaya mana cewa,
"Babu lokacin hunturu a nan Sanya. Wannan yana da amfani ga mu tsoffafin da muke fama da ciwon zuciya da na hanyar numfashi. Mutanen da suka zo daga yankin arewa maso gabashin kasar da lardin Sichuan da birnin Chengdu sun fi rinjaye a tsakanin masu yawon shakatawa a wurin. Mu kan yi watanni 3 zuwa 4 muna zaune a nan."
Madam Xie ta zo ne daga birnin Nanjing ta sayi gida a Sanya. A watan Nuwamba na ko wace shekara, a kan yi sanyi sosai a garinta na Nanjing, shi ya sa abokai da dangogi da ita su kan zo Sanya domin gudun sanyi. Dukkansu sun nuna babban yabo kan muhallin wurin. Madam Xie ta ce,
"Na zo nan ne da zummar gudun sanyi a ran 2 ga watan Nuwamba na shekarar bara. Yawan zafi ya kai digiri 5 a karkashin sifiri a Nanjing. Amma a wurin yanayi na da kyau, ba na bukatar sanya tufafin maganin sanyi."
A sakamakon sabuwar shekara bisa kalandar gargajiya ta kasar Sin, Sanya na sake shiga lokacin da aka fi cin kasuwar yawon shakatawa a ko wace shekara. Yanzu Sanya tana zama tamkar aljanna ce a zukatan mutane da zummar gudun sanyi a kwana a tashi.
|