Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-01-27 19:58:21    
More bakinku a titin Guijie

cri
Masu sauraro, in an tabo magana kan abinci mai dadi na birnin Beijing, to, shahararren titin Guijie shi ne wuri mafi dacewa a gare ku. Wannan titi ne da ya yi suna saboda abinci mai dadi da ake samu a titi daya tilo da ake sayar da abinci mai dadi har na tsawon awoyi 24 na ko wace rana a nan Beijing. A kan wannan titi, ana iya dandana dukkan abinci da ke samun karbuwa sosai a Beijing, kamar kayan abinci mai yaji na lardin Sichuan da gasassun namun teku masu dadi da kuma gasasshiyar agwagwa ta Beijing. Yau ma bari mu ci albarkacin bakinmu a wannan titi.

"Titin Guijie, wuri ne na musamman na cin abinci da daddare. Sa'an nan kuma, abinci na da kyau a nan."

"Ina son dafa yankakken nama da ganyaye a cikin tukunya. Wannan gidan abinci da ke nan titin Guijie yana da kyau, shi ya sa nake ta zuwa nan."

"Titin Guijie ya yi suna sosai da sosai, ana sayar da abinci mai dandano a duk wannan titi."

"Ina son cin abinci irin na kasar Rasha. Wannan gidan abinci ya fi kyau a gare ni, kuma farashin abincin na da rahusa."

"A kan shirya harkoki da yawa a wannan titi mai ban sha'awa, inda a kan sami mutane da yawa. Titin ya fi dacewa da samun sabbin abokai. Haka kuma, ya fi nuna halin musamman na al'adun kasar Sin."

"Mu kan zo wannan gidan abinci saboda abinci mai dadi da kuma kyawawan hidimomin da ake bayarwa. Mu kan zo nan a kalla sau daya a ko wane mako."

Masu sauraro, kalaman da kuka saurara a yanzu yabo ne da masu cin abinci da suka zo daga sassa daban daban na duniya suka nuna wa titin Guijie. Titin Guijie na cikin yankin Dong Zhi Men Nei da ke gundumar Dongcheng na birnin Beijing. A kan wannan titi mai tsawon mita 1400 ko fiye, akwai gidajen abinci manya da kanana misalin 150, adadin gidajen abinci da ke cikin ko wane murabba'in mita na da yawa, fiye da na sauran wuraren da ke Beijing. Da rana, babu mutane da yawa a titin Guijie, amma bayan da duhun dare ya yi, wannan titi sai ya fara cika da mutane. Ana fara kunna fitilun da ke gaban kofofin gidajen abinci daya bayan daya, sa'an nan kuma, kamshin abinci ya game duk titin. Masu cin abinci kan mamaye dukkan kujerun da ke gidajen abinci cikin sauri, wadanda suka makara kuwa, ba yadda za su yi, sai su jira cikin hakuri a gaban kofofin gidajen abinci.

Titin Guijie ya zama wani titi na farko da ake sayar da abinci duk rana da dare a ciki a nan Beijing a shekarar 1995. A sakamakon yaduwar kayan abinci mai yaji irin na lardin Sichuan da birnin Chongqing a nan Beijing, kayan abinci irin na Sichuan ya fara samun rinjaye a titin Guijie tare da kayayyakin abinci irin na sauran wuraren kasar, har zuwa yanzu titin Guijie yana kasancewa kamar yadda yake ciki a wancan lokaci. Domin dacewa da mazauna Beijing, an waiwayi halin musamman na abinci irin na Beijing a lokacin da ake dafa abinci a titin Guijie.

A titin Guijie, masu talla su kan kira masu wucewa dan su shiga gidajen abincinsu kamar abun da kuku saurara a yanzu. Akwai gidajen abinci da yawa a wannan titi, haka kuma akwai dimbin masu cin abinci. Wasu baki su kan ratsa duk birnin Beijing kan keke domin cin abinci a titin Guijie. Wasu shugabannin masana'antu kan ci abinci a titin bayan da suka tuka mota har na tsawon daruruwan kilomita dan zuwa wajen. Wasu matasa su kan dandana abinci mai dadi a titin tare da abokansu. Wasu tsofaffi kuwa, su kan jira har na tsawon awa guda domin cin abinci mafi tsantsar dandano da gidan abinci da ya fi dadewa yake samarwa. Mr. Duan ya kan ci abinci a wani gidan abinci da ke titin Guijie, yana son kayan abinci da ake sayarwa a nan sosai. In babu kujera, to, ya kan jira ko da yanayi ba ya da kyau. Mr. Duan ya gaya mana cewa,

"Ina son kayan abinci mai yaji. Abincin da ake sayarwa a nan na da tsantsar dandano. Ba na iya sifanta wannan dandano sosai, amma ina son wannan dandano sosai. Ba na zuwa sauran gidajen abinci, sai wannan kawai."

Ko wane gidan abinci da ke titin Guijie na da mahalartansa. Xiao Meng, mai jagorar masu cin abinci a wani shagon sayar da kayan kalaci, ya gaya mana cikin alfahari cewar,

"Kuku-kukun da ke aiki a shagonmu na da kyau kwarai! In ba su da kwarewar dafa abinci, to ba za mu iya samun masu cin abinci masu yawan haka ba. Ana shiga shagonmu ne ba domin muna lallashi kawai ba. Ga wadanda suke cin abinci a shagonmu a yanzu, yawansu ya wuce kashi 80 cikin dari su kan zo shagonmu kullum, watakila su kan zo sau 2 ko kuma 3 a ko wane mako, har ma wasu su kan zo shagonmu bayan ko wane kwana daya. In babu kujera, to, su kan jira a maimakon zuwa sauran gidajen abinci."

Baki da yawa da suke zaune a nan Beijing su kan ci abinci a titin Guijie. Guillaume da ya zo daga kasar Faransa yana daya daga cikin wadannan bakin da su kan more bakinsu a titin Guijie. Ya kan shiga gidajen abinci daban daban tare da abokansa a ko wane karo. Ya gaya mana cewa,

"Mun taba shiga ko wane gidan abinci da ke titin Guijie. Mu kan canza zuwa wani a ko wane karo. Wannan gidan abinci da muke ciki a yanzu yana samar mana abinci mai dadi kuma mai yaji, kamar dafa kifi a cikin tukunya. Muna son ci abinci a nan tare da abokai, mu kan dauki dogon lokaci na cin abinci. Muna cin abinci, muna shaye-shaye, muna hira, muna farin ciki sosai."

Jennifer da Gaby sun zo ne daga kasar Brazil. A cikin shekara guda da rabi da suka wuce, a ko wane sati su kan je wani gidan dafa yankakken nama da ganyaye a cikin tukunya a titin Guijie. Jennifer ta ce,

"Kayan abinci na da kyau da dadin ci sosai a nan amma babu tsada sosai. Masu talla da ke aiki a nan mun san juna sosai. Su kan karbi baki da hannu biyu biyu, shi ya sa mu kan zo nan. A ganina, wannan gidan dafa yankakken nama da ganyaye a cikin tukunya ya fi kyau a duk Beijing."

Liu Jinjun, wanda ke aiki a wani gidan abinci matsakaici, ya bayyana cewa, a ko wace rana, baki da yawa su kan zo gidan abincinsa, sabis din da ke aiki a gidan abincinsa sun iya kula da su cikin Turanci . Ya ce,

"Baki su kan ci abinci a gidan abincinmu, saboda muna da takardar sunayen kayayyakin abinci a Turance, haka kuma, sabis da yawa da ke aiki a nan sun iya Turanci. A cikin wadannan bakin da su kan zo gidan abincinmu, wadanda suka zo daga kasashen Birtaniya da Rasha sun fi rinjaye. Su kan zo nan a ranar Lahadi."

Masu sauraro, a sakamakon shirya gasar wasannnin Olympic a nan Beijing, an yi kwaskwarima kan titin Guijie daga dukkan fannoni, shi ya sa wannan titi ya sami kyautatuwa sosai a fannonin yin kiliya da muhallin cin abinci. Mr. Liu ya yi farin ciki saboda ganin wadannan sauye-sauye a titin Guijie, ya ce,

"Mun kebe wa wadanda ba su shan taba wani waje na musamman a bene na biyu na gidan abincinmu. Sa'an nan kuma, masu cin abinci da yawa ko suna cikin yankin shan taba, ba su shan taba, a ciki su kan fita daga gidan abincinmu, su sha taba a waje."

Titin Guijie ya riga ya zama alamar Beijing a fannin al'adun abinci, saboda mutane kan iya dandana kayan abinci da ake yayi a Beijing a wannan titi, kamar jatan lande da aka dafa tare da barkono da yaji, da gasasshen kifi da na fiffiken kaji. Bugu da kari kuma, titin Guijie yana matsayin muhimmin bangare na al'adun zaman rayuwar mazauna Beijing da dare. Shi ba titin sayar da abinci ne kawai ba, ana iya kara fahimta kan sassan zaman rayuwar yau da kullum ta farar hula mazauna Beijing. Masu sauraro, in kuna sha'awar wannan titi, titin Guijie na maraba da zuwanku.