Masu sauraro, Kabilar Kazakstan, wata kabilar gargajiya ce ta makiyaya da ke zaune a arewacin jihar Xinjiang ta kabilar Uygur da ke arewa maso yammacin kasar Sin, tantuna masu saukin kafawa da riguna marasa kyau da aka yi da fatar tumaki alamu ne na zaman rayuwar makiyaya 'yan kabilar Kazakstan a cikin shekaru darurruwa. Amma yanzu, wasu mutane daga cikinsu sun riga sun shiga sabbin dakunan kwana da aka gina su da bulo, da kuma kallon shirye-shirye talibijin a kewayen risho. Yanzu kalmar "Matsuguna" ta riga ta zama abin farin jini a tsakanin 'yan kabilar Kazakstan. To, a cikin shirinmu na yau, za mu leka gidan wani iyalin 'yan kabilar Kazakstan domin ganin yadda suke yin zamansu kafin da kuma bayan da suka kafa muhalli.
Adelhan wani tsoho ne na kabilar Kazakstan. Yanzu shi da matarsa Zuran da kuma yaransu 4 suna zaune a kauyen Sakru na gundumar Fuhai da ke yankin Altai na jihar Xinjiang. Kuma su shida suna zaune cikin kwanciyar hankali a cikin wani dakin da fadinsa ya kai murabba'in mita 116. Amma wannan ya sha bamban sosai da zamansu na yau da shekaru da dama da suka gabata. Mr. Adelhan ya bayyana cewa,
"A wancan lokaci, mu kan shiga filin ciyayi na dutsen Altai a lokacin zafi, da kuma kaura zuwa dutsen Shawul a lokacin hunturu. Hanyar da ke tsakanin wadannan wurare biyu na da nisa sosai, dabbobi na da yawa, amma yara suna kanana, shi ya sa mun sha wahala sosai. Haka kuma zamanmu na wancan lokaci babu kyau sam, muna kwantawa a cikin dakin 'Huosi', ba mu da wutar lantarki sai dai filitun kananzir kawai."
'Huosi' wani irin tanti ne mai saukin kafawa na kabilar Kazakstan, wanda yana da kankanta, kuma ba ya iya kare sanyi sosai ba. Muddin lokacin hunturu ya zo, iyalin Adelhan za su sha wahala sosai. Mr. Adelhan ya gaya mana cewa,
"Lokacin hunturu na da sanyi kwarai. Kuma a ko wane karo da a gamu da hadarin kankara, dabbobi darurruwa da muke kiwatawa suna mutuwa. Har ma a wani karo na shekaru 80 na karnin da ya gabata, rabin dabbobin gidanmu sun mutu."
Domin gudun hadarin kankara, Adelhan da sauran makiyaya 30 sun fara gina dakunan kwana da itatuwa a kwarin kogi da ke tsakanin duwatsun Altai da Shawul. Ko da yake kwarewar wadannan dakunan kwana wajen fama da hadari ta samu kyautatuwa, amma zaman makiyaya bai samu kyautatuwa sosai ba. Kuma sakamakon karuwar yawan dabbobi, halin raguwar ciyayi ya kara tsananta, har ma dabbobi ba su iya samun abinci sosai.
A shekara ta 2005, gwamnatin gundumar Fuhai ta kaddamar da aikin kafa muhallin makiyaya bisa babban matsayi domin kyautata zamansu da kuma kara yawan kudaden da suke samu. Kuma a shekara ta 2006, gwamnatin ta kebe kudaden Sin Yuan miliyan 23 wajen kafa wani sabon kauye a wurin da ke da nisan kilomita 1 da dakunan kwana da Adelhan ya gina, inda aka shimfida hanyoyi, da samar da ruwa da wutar lantarki da wayar tarho da talibijin da kuma hanyar sadarwa ta zamani wato Internet, ban da wannan kuma an gina asibiti da kantuna da makarantu da wurin nishadi, har ma an samar da filin ciyayi da gonaki a kusan kauyen.
Bayan da aka kafa wannan kauye, lallashin makiyaya don zama a ciki ya kasance wata matsala. Jiger, wani ma'aikaci na hukumar kauyen ya bayyana cewa,
"makiyaya sun riga sun saba da zamansu na da, wato na zama a wurare daban daban, shi ya sa ba su son kafa gindin zamansu sosai. Sabo da haka, kauyenmu ya kira taro domin gaya musu alherin kafa muhalli, amma ba a mayar da martani ba. Ganin haka, ba yadda za a yi sai mu je gidaje daya bayan daya domin su kaura zuwa kauyen bisa son ransu."
Ganin halin da ake ciki a wancan lokaci, farin ciki da damuwa dukkansu sun cike a zuciyar Adelhan kamar yadda yawancin makiyaya 'yan kabilar Kazakstan suka yi. Matarsa Zuran ta gaya mana cewa,
"A wancan lokaci ba mu saba da kafa muhalli a wani wuri ba zato ba tsammani ba, kuma ba mu san ko dakunan kwana na bulo na da dumi ko a'a ba. Amma ma'aikatan hukumar kauye sun gaya mana cewa, an samar da ruwa da wutar lantarki a matsugunin, kuma an shimfida hanyoyi da gina makarantu, shi ya sa muka yi rajista tare da ra'ayin nuna shakku."
Bayan da suka shiga sabbin dakunan kwana, iyalin Adelhan sun gano cewa, abin da ke gabansu ya sha bamban sosai da wanda suke tsammani. Ba kawai sun samu ruwa da wutar lantarki ba, a'a har ma suna iya buga wayar tarho da kuma kallon talibijin. Gwamnatin wurin kuma ta ba su yawan kudaden taimako. Jia Lin, mataimakin shugaban gundumar Fuhai ya bayyana cewa,
"za a samar da kudin taimako Yuan dubu goma ga ko wane gidan makiyaya in ya gina wani dakin kwana, yayin da za a samar da kudin taimako Yuan dubu 10 gare su in su gina wani dakin kiwon dabbobi. Ban da wannan kuma bisa halin da ake ciki, kauyuka daban daban za su kara samar da kudin taimako dubu biyar, ta haka ko wane gidan makiyaya zai iya samun kudin taimako Yuan dubu 25."
Sabo da haka ba kawai iyalin Adelhan sun shiga babban dakin kwana ba, har ma sun gina wani dakin kiwon dabbobi da fadinsa ya kai murabba'in mita 80 domin kare dabbobin gida daga sanyi, ta hakan ba za su damu da hadarin kankara ba. Bugu da kari kuma sun samu filin ciyayi kadada shida da kuma gonaki kadada 4 domin dasa ciyayi.
Yanzu Adelhan ya shiga kwas din horaswa da kauyen ya shirya domin samun ilmin kiwon dabbobi da shuke-shuke bisa ilmin kimiyya. Ya bayyana cewa,
"bayan da na shiga kwas din horaswa, na samu ilmi kan kiwon dabbobi da shuke-shuke. Yanzu dabbobin da na kiwata su nagartattun shanu ne masu samar da nono da kuma tumaki, yawan ciyayi, yawan nono da gashin tumaki da aka samar sun samu karuwa a bayyane. Kuma yawan kudaden shiga da iyalinmu suke samu a ko wace shekara ya riga ya karu daga Yuan dubu da dama zuwa dubu 50."
Ba kawai kafa muhalli ya bai wa iyalin Adelhan yawan kudin shiga ba, a'a har ma ya samar musu da sauki a fannonin asibiti da makarantu da kuma wurin nishadi. Yanzu nisan mita fiye da dari daya ne kawai a tsakanin aisibiti na kauyen da gidan Adelhan, inda ake iya samun likita daya da kuma nus guda, wadanda dukkansu kwararru ne a fannin aikin likita, kuma ana iya samun magungunan yau da kullum da kuma kayayyakin jiyya a cikin asibitin. Yau da shekaru uku da suka gabata, iyalin Adelhan sun shiga tsarin jiyya na hadin gwiwa, shi ya sa a ko wane karon da suka je ganin likita, suna iya samun wasu kudaden da suka kashe wajen jiyya.
Ganin halin da iyalin Adelhan suke ciki wajen kafa muhalli, mutane da yawa sun fara kaura zuwa kauyen don samun gindin zama. A shekarar ta 2007, yawan gidajen makiyayan da suka kaura zuwa kauyen Sakru bisa son rai bai wuce 30 ba, amma a shekara ta 2008, wannan jimilla ta riga ta kai 60. Ya zuwa yanzu a duk yankin Altai, yawan gidajen makiyaya da suka kafa muhalli ya riga ya zarce dubu 8, wanda ya kai kashi 30 cikin kashi dari na dukkan yawan 'yan kabilar na yankin.
A 'yan kwanakin da suka gabata, yankin Altai ya tsai da kudurin mayar da aikin kafa muhallin makiyaya a matsayi daya daga cikin muhimman ayyuka uku na sa kaimi ga bunkasuwar tattalin arziki da zaman al'umma. Kuma a shekaru da dama na nan gaba, yankin zai kara yawan kudaden da za a kebe a wannan fanni. Ren Zhenping, shugaban hukumar kula da kiwon dabbobi ta yankin ya bayyana cewa,
"aikin kafa muhallin makiyaya wani babban aiki ne wajen kyautata hanyar samar da muhallin halittu da kuma kara yawan kudaden da makiyaya za su samu, shi ya sa za mu gudanar da aikin cikin himma da kwazo."
|