------ Masu saurare, bisa binciken da wasu kwararru daga sashen koyon ilimin aikin gona da kiwon dabbobi na jami'ar Tibet suka gudanar, ana kyautata zaton cewar, yankin kudu maso gabashin jihar Tibet mai ikon tafiyar da harkokin kanta, zai kasance daya daga cikin kyawawan wuraren halitta a kudu maso yammacin kasar Sin wadanda ke jawo hankulan mutane masu yawon bude ido.
Yankin kudu maso gabashin Tibet yana kunshe da yankunan mulki guda biyu, wato Linzhi da Changdu. Fadin kungurmin daji dake shimfidu a Linzhi yana kan gaba a kasar Sin, yankin Changdu kuma yana daya daga cikin manyan yankunan yawon shakatawa na Shangri-La.
A waje daya kuma, kaddamar da hanyar dogo da ta hada lardin Qinghai da jihar Tibet ya sanya kuzari ga bunkasuwar sha'anin yawon shakatawa na Tibet, haka kuma, sha'anin yawon shakatawa na Tibet ya riga ya kasance wani muhimmin jigo a jihar.
Kwararrun sun bada shawarwari cewar, ya kamata a kiyaye da raya albarkatun yawon shakatawa na yankin kudu maso gabashin jihar Tibet, har ya zama daya daga cikin kyawawan wuraren halitta a kudu maso yammacin kasar Sin wadanda ke jawo hankulan mutane masu yawon bude ido.
|