Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-01-22 16:41:18    
Gasar wasan kwallon tebur mai ban sha'awa da aka yi a kasar Sin

cri
Masu sauraro, barka da war haka! Ni ce Tasallah nake gabatar muku da wannan shiri game da wasannin motsa jiki. Ana sane da cewa, wasan kwallon tebur na kasancewa tamkar wasa ne na kasar Sin. Dalilan da suka sa haka su ne domin da farko 'yan wasan kwallon tebur na kasar Sin sun fi nuna hazakansu bisa 'yan wasa na sauran sassan duniya, kuma sun sami nasarori da yawa a cikin gasannin duniya. Dalili na biyu shi ne domin wasan kwallon tebur na samun amincewa sosai a kasar Sin. Mutanen Sin suna sha'awar irin wannan wasa sosai da sosai.

Tun daga ran 9 zuwa ran 11 ga wata na shekara da muke ciki, a birnin Changsha da ke kudancin kasar Sin, an yi gasar wasan kwallon tebur mai ban sha'awa, inda nagartattun 'yan wasa 16 na sassan daban daban na duniya da kuma dubban masu kishin wasan kwallon tebur suka shirya wani kasaitaccen bikin wasan kwallon tebur mai ban sha'awa kuma mai ban dariya tare da faranta zukatun mutane sosai.

Yin musaya a tsakanin zakarun duniya a wasan kwallon tebur da masu kishin wasan kwallon tebur da zuciya daya shi ne abun da ya fi jawo hankali a gun wannan gasar wasan kwalllon tebur.

Dai Zhixian, mai shekaru 90 da haihuwa, wani mazauni birnin Changsha, ya yi shekaru 70 yana yin wasan kwallon tebur. Ya zuwa yanzu dai ya kan yi wasa da wannan farin kwallo kullum. A lokacin da ake tambayar shi da cewa, yau wane dan wasan kwallon tebur kuma tauraron duniya ne yake son ya yi karawa da shi? Cikin ban dariya wannan tsoho ya amsa cewa, yana son ya kara da 'yan wasa mata masu kyan gani! Ta haka, ya cimma burinsa na karawa da 'yan wasa mata masu kyan gani, wadanda kuma yawansu ya kai 4. 'Yar wasa Li Jiawei da Feng Tianwei na kasar Singapore da Elizabeta Samara ta kasar Romania da Ruta Paskauskiene ta kasar Lithuania su ne 'yan mata 4 masu kyan gani da suka kara da Mr. Dai a lokaci guda. Wannan ya sa shi zumudi sosai. Ya ce,"Ina farin ciki sosai. Ban nuna gwanintata sosai ba tukuna. A ganina, yin wasa da kwallon tebur na amfanawa wajen kiwon lafiya tare da samun nishadi. Haka kuma, wasan kwallon tebur ya iya kawo more ido ga mutane. A takaice dai, wasan kwallon tebur na da kyau kwarai."

Ban da wannan kuma, gasar wasan kwallon tebur da aka yi a wannan shekara ya iya faranta zukatun mutane sosai. Jin Mengyan, mai shekaru 4 da haihuwa kawai, tsayinta ya fi na teburin wasa kadan, amma ta yi shekara guda ko fiye tana wasa da kwallon tebur. A wannan gami, wannan yarinya ta sami damar yin karawa da 'yar wasa Zhang Yining ta kasar Sin, wadda ita ce zakarar gasar wasannin Olympic. Bayan gasar, Zhang Yining ta sumbace ta. Wannan ya fi burge mutane a wannan rana.

A cikin gasar wasan kwallon tebur din, ba a shirya dukkan karawa a tsakanin wadanda suka nuna bambanci sosai a karfinsu ba. A zahiri, fintikau din da masu kishin wasan kwallon tebur suka yi, a wasan ya ba wadannan shahararrun 'yan wasa matsin lamba kadan. Li Xinyang, wani yaron Sin mai shekaru 14 da haihuwa ya yi karawa mai zafi da shehararren dan wasa Jorden Persson na kasar Sweden, wanda ya taba zama zakara na duniya. A karshe dai, Mr. Persson ya amsa sunansa na zakarar duniya, ya kada Li Xinyang, amma wannan yaron Sin ya ba shi matsala a cikin gasar, ta haka ya gane karfin masu kishin wasan kwallon tebur na kasar Sin. Bayan gasar, Mr. Persson ya gaya mana cikin dariya cewa,"Ya nuna karfi sosai. Amma ban damu kan ko zan kara da shi a nan gaba a cikin gasa ba. Shi yaro ne, amma na tsufa. Fasaharsa na da kyau, ya aza harsashi mai kyau. Ina farin ciki da yin wasa da shi."

Dalilin da ya sa Li Xinyang ya sami damar karawa da Mr. Persson a wannan karo shi ne domin ya shiga harkar zaben masu kishin wasan kwallon tebur masu karfi a birane da dama na kasar Sin. Masu shirya gasar wasan kwallon tebur sun gudanar da wannan harka ne domin karfafa gwiwar masu kishin wasan kwallon tebur da su shiga ciki da kuma inganta yin musaya a tsakanin 'yan wasa da kuma masu kishin wasan, inda dubban masu kishin wasan na kasar Sin suka shiga ciki. An fid da Li Xinyang daga zaben. Wannan yaro ya gaya mana cewa,"Na yi zumudi kwarai da gaske. Na yi karawa da shi da zummar yin koyi da shi. Tabbas ne Mr. Persson bai nuna karfi sosai ba, ta haka na iya karawa da shi a cikin karin lokaci. A zahiri, yau ina farin ciki sosai bisa maki da yawa da na samu a cikin gasar."

Gasar da ke tsakanin wani dan wasa da wata 'yar wasa da dukkansu zakaru ne na duniya, ta sanya halin annashuwa ya game ko ina a cikin gasar wasan kwallon tebur. Bayan da aka jefe kuri'a a kan internet a kwanan baya, masu amfani da internet sun zabi wadanda suke fi Alla-Alla wajen kallon karawa a tsakaninsu, wato dan wasa Timo Boll na kasar Jamus da kuma 'yar wasa Guo Yue ta kasar Sin. Ta haka wadannan 'yan wasa 2 da ke kan gaba a duk duniya sun kara da juna a ran 9 ga wata. A karshe dai, Boll ya kada Guo Yue.

Bayan gasar, Boll ya bayyana cewa,"Karawar da na yi da Guo Yue ya ba ni sha'awa. Ban taba karawa da wata 'yar wasa ba a da. A zahiri, yin karawa da wata zakarar duniya mace domin ganin karfinta yana da ban sha'awa. Na yi namijin kokarina a cikin gasar. E, haka ne, a ganina na yi fintikau a yau."

An fara shirya gasar wasan kwallon tebur a shekarar 2004. Yanzu gasar ta zama wani kasaitaccen biki ne da a kan shirya shi a ko wace shekara. Gidan telibijin na lardin Hunan ya shirya gasar ne tare da samun goyon baya daga hadaddiyar kungiyar wasan kwallon tebur ta duniya da kuma hadaddiyar kungiyar wasan kwallon tebur ta kasar Sin, kuma bisa ka'idar jin dadin jama'a da nuna godiya ga masu kishin wasan kwallon tebur. Haka kuma, ya bi hanyar samar da nishadi. A cikin gasar, an kusantar da 'yan wasa da masu kishin wasan, ta haka, gasar ta sami amincewa daga masu kishin wasan na kasar Sin. Sa'an nan kuma, ta cikin telibijin, 'yan kallo masu tarin yawa su kan kalli gasar. A wurin da ake shirya gasar, Cui Qiang, wani mazauni Changsha, wanda ke kishin wasan kwallon tebur ya yi mana bayanin cewa,"Ina sha'awar gasar wasan kwallon tebur. Na fi son kallon wadannan gasanni masu ban sha'awa. A ganina, wadannan harkoki sun iya jawo hankulan masu kishin wasan kwallon tebur ainun."

Kazalika kuma, shahararrun 'yan wasan kwallon tebur su ma sun nuna sha'awarsu kan wannan hawa. Dan wasa Ma Lin na kasar Sin da ya zama zakara a shirin tsakanin namiji da namiji a cikin gasar wasannin Olympic ta Beijing ya bayyana cewa,"Gasar wasan kwallon tebur ta kara sa kaimi kan bunkasuwar wasan kwallon tebur. Saboda ta kara kusantar da 'yan wasa da kuma masu kishin wasan, ta kuma kara kusantar da wasan kwallon tebur da jama'a. Wannan yana amfanawa wajen yayata wasan kwallon tebur."

Dadin dadawa kuma, dan wasa Persson na kasar Sweden ya nuna mana cewa,"Gasar wasan kwallon tebur na da matukar kyau. Wannan shi ne wani gwaji ne da aka yi domin raya wasan kwallon tebur ta hanyar kasuwanci. Ya iya nuna wa mutane na duk duniya ban sha'awar da wasan kwallon tebur ke da ita. Masu shiga wannan wasa na iya jin dadi a jiki da kuma tunani duka. Shi ya sa gasar yana da kyau ainun."

Tare da shirya gasar wasan kwallon tebur, a kan yi gasar zama zakara ta wasan kwallon tebur ta duniya, inda 'yan wasan da suka zama zakaru a cikin muhimman gasannin duniya a shekarun baya da kuma wasu 'yan wasan da ke kan gaba a duk duniya suka kara da juna. A kan bai wa wanda ya zama zakara a karshe kyautar kudi da yawansa ya kai dalar Amurka dubu 250, don haka, wannan gasa tana matsayin jerin gasanni na matsayin koli na duniya, wadda kuma ta ba da kyautar kudi mafi yawa a cikin wadannan gasanni. Gasanni masu zafi da ke tsakanin wadannan nagartattun 'yan wasa na sassan daban daban na duniya sun sanya wa masu kishin wasan suka ji dadi sosai da sosai.(Tasallah)