Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-01-22 16:22:16    
Isra'ila ta janye sojojinta duka daga zirin Gaza

cri

A ran 21 ga wata, kakakin sojan Isra'ila ya sanar da cewa, a ran nan, an janye sojojin kasar duka daga zirin Gaza. Wato ke nan an kwantar da kurar yake-yaken da aka shafe tsawon kwanaki 22 ana yi a zirin Gaza.

Dalilan da suka sa Isra'ila ta janye sojojinta su ne, na farko, bayan da aka tsagaita bude wuta, yawan rokokin da Hamas ta ke harba ya ragu a zahiri, wanda ya biya bukatun Isra'ila na janye sojojinta. A waje daya kuma, wannan sakon gaisuwa ne ga sabon shugaban Amurka, Barack Obama, wanda ya yi rantsuwar kama aiki a ran 20 ga wata. Ban da wannan, ba da jimawa ba, za a gudanar da babban zabe a Isra'ila, tare kuma da yin la'akari da fannin diplomasiyya, shi ya sa Isra'ila ta janye sojojinta a wannan lokaci. An ce, gaba daya hare-haren sojojin Isra'ila sun yi sanadiyyar mutuwar Palasdinawa 1414, tare kuma da jikkata wasu 5500. A nata bangare kuma, akwai sojojin Isra'ila 10 da wasu fararen hula 3 da suka mutu.

A halin yanzu, sojojin Isra'ila sun koma gefen Isra'ila da ke kan iyakar zirin Gaza, kuma a shirye suke su tinkari duk wani al'amari. A Gaza kuma, 'yan sandan Hamas sun fara fitowa kan tituna, don kiyaye doka, kuma an fara gyara hanyoyin samar da wutar lantarki da hanyoyin samar da ruwa. Bisa kwarya-kwaryar binciken da manazarta suka yi, an ce, matakan soja da sojojin Isra'ila suka dauka a zirin Gaza sun lalata gidajen jama'a 4100 da masana'antu 1500 da masallatai 20 da dai sauransu, kuma yawan asarorin da aka yi kai tsaye ya kai dalar Amurka biliyan 2.

A ran 20 ga wata, babban sakataren MDD, Ban Ki-moon ya kai ziyara zuwa zirin Gaza, kuma a gun taron manema labarai da aka yi a hedkwatar sassan MDD da ke zirin Gaza, ya ce, 'yan wasu asarori ne kawai ya gani, amma duk da haka, sun bakanta masa rai sosai. Sa'an nan, a cewar wani injiniya da ke zaune a zirin Gaza, barnar da hare-haren sojojin Isra'ila suka yi ya fi irin na girgizar kasa har sau 10. Bi da bi ne wasu mazaunan zirin Gaza suka koma gida, amma yanzu kufayi ne kawai ya rage a gare su.

Farfado da zirin Gaza aiki ne na gaggawa yanzu, amma aikin na bukatar wani yanayi na kwanciyar hankali. Ga shi mako guda ne kawai Hamas ta alkawarta don tsagaita wuta, kuma a cewar Isra'ila, idan ta sake samun hare-haren rokoki, lalle, za ta dauki matakan soja nan da nan. To, tambaya ita ce, ko yanayin kwanciyar hankali maras inganci da aka samar a zirin Gaza zai iya dorewa? Masharhanta suna ganin cewa, yanzu Isra'ila da Hamas sun dakatar da rikicinsu a fannin soja, kuma sun fara ja-in-ja ta fannin siyasa. A sa'i daya, rikicin ya sa gamayyar kasa da kasa suka kara fahimtar muhimmancin shimfida zaman lafiya a tsakanin Palasdinu da Isra'ila. Sabo da haka, ana iya samun kwanciyar hankali a zirin Gaza cikin wani guntun lokaci.

Ban da kwanciyar hankali, makudan kudade shi ma abu ne da ake bukata wajen farfado da zirin Gaza. Kasashen Larabawa da yawa sun sanar da ba da kyautar kudi don farfado da zirin Gaza. Amma duk da haka, manazarta sun yi nuni da cewa, farfado da Gaza aiki ne ja wur, sabo da Isra'ila tana son farfado da zirin tare da rage karfin Hamas. Ban da wannan, yanzu kasashen Qatar da Saudiyya sun sanar da ba da taimakon kudi da yawansa ya kai sama da dala biliyan, amma sabo da yawancin taimakon duniya ana karbar su ne daga hannun hukumar al'ummar Palasdinu, sabo da haka, yaya hukumar za ta hada gwiwa da Hamas shi ma wata babbar tambaya ce.

A game da jama'ar zirin Gaza, abin da ya fi muhimmanci gare su shi ne dadadden zaman lafiya, wato zaman lafiya a tsakanin Palasdinu da Isra'ila mai dorewa. Bayan da Isra'ila ta janye sojojinta, bangarorin da abin ya shafa za su iya zaunawa su yi shawarwari. Amma a watan Faburairu mai zuwa, Isra'ila za ta gudanar da babban zabe, kuma a halin yanzu, jam'iyyar Likud, wadda ke daukar tsattsauran matsayi a kan shawarwarin Palasdinu da Isra'ila, tana samun rinjaye bisa binciken ra'ayin jama'a da aka yi, don haka, idan jam'iyyar ta ci zaben da za a yi, lalle, za a iya fuskantar sabuwar barazana a halin da ake ciki a tsakanin Palasdinu da Isra'ila.(Lubabatu)