Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-01-22 12:13:43    
Kasar Kenya ta fara fama da karancin abinci

cri

Tun karshen rabin shekarar bara, an samu matsalar karancin abinci a kasar Kenya wadda ta kara tsananta a kwana a tashi,har ma ta addabi zaman dubunan 'yan kasa.

A ranar tara ga wata Gwamnatin Kenya ta bayyana cewa matsalar karancin abinci ta kara tsananata a kwana a tashi, kimanin mutane miliyan goma daga dukkan mutanen kasa miliyan 35 suna fuskantar yunwa, daga cikinsu wadanda matsalar yunwa ta fi shafuwa su ne mutane masu kamu da kwayoyin cutar kanjamo da marayu da kuma matalautan mazaunan birane da sauran marasa karfi. Jami'an wurare na Kenya sun sha yin kashedi cewa matsalar karancin abinci ta fi tsananni a yankunan dake karkashin mulkinsu, kayayyakin taimakon da gwamnatin take samarwa a halin yanzu ko kusa ba su iya biyan bukatunsu ba.

Kan ummal aba'isin karancin abinci, jami'an gwamnati da kwararru masana da kuma manyan mutane sun fadi albakarcin bakinsu. A ganinsu muhimman dalilan sun hada da tashen hankula sakamakon zabe,fari,hauhawar farashin kayayyakin noma,da ayyukan ban ruwa sun shiga tsohon yayi, da kuma irin abincin da ake noma ya yi karanci.

Kwanan baya yayin da kakakin ma'aikatar noma ta kasr Kenya ya yi hira da dan jarida na kasar Sin ya bayyana cewa "canjin yanayi,da hauhawar farashin takin zamani da na kayayyakin noma da tashin hankalin da ya wakana a farkon shekarar bara sakamakon zabe su ne muhimman dalilan da suka haddasa karancin abinci."

Tashe tashen hankulan da suka faru sakamakon zaben shugaban kasa sun yi sanadiyyar mutuwar mutane sama da dubu, mutane dubu dari uku sun rasa gidajen zama. Wuraren da suka samu tashin hankali mai tsananni a ce su ne rumbunan abinci na kasar Kenya. Kakakin nan ya kuma ce a farkon shekarar bara manoma masu dimbin yawa sun tsere daga gidajensu saboda fargabar tashen tashen hankula, bayan wasu watanni sun komo gidajensu a kai a kai duk da haka sun gaza noma abincinsu cikin lokaci, shi ya sa fadin filayen da aka noma kayan abinci ya ragu kwarai da gaske.

Watan Afril da na Mayu na kowace shekara, damina ce a kasar Kenya,ta fi muhimmanci ga amfanin gona. Ammam a wannan lokaci na shekarar bara, an samu fari mai tsanani a wurare da dama na kasar Kenya, shuke shuke a filaye masu fadi sun yi yaushi, manoma da yawa da tashe tashen hankula ba su shafe su ba su ma sun shiga halin kaka-nika-yi sabo da amfanin gona kalilan ko babu da suka samu.

Wasu kwararu masana na kasar Kenya sun rubuta bayanai a cikin jaridu kwanan baya inda suka yi nuni da cewa nau'o'in amfanin gona ba su da yawa da ayyukan ban ruwa sun shiga tsohon yayi su ma muhimman dalilai ne da suka haddasa karancin abinci. Kasawa wajen kula da su da rashin shiri na dogon lokaci na gwamnati kan samun tabbacin abinci, su ma dalilai ne da suka sanya Kenya cikin karancin abinci.

A gun taron hukumar samar da tabbacin abincin da shugaban kasar Kenya Mbeji ya kira kuma ya shugabanta, gwamnatin Kenya ta dauki wasu matakai masu muhimmanci domin tinkarar karancin abinci.

Wadannan matakan da aka dauka sun hada da a kafa wani kwamiti na ketare ma'aikatu wanda ya fara binciken hanyoyin tabbatar da matakan nan da nan cikin yanayin dokar ta-baci;da shiga da karin masara mai nauyin TON dubu 450 da kuma soke harajinsu na kwastam; da samar da taimakon abinci ga mutanen da suke fama da yunwa; a kebe kudin musamman na kimanin dalar Amurka miliyan shida da dubu dari hudu domin saye dabbobin gida na wuraren da fari ya rintsar da su,da kuma samar abincin dabbobi ga makiyaya na wuri,da shiga da karin takin zamani da za a baiwa manoma bisa farashi mai araha ko a fayu, da kuma samar da iri mai nauyi Ton dubu 25 ga manoma a fayu na wuraren da fari ya shafe su gaba daya ko na wasu kashi ne kawai.

A ganin manazarta, ga Kenya matsalar karancin abinci ta yi tsanani,ta gaza warware ta da kanta tana bukatar taimako daga kasashen duniya. Nan gaba kamata ya yi Kenya ta dora muhimmanci kan aikin gona da zuba karin kudi a wannan fanni,za ta iya warware matsalar abinci da kanta. Ali)