Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-01-21 09:18:31    
Kwararru sun ba da shawarwari domin daga matsayin wasan kwallon kafar matan kasar Sin

cri

A yayin gasar cin kofin duniya ta wasan kwallon kafa ta matan da ba su kai shekaru 20 da haihuwa ba ta shekarar 2008 da aka yi a kasar Chile, kungiyar 'yan wasan kwallon kafar matan kasar Sin ba ta sami sakamako mai kyau ba, kuma an lashe ta a yayin gasa tsakanin kungiyoyi. Bisa matsayinta na kungiyar kwallon kafar mata mai karfi a duniya, a cikin 'yan shekarun da suka wuce, kungiyar kasar Sin ba ta sami sakamako mai gamsarwa ba. Kan wannan batu, wasu kwararrun da abin ya shafa na kasa da kasa sun gabatar da shawarwari masu amfani gare ta, ana fatan matsayin kungiyar 'yan wasan kwallon kafar matan kasar Sin zai dinga dagawa a kwana a tashi. A cikin shirinmu na yau, bari mu yi muku bayani kan wannan.

A yayin gasar cin kofin duniya ta wasan kwallon kafa ta matan da ba su kai shekaru 20 da haihuwa ba ta shekarar 2008, kungiyar kasar Sin ba ta nuna karfinta yadda ya kamata ba, shi ya sa kwararru a harkar wasan kwallon kafa da 'yan kallo sun nuna rashin jin dadi gare su. Game da wannan, 'dan jaridan da ya zo daga wani gidan rediyo na kasar Chile Glaudio Lazo ya bayyana cewa,  "Na kimanta cewa, a kalla kungiyar kasar Sin za ta ci nasara a cikin gasar fidda gwani, kuma za ta shiga zagaye na biyu na gasar. Amma ba ta yi haka ba, wannan abin bakin ciki ne. A hakika dai, 'yan wasan kungiyar kasar Sin sun yi wasan kwallon kafa cikin sauri kuma sharadin jikunansu ya yi kyau kwarai, ban da wannan kuma, canjawar wuri tsakanin 'yan wasa shi ma yana da kyau. Koda yake ba su shiga zagaye na biyu na gasar ba, amma ana iya cewa, kungiyar kasar Sin ita ma kungiya ce mai kyau."

Sau da yawa Glaudio ya darajanta kungiyar wasan kwallon kafar matan kasar Sin. Dalilin da ya sa haka shi ne domin ya taba kallon gasa tsakaninta da kungiyar kasar Amurka wato a zagaye na karshe na gasa tsakanin kungiyoyi, a yayin wannan gasa, kungiyar kasar Sin ta lashe kungiyar kasar Amurka da 2 da nema, ana iya cewa, 'yan wasan kasar Sin sun nuna karfinsu sosai da sosai. Babban mai horaswa na kungiyar kasar Amurka wadda ta samu damar zama zakara a yayin wannan gasa Tony Dicicco ya bayyana cewa, a cikin gasar, 'yan wasan kungiyarsa sun koyi abubuwa da yawa daga wajen 'yan wasan kasar Sin. Ya ce,  "A yayin gasa tsakanin kungiyar kasar Amurka da ta kasar Sin, mun koyi abubuwa da yawa. 'Yan wasan kasar Sin sun yi wasa da hanzari kwarai, kuma fasahar wasansu ta yi kyau ainun. Kowace 'yar wasa ta yi kokari a yayin gasar. Kodayake kungiyar kasar Sin ta lashe kungiyarmu, amma gasar ta taimake mu saboda mun sami kyautatuwa musamman a fannin fasahar wasa. Kana kuma abu mafi takaici shi ne kungiyar kasar Sin ba ta shiga zagaye na biyu na gasar ba."

A karawa tsakanin kungiyoyi, da farko dai kungiyar kasar Sin da kungiyar kasar Agentina sun yi kunnen doki, daga baya kuma kungiyar kasar Faransa ta lashe kungiyar kasar Sin. A zagaye na karshe na gasa tsakanin kungiyoyi, koda yake kungiyar kasar Sin ta lashe kungiya mai karfi wato kungiyar Amurka, amma kungiyar kasar Sin ba ta samu damar shiga gasa ta mataki na biyu ba. To, ina dalilin da ya sa haka? Game da wannan, an dauka cewa, da farko dai, kungiyar kasar Sin tana cikin rukuni na biyu wanda ya hada da kungiyoyi hudu masu karfi. Ban da wannan kuma, shahararrun masu tsaron gaba biyu na kasar Sin wato Ma Xiaoxu da Ma Jun ba su shiga gasa ba saboda raunin da suka ji. A sanadiyar haka, karfin kungiyar kasar Sin ya ragu bisa babban mataki. Kazalika, kungiyar kasar Sin ba ta yi hayar malaman horaswa masu yin nazari kan fasahar wasa ta 'yan wasan sauran kasashen duniya ba, shi ya sa 'yan wasa na kasar Sin ba su gane fasahar abokan karawa ba, wato ba su yi aikin share fage sosai ba.

Duk da haka, a bayyane kungiyar wasan kwallon kafar matan kasar Sin ta koma baya, kodayake ta taba samun damar zama ta biyu a karo biyu a yayin gasar cin kofin duniya ta samarin duniya. To, ina dalilin da ya sa haka? Bari mu saurari abubuwan da kwararrun da abin ya shafa suka fada. "A ganina, 'yan wasan kwallon kafar matan kasar Sin ba su iya sarrafa sashin tsakiya na filin wasa sosai ba, wato 'yan wasan kasar Sin sun kasa karfin sarrafa kwallo a wurin." Wannan ra'ayi ne na babban mai horaswa na kungiyar kasar Japan. Kamar yadda kuka sani, a cikin shekaru 3 da suka shige, a kullum kungiyar Japan tana samun sakamako mai gamsarwa ko a cikin gasar cin kofin duniya ta mata samari ko a cikin gasar cin kofin duniya ta matan da suka kai shekaru 20 da haihuwa. Game da kungiyar kasar Sin kuwa, ana iya cewa, tsarin wasanta ba shi da kyau, wato kokarin 'yan wasa ya kan bi ruwa.

Tony Dicicco, babban mai horaswa na kungiyar Amurka wanda kullum ke nuna goyon baya ga tunanin 'kwallon kafa mai sa farin ciki' ya fi gane halin da kungiyar Sin ke ciki saboda ya taba yin takarar zama babban mai horaswa na kungiyar Sin a shekarar 2004. Ya dauka cewa, kamata ya yi kungiyar Sin ta gyara dabarar atisaye. Dicicco ya bayyana cewa,  "Ina tsammani 'yan wasan kungiyar Sin sun yi atisaye sosai, a kasar Sin, 'yan wasa da suka kai shekaru 30 da haihuwa ba su da yawa, amma a Amurka, suna da yawan gaske. Lokacin horaswa na 'yan wasan Sin ya yi tsawo sosai, ba ma kawai haka zai sa 'yan wasa su gaji ba, har ma zai sa su rasa sha'awa kan wasan. Idan sun rasa kauna ga kwallon kafa, to, ba za su ci nasara a gun gasa ba."

Kafin 'yan wasan kungiyar Sin su tashi zuwa Chile domin shiga gasa a wannan karo, sun riga sun yi atisaye na fiye da wata guda, a cikin wannan wata, sun yi hutu na kwanaki uku ne kawai. Amma 'yan wasan Amurka ba su yi atisaye tare kafin gasa ba saboda sun zo ne daga jami'o'i daban daban.

Glaudio Lazo ya riga ya yi aikin 'dan jarida mai kula da wasan kwallon kafa na kusan shekaru 14, a kullum yana mayar da hankali kan bunkasuwar wasan kwallon kafa ta Sin. Yana ganin cewa, kan wannan batu, kamata ya yi sinawa su yi hakuri. Ya ce,  "In kana son yalwata wasan kwallon kafa, abu mafi muhimmanci shi ne lokaci. Ban da wannan kuma, kudi shi ma yana da muhimmanci. Alal misali, a kashe kudin dauko hayar mai horaswa daga kasashen waje kuma a kashe kudin sayen kayayyakin atisaye nagari ko kuma a kashe kudin samar da filin wasa mai kyau. Amma a karshe dai, dole ne a dauki lokaci, saboda dole ne a bunkasa wasan kwallon kafa bisa matakai daban daban, wato daga yara da samari, domin ana bukatar samun isashen lokaci. Ba mai iyuwa ba ne a sami babban ci gaba cikin shekara daya ko biyu." (Jamila Zhou)