Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-01-20 18:30:55    
Gwamnatin kasar Sin ta bayar da takardar tsaron kasar domin bayyana shirin soja a cikin sabon lokacin da ake ciki

cri

A ran 20 ga wata, ofishin yada labaru na majalisar gudanarwa ta kasar Sin ya bayar da "Takardar tsaron kasa a shekara ta 2008", inda aka yi filla fillar bayanin ka'idoji da manufofin soja da kasar Sin ke dauka a cikin sabon lokacin da ake ciki domin tsaron kasar.

Wannan shi ne karo na 6 da kasar Sin ta bayar da takardar tsaron kai tun shekarar 1998. Wannan takarda wadda take dauke da bakaken Sinanci kimanin dubu 3 tare da babi 14 ta bayyana halin da ake ciki yanzu wajen tabbatar da kwanciyar hankali a duniya da manufofin tsaron kai na kasar Sin da halin da rundunonin sojan kasa da na ruwa da na sama da rundunar soja mai dauke da makamai masu linzami na kasar Sin suke ciki da kuma yadda ake raya masana'antun tsaron kai a kasar Sin da yawan kudaden soja da kasar Sin ke kashewa da dai makamantansu.

A cikin wannan takarda, an bayyana cewa, sabo da kasancewar rashin kwanciyar hankali da abubuwan da ba a iya tabbatar da su ba a ketare da kuma cikin gida, a cikin dogon lokaci mai zuwa, kasar Sin za ta ci gaba da fuskantar barazana da kalubale masu sarkakiya. Sabo da haka, kasar Sin ta tsara sabuwar ka'idar soja ta kare kai a cikin sabon lokacin da ake ciki bisa manyan tsare-tsare domin dacewa da sabon halin da ake ciki a duniya da tabbatar da kwanciyar hankali a gida.

A gun wani taron manema labaru da ofishin yada labaru na majalisar gudanarwa ta kasar Sin ya shirya a ran 20 ga wata, babban janar Hu Changming, kakakin ma'aikatar tsaron kai ta kasar Sin ya ce, "An jaddada cewa, kasar Sin za ta tsaya kan matsayin kariya da kariyar kai kuma za ta nuna kwarewa wajen daukar fansa yayin da aka taba ta bisa manyan tsare-tsaren soja. A waje daya kuma, za ta yi kokarin samun nasara a cikin yakin shiyya-shiyya da mai yiyuwa ne za a samu a lokacin da ake samun bayanai cikin sauki. Kuma za ta kara mai da hankali kan yin rigakafin aukuwar rikice-rikice da yake-yake da dai makamantansu. Sannan za ta kara karfin rundunonin sojanta wajen tinkarar barazana iri daban daban da sauke nauyin soja na salo iri iri da ke bisa wuyansu."

Bisa wannan ka'idar soja da kasar Sin ke dauka, wannan takarda ta nuna cewa, kasar Sin za ta kara yin kwaskwarima kan harkokin tsaron kai da rundunar soja, kuma za ta kara karfin yin yaki na rundunonin soja lokacin da ake samun bayanai cikin sauki. Sannan za a kara raya masana'antun tsaron kai da kuma kara yin nazari kan fasahohin samar da sabbin na'urorin soja.

Babban janar Hu Changming ya jaddada cewa, kasar Sin za ta cigaba da tsayawa tsayin daka kan matsayin bin manufar kariya kai da ka'idar soja da take bi ba tare da tangarda ba. Kuma tana ganin cewa, ya kamata a daidaita rikice-rikice da sabanin da suke kasancewa a tsakanin kasashe daban daban cikin lumana ta hanyoyin yin shawarwari.

Game da huldar soja da ke tsakanin kasashen Sin da Amurka, babban janar Hu Changming ya ce, raya huldar soja a tsakanin kasashen biyu yana dacewa da babbar moriyar bangarorin biyu, kuma ana bukatar bangarorin biyu su yi kokari tare.

"Idan za a iya girmama babbar moriya ta kowane bangare, za a iya tabbatar da tushen siyasa wajen raya huldar soja a tsakanin bangarorin biyu. A lokacin da huldar soja da ke tsakanin Sin da Amurka take cikin mawuyacin hali, mun nemi ma'aikatar tsaron Amurka da ta dauki hakikanan matakai domin kaucewa abubuwan da ke kawo illa ga kokarin raya huldar soja a tsakanin kasashen biyu, kuma ta kafa wani kyakkyawan sharadin raya huldar soja a tsakanin kasashen biyu kamar yadda ya kamata."

Sannan a cikin wannan takarda, an nuna cewa, karfin yunkurin kawo wa kasar Sin baraka, kamar su "karfin yunkurin neman mulkin Taiwan cikin 'yancin kai" da "karfin yunkurin neman mulkin Tibet cikin 'yancin kai" su ne suke kawo barazana ga halin da kasar Sin ke ciki wajen tabbatar da ikon mulkin kasar da cikakkun yankunan kasar, kuma suna da nasaba da babbar moriyar al'ummar Sinawa da ta kasar Sin. Sakamakon haka, a kan wannan batu, ba za a cimman tudun dafawa ko yin rangwame ko kadan ba.

Game da batun Taiwan, babban janar Hu Changming, kakakin ma'aikatar tsaron kai ta kasar Sin ya ce, kokarin dinkuwar duk kasar Sin gaba daya da kiyaye ikon mulkin kasar da kwanciyar hankali da cikakkun yankunan kasar, muhimmin nauyi ne da ke bisa wuyan rundunar sojan kasar Sin bisa tsarin mulkin kasar. Hu Changming ya ce, "Mun dauki matakin soja ne domin tabbatar da kwanciyar hankali a kasar da kiyaye babbar moriyar al'ummar Sinawa da kuma kiyaye babbar moriyar kasarmu. Za mu daidaita matakin soja da muke dauka bisa hakikanin halin da ake ciki a nan gaba." (Sanusi Chen)