Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-01-19 15:45:27    
Rikicin hada-hadar kudi ta kawo wa tattalin arzikin kasar Nijeriya barazana

cri
Cikin shirin yau za mu yi muku bayani kan barazanar da aka samu kan tattalin arzikin kasar Nijeriya, sakamakon rikicin hada-hadar kudi da ke addabar kasashen duniya.

Wakilin kamfanin dillancin labaru na Xinhua ya ruwaito mana labarin cewa, a wajen taron kwamitin zartaswa na tarayyar Nijeriya da aka yi shi a Abuja, hedikwatar kasar Nijeriya, bisa matsayinsa na taron karo na farko da aka yi cikin shekarar 2009, Umaru Musa Yar'adua, shugaban kasar Nijeriya, ya amince da cewa, yanzu an fara gano mugun tasirin da rikicin hada-hadar kudi ya kawo wa tattalin arzikin kasar. Shi ya sa ya bukaci gwamnatocin kananan hukumomin kasar da su dauki matakai don tinkarar barazanar rikicin hada-hadar kudi.

Shugaba Yar'adua ya ce, a wajen wasu abubuwa ne an fi samun ganin cewa rikicin hada-hadar kudi na haifar da barazana kan tattalin arzikin kasar Nijeriya, kamarsu kudin shiga da gwamnatin kasar ta samu na raguwa, kasuwar hannayen jari na samun tashi fadi, kuma farashin kudin Nijeriya wato Naira na dinga faduwa idan a kwatanta shi da dalar Amurka. Shugaba Yar'adua na ganin cewa, tattalin arzikin kasar Nijeriya na faduwa cikin wani mawuyacin hali, shi ya sa ya umarci gwamnatocin kananan hokumomi na kasar da su dauki matakai cikin sauri, don kauce wa tabarbarewar tattalin arzikin kasar.

Bayan taron, shugaba Yar'adua ya sanar da kafuwar wata kungiya ta musamman don yaki da rikicin hada-hadar kudi, inda kungiyar na karkashin jagorancin shugaban kasa, kuma tana kunshe da manyan jigogin kasar masu kula da aikin kudi da tattalin arziki, da shahararren masanan tattalin arzki, ta yadda za a fito da matakai don tinkarar rikicin, da kuma daidaita ayyukan sassa daban daban na gwamnatin kasar.

Gwamnatin kasar Nijeriya ta fi samun kudi a wajen sayar da danyen mai. Shi ya sa faduwar farashin danyen mai a kasuwannin kasa da kasa ta sa gwamnatin kasar Nijeriya ta shiga cikin mawuyacin hali na samun raguwar kudin shiga. Ban da wannan kuma, yawan kudin kasashen waje da kasar Nijeriya ta ajiye a gida ya ragu daga fiye da dalar Amurka biliyan 60 na watan Augusta na shekarar 2008 zuwa kimanin biliyan 52 na karshen shekarar 2008. A halin yanzu, farashin danyen mai shi ne kimanin dalar Amurka 40 bisa ko wace ganga, bai kai dala 45 yadda gwamnatin kasar Nijeriya ta yi hasashe cikin kasafin kudinta na shekarar 2009 ba. Shi ya sa halin da gwamnatin kasar Nijeriya ke ciki a wannan shekara wajen aikin kudi na da wuya.

Haka zalika, tun daga farkon shekarar 2008, kasuwar hannyen jari ta Nijeriya ta kasance cikin hali mai wuya, inda aka dinga samun faduwar hannayen jari, musamman ma cikin karshen rabin shekarar 2008. Zuwa karshen shekarar bara, muhimmin maki na kasuwar hannayen jari ta kasar ya fadi da kashi 40%.

Bisa alkaluman da baitul'malin kasar Nijeriya ya bayar, an ce, zuwa ran 15 ga watan Janairu na shekarar da muke ciki, darajar kudin Nijeriya wato Naira ta fadi zuwa Naira 150 bisa dalar Amurka 1, inda faduwar ta kai kashi 26%, idan a kwatanta da farashin da na farkon watan Disamba na shekarar 2008.

Manazarta na ganin cewa, kafuwar kungiyar musamman ta yaki da rikicin hada-hadar kudi na da nufin cewa, za a samu sauye-sauyen yanayi kan manufar aikin kudi da ta tattalin arziki ta kasar Nijeriya, bisa kara jin radadin rikicin hada-hadar kudi a jikin kasar, wannan ka iya taka rawa mai kyau ta yadda kasar Nijeriya za ta samu nasara cikin aikinta na yaki da rikicin hada-hadar kudi.(Bello Wang)