Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-01-16 17:23:56    
Tarihin Barack Obama

cri
Tambayar da za mu amsa a wannan mako ta fito ne daga hannun alhaji Nura Musa Zaria. A cikin wasikar da ya aiko mana, ya ce, don Allah, ina so a ba ni cikakken tarihin Barack Obama, zababben shugaban kasar Amurka. Sabo da haka, masu sauraro, yanzu sai a gyara zama a saurari amsarmu game da tarihin Barack Obama.

An haifi Barack Obama a ran 4 ga watan Agusta, shekarar 1961, a birnin Honolulu, jihar Hawaii, kasar Amurka. Mahaifinsa dan kasar Kenya ne, kuma mahaifiyarsa ta kasance wata farar fata da ke zaune a jihar Kansas ta kasar Amurka. Mahaifansa sun gamu da juna a lokacin da suke karatu a jami'ar Hawaii. A lokacin da yake da shekaru biyu da haihuwa, auren mahaifansa ya rabu. Sa'an nan, a lokacin da yake da shekaru shida da haihuwa, Mr.Obama ya kaura zuwa kasar Indonesia don zama tare da mahaifiyarsa da kuma mijinta.

Bayan shekaru hudu, Mr.Obama ya koma Hawaii. Bayan da ya gama karatun makarantar sakandare, sai ya fara karatu a jami'ar Occidental da ke jihar California, daga baya, ya yi karatu a jami'ar Columbia da ke New York, inda ya gama karatu a shekarar 1983. A shekarar 1985, Mr.Obama ya je Chicago, don gudanar da hidimomi a unguwannin birnin. A shekarar 1988, Obama ya ci gaba da karatu a makarantar koyon shari'a da ke jami'ar Harvard, inda ya sami digiri na uku a shekarar 1991. Daga baya, ya koma Chicago, inda ya kama aikin lauya tare da koyar da tsarin mulki a makarantar koyon shari'a da ke jami'ar Chicago.

A shekarar 1997, Mr.Obama ya fara shiga fagen siyasa, kuma ya ci zaben zama dan majalisar dattawa na jihar Illinois. Sai kuma a shekarar 2004, ya fara jawo hankulan jama'a sakamakon wani jawabin da ya yi a gun taron wakilan jam'iyyar Democrat. Sa'an nan, a watan Nuwamba, ya ci zaben zama dan majalisar dattawa ta Amurka daga jihar Illinois.

A lokacin da yake zama kan kujerar dan majalisar dattawa ta Amurka, Mr.Obama ya sa hannu cikin tsara daftarin kayyade makaman da aka amince a yi amfani da su, kuma ya sa kaimi ga jama'a da su kara sa ido kan yadda ake amfani da asusun tarayya. Ban da wannan, ya kuma nuna goyon baya ga jerin shirye-shiryen doka game da tafka magudi a wajen zabe da sauye-sauyen yanayi da ta'addanci irin na nukiliya da dai sauransu.

A watan Faburairu na shekarar 2007, a hukunce Mr. Obama ya sanar da shiga takarar zama shugaban Amurka. A yayin takarar, ya dora muhimmanci a kan batun kawo karshen yakin Iraki da dakatar da manufar rage karbar haraji da kuma yada inshorar kiwon lafiya. Ban da wannan, ya kuma yi alkawarin tabbatar da hadin kai a tsakanin jam'iyyu da kafa kawance da kasashen duniya da kuma maido da matsayin Amurka na jagora a duniya. A ran 27 ga watan Agusta na shekarar 2008, jam'iyyar Democrat ta gabatar da sunan Obama a matsayin dan takarar zaben zama shugaban Amurka daga jam'iyyar. Daga baya, a ran 4 ga watan Nuwamba, Mr.Obama ya ci zaben, wato ke nan ya zama dan asalin Afirka na farko da ya zama shugaban Amurka a tarihin kasar.

Mr.Obama zai kama aiki ne a ran 20 ga awtan Janairu na shekara mai zuwa.

Uwar gidan Obama ita ce Michelle Robinson, kuma suna da 'ya'ya biyu.(Lubabatu)