Birnin Yiwu yana gabashin lardin Zhejiang na kasar Sin. Bayan shekaru 20 da wani abu da suka wuce, birnin Yiwu yana ta samun bunkasuwa har ma ya zama sansanin fitar da kananan kayayyaki da ya fi girma a dukkan kasar Sin, kana kasuwar sayar da kananan kayayyaki da ta fi girma a duniya. A da, babu musulmi a birnin Yiwu, amma tun daga karshen karnin da ya wuce, bisa bunkasuwar kasuwar kananan kayayyaki, birnin Yiwu, wanda ke bude kofa ga kasashen waje ya jawo hankulan 'yan kasuwa musulmi da yawa daga gida da waje, saboda haka, ana iya ganin wadannan 'yan kasuwa masu shan aiki a ko ina, a cikin wannan muhalli kuma an giggina masallatai a Yiwu. To, masu sauraro, a cikin shirinmu na yau, za mu kawo muku wani bayani ne game da babban masallaci na Yiwu.
A lokacin da aka soma yin gyare-gyare da bude kofa ga kasashen waje, ba ma kawai babu masallatai a birnin Yiwu ba, har ma babu wurarren aiwatar da ayyukan addini da na cin abinci ga musulmi. Ma Chunzhen, limami na babban masallacin Yiwu ya waiwayo cewa, Musulunci wani sabon abu ne ga birnin Yiwu a shekaru 20 da suka wuce, hukumomin kula da harkokin addinai na wurin ba su san Musulunci sosai ba, saboda haka, bisa karuwar yawan 'yan kasuwa musulmi na gida da na waje a wurin, gwamnatin wurin na fatan gayyatar wasu kwararru don taimaka mu wajen kula da wannan birni. Ma Chunzhen ya gabatar da cewa,
"A farko, 'yan kasuwa daga kasar Pakistan sun fi yawa, su kan zauna a hotel na Hong Lou, amma ba su da wurin yin salla, daga baya kuma, sun yi aron wani karamin wuri don yin sallah. Kan wannan halin da ake ciki, gwamnatin wurin ta yi cudanya tare da majalisar musulunci, kuma sun shirya kafa wani babban masallaci don biyan bukatun musulmi daga kasashen Larabawa wajen zaman rayuwar addininsu."
Kafin shekarar 2000, yawan musulmin da suka zo birnin Yiwu daga sauran wurare sun kai 200 da wani abu. A lokacin kuma, an kafa wuraren yin sallah na wucin gadi guda biyu ne kawai. Amma, bayan 'yan shekarun da suka wuce, musulmi sun karu Yiwu, wadannan wuraren yin sallah na wucin gadi ba su iya biyan bukatunsu ba.
Khda Iburahim Al Minawy, 'dan shekaru fiye da 30 da ya fito daga Falestinu yana da wani kamfanin cinikin waje a birnin Yiwu, a lokacin da yake tabo tabun soma sana'arsa a shekarar 2001 a birnin Yiwu, Khda, wanda ke iya Sinnanci sosai ya ce, a farkon lokacin da yake zaune a birnin Yiwu, bai samu sauki wajen zaman rayuwa ba.
"Lallai na sha wahalhalu da yawa a lokacin da na iso birnin Yiwu ba da dadewa ba, babu dakunan cin abincin Larabawa, kuma babu wuraren yin sallah a wannan birni, saboda haka ba mu samu sauk wajen zaman rayuwa ba."
Bisa matsayinsa na wata tagar kasar Sin wajen aiwatar da manufar yin gyare-gyare da bude kofa ga kasashen waje, a cikin yunkurin samun bunkasuwa mai tsawon shekaru kusan 20, ba ma kawai birnin Yiwu ya nuna tunanin "Gyare-gyare" da "Bude kofa ga kasashen waje" a fannonin tattalin arziki da ciniki, da kuma tabbatar da samun saurin bunkasuwa ba, har ma ya yi kokari don shigar da irin wannan tunani a fannin al'adu, ta yadda musulmi na kasar Sin da na waje, kuma al'adu na kasar Sin da na waje suna iya kasancewa kamar yadda ya kamata a wannan birni, gaskiya ne ana iya ganin cewa, birnin Yiwu birni ne na kasar Sin, kuma birni ne na musulmi, har ma birni ne na dukkan duniya.
Bisa kokarin da bangarori daban daban suka yi tare, a shekarar 2004, gwamnati, da jama'ar birnin Yiwu sun zuba jari tare don kafa wani wurin gudanar da ayyukan musulunci na farko da gwamnati ta amince da shi a wannan birni, wato babban masallacin Yiwu. Fadin masallacin ya kai muraba'in kilomita kusan dubu 13. Ya zuwa watan Afril na shekarar 2007, mutane kamar 7000 suna yin sallah a babban masallacin Yiwu a ko wace ranar Jumma'a, ciki kuma musulmi na kasashen ketare sun kai kashi 60 cikin dari.
Limami Ma Chunzhen ya gabatar da cewa, yanzu da akwai masallaci daya da wuraren yin sallah na wucin gadi 10 a birnin Yiwu. Ya kara da cewa, ya ga yunkurin kafa masallacin Yiwu da kuma bunkasuwarsa, lallai yana da ma'ana sosai ga dukkan musulmin da ke zaune a wurin.
"Musulmin kasashen ketare sun nuna yabo sosai ga wannan masallaci, a ganinsu gwamnatin birnin Yiwu na nuna karbuwa sosai ga halin zaman rayuwar addini na musulmi daga kasashen ketare, saboda haka, suna iya yin ayyukan addininsu cikin 'yanci kuma ba tare da wata kayyade ba. Lallai, dukkansu suna jin farin ciki sosai."
Zarjan Khan Zada, mai cinikin tuffafi daga kasar Afghanistan ya zo nan kasar Sin a shekarar 2003. A shekaru 5 da suka wuce, ya kan yi yawo a tsakanin birnin Yiwu da kasar Afghanistan. Yana ganin cewa, gwamnatin birnin Yiwu ta kafa masallacin Yiwu bisa ra'ayin bude kofa ga kasashen waje, domin biyan bukatun musulmi na gida da na waje kan zaman rayuwar addinsu na yau da kullum, sakamakon haka, suna iya kwantar da hankulansu don kafa gidajensu a birnin Yiwu, da kuma bayar da taimakonsu kan bunkasuwar birnin. Zarjan ya ce,
"Wannan masallaci yana da kyau sosai. A zama na wani musulmi ina yin farin ciki sosai saboda gwamnatin kasar Sin ta kafa wannan wurin addini mai kyau gare mu. 'Yan kasuwa daga kasashe daban daban da ke zaune a birnin Yiwu suna iya yin sallah a masallacin, lallai mun yi godiya ga gwamnatin kasar Sin. Ba ma kawai wannan ne abu mai kyau ga 'yan kasuwar kasar Afghanistan ba, har ma wannan ne abu mai ma'ana sosai ga 'yan kasuwa musulmi daga kasashen ketare."
|