A cikin shekarun nan, an shaida ci gaban fasahohi da dama a gundumar Songzhuang da ke gabashin birnin Beijing da kananan kauyuka da ke makwabtaka da ita, kuma wadannan wurare sun zama unguwannin fasaha na zamani da suka shahara a gida da waje, haka kuma ana yin bikin al'adu na gundumar Songzhuang a wannan wuri shekara bayan shekara.Yanzu, a nan ne, ake gudanar da bikin al'adu a karo na hudu na Songzhuang, manazarta da masana fasahohi da hukumomin fasaha da masu sha'awar fasahohi na gida da na waje da dama da jama'ar Beijing sun hallara a wannan wuri, domin ganewa idanunsu yadda wannan biki yake.
Shekarun nan da muke ciki, fasahar zamani ta Beijing ta habaka sosai, masu fasahar zane-zane da suke da mafarki na inganta ayyukansu, sun yi tururuwa zuwa birnin Beijing, a sakamakon zaman rayuwar jama'ar da ke gundumar Songzhuang da ke nesa da cibiyar Beijing ba ya da tsada, sai masu sana'ar zane-zane suka zauna a wannan wuri. A shekarar 2005, an yi bikin al'adu a karo na farko na gundumar Songzhuang a nan, kuma masana fasahohi sama da 300 sun yi zaman rayuwarsu a gundumar Songzhuang, kuma sun nuna zane-zanensu a kan titi a fili, kuma sun jawo hankulan mutane sosai. Daga bisani kuma, yawan jama'a da suke zaune a gundumar Songzhuang na kara karuwa. Ma'aikaciyar kwamitin shirya bikin fasaha na gundumar Songzhuang Zheng Na ta bayyana cewa,
"A gundumar Songzhuang, akwai masanan ayyukan fasahohi fiye da 3000, balle ma sauran unguwannin da ke kewaye da ita, a shekarar 2006, gundumar Songzhuang ta kasance wani yankin al'adu a nan birnin Beijing. Haka kuma bikin al'adu na gundumar Songzhuang da ke kasar Sin ya habaka sosai har ya zama wata alama ta bikin fasahohi na zamani."
Zheng Na ta gabatar da cewa, babban taken bikin al'adu da aka yi na wannan karo shi ne "bunkasuwar gundumar SongZhuang". Ta bayyana cewa,
"Dalilai guda uku ne suka haddasa wannan kuma su ne, na farko, wannan ya dangane ga wannan yanki. Na biyu kuwa shi, ya dangane ga raya sana'ar al'adu da gwamnatin Sin ta gabatar cikin shekarun nan. Na uku kuma yana da alaka da bunkasuwar tattalin arziki na wurin, alal misali, idan wani wuri yana son habaka har ya zama tamkar yankin musamman wajen tattalin arziki, to, dole ne ya sami babban take ta fannin yin furofaganda shi."
Bikin ala'du a karo na hudu na gundumar SongZhuang ya samar da wani dandali ga masana ayyukan fasahohi na Sin da masu sha'awar kirkiro da sabbin fasahohi don su kara yin kokari wajen tuntubawar juna, 'yan kallo da masu sana'ar fasahohi suna da kuzari wajen shiga cikin wadannan bukukuwa, kuma bikin baje-koli kan abubuwan da masana ayyukan fasahohi na gundumar Songzhuang suka yi, ya bayar da wani yanayi mai sassauci da bude kofa kuma mai cin gashi ga sauran masana ayyukan fasahohi. A gun bikin, an kafa hukumomin fasaha da dama a wurin da ke kewaye, su ma suna shirya bukukuwa da dama.
Dukkan wadannan bukukuwa, sun sanya gundumar Songzhuang tana cike da wani yanayi na ayyukan a watan Nuwanba.
Manema labaru sun halarci wani bikin nune-nunen da ke da suna "Tsallake dausayi", wannan biki ya tattara tunanin masanan ayyukan fasahohi 17 a gun bikin har su zama wani biki wajen zane-zane da sassaka, kuma wannan yanayi na musamman ya sa mutane sun shiga rudani. Wasu kekunan da aka sanya su a kan hanya, kuma sun lallace, sabo da an matsa su. Kowa da kowa na nazarin ma'anar wannan kayan fasaha, wani matashi da ya fito daga birnin Tian Jin, Wang Ming ya bayyana cewa,
"Ko wannan yana nufi an fi kara samun motoci masu yawa, halin gurbata yanayi ke kara tsananta, ya kamata a yi kira ga kowa da kowa da su dawo ainihin matsayin da suke ciki."
Mai tsara wannan kayan fasaha Wang Qiang ya gabatar da ma'anar da yake so bayyana, kuma ya bayyana cewa
"Ina so in bayyana karfin matsin lamba daga kimiyya da fasaha, sabo da an matsa wadannan kekuna, sai suka lallace, mene ne kimiyya da fasaha suka kawo? Yaya za mu bunkasa.
A cikin wani tanti mai muraba'in mita dubu 4 a kasuwar fasaha, 'yan fasahohi sama da 400 sun nuna abun fasahohinsu fiye da 2000 a nan, masu sha'awar fasahohi za su iya yin musanyar fasahohinsu tare da sauran mutane. Wasu masu zane-zane da suka shiga cikin wannan kasuwa, ba su yi suna ba, sabo da haka farashin kayayyakin fasahohinsu ba su yi tsada ba,. Madam Li Xianshu ta gaya wa manema labaru cewa:
"Kayayyakin fasahohinsu sun burge ni, sabo da ba za su yi la'akari da sayarwar da wadanan zane-zane ba, amma za su ci gaba da rayuwarsu"
Ma'aikata na bikin al'adu sun bayyana cewa, kasuwar fasaha ta Sin ta yaba wa tunanin "shimfida fasaha zuwa gidajen jama'a, don su kara sanin ayyukan fasahohi, kuma yayin da suka shiga cikin wannan aiki, jama'a za su ga fasahohin musamman, kuma wannan zai yi amfani da su wajen kirkiro da kyakkyawan yanayi wajen yalwata fasahohi, da kyautata kasuwar fasaha, don samun wani yanayin fasaha da ke da ma'anar musamman.
Yayin da aka shiga lokacin kawo karshen bikin al'adu a karo na hudu na gundumar Songzhuang na kasar Sin, gundumar Songzhuang da ke karkarar kasar Sin, ta kasance wata unguwar fasaha ta jama'a, kuma a karkashin yanayin ciyar da sana'ar raya al'adu na Sin, zai kasance wani wuri da ke da makoma da sana'ar fasaha ta gida da ta waje za su sa lura sosai.
|