Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-01-14 15:38:13    
Baligan da suke zama tare da yara sun fi yawan cin abinci mai mai

cri
Bisa wani rahoton nazari da kasar Amurka ta bayar a kwanan nan, an ce, baligan da suke zama tare da yara sun fi yawan cin abinci mai mai idan an kwatanta su da wadanda ba su yi zama tare da yara ba.

Manazarta na jami'ar Lowa da kuma kwalejin kiwon lafiya na jami'ar Michigan ta kasar Amurka sun gudanar da bincike ga baligai 6600 wadanda shekarunsu ya kai 17 zuwa 65 da haihuwa. Daga baya kuma sun gano cewa, baligan da suke zama tare da yara sun fi cin abinci mai mai da ya kai gram 4.9 a ko wace rana idan an kwatanta su da wadanda ba su yi zama tare da yara ba.

Kuma rahoton ya bayyana cewa, a da manazarta su kan mai da hankali kan tasirin da baligai suka bayar ga yara wajen cin abinci kawai, amma sun yi watsi da rawar da yara suke taka ga baligai wajen cin abinci.

Likita La Roche mai kula da wannan bincike ya bayyana cewa, dalilin da ya sa baligan da suke zama tare da yara su kan ci abinci mai mai masu yawa shi ne sabo da su kan samu matsin lamba daga zaman rayuwarsu, da kuma tasirin da tallace-tallace suke bayarwa wadanda ake yi don yara kawai. Ban da wannan kuma a kan kiyaye abincin da ake shiryawa don yara a gida, wadannan baligai su kan ci irin wannan abinci tare da yara.

Ban da wannan kuma likita La Roche ya ba da shawarar cewa, ya kamata baligan da ke zama tare da yara su yi iyakacin kokari wajen daina cin abinci mai mai. Haka kuma ya kamata su kara shan nono maras mai sosai, da kuma dafa abinci tare da man zaitun a maimakon man shanu ko na sauran dabbobi. Ban da wannan kuma bai kamata su ci abinci irin na fast food da pizza fiye da sau biyu a ko wane mako ba.

To, masu sauraro, yanzu sai ku shakata kadan, daga baya kuma za mu yi muku wani bayani daban kan samun kiba, wato mutanen da su kan ci kayayyakin kwalama da yawa sun fi saukin samun kiba fiye da kima.

Wani sabon bincike da kasar Amurka ta gudanar ya tabbatar da cewa, mutanen da su kan ci kayayyakin kwalama masu yawa sun fi saukin mun kiba fiye da kima, ta yadda za a iya kara hadarin kamuwa da cutar sukari.

A cikin wannan bincike da aka yi har shekaru 10 ga matasa fiye da 3000, Barry Austin, wani manazarci na jami'ar North Carolina ta kasar Amurka da abokan aikinsa sun gano cewa, bisa dakunan cin abinci na gargajiya, mutanen da su kan ci abincin a cikin dakunan sayar da kayayyakin kwalama sun fi saukin samun karuwar jimlar BMI, wanda wani ma'aunin nauyin jiki ne da a kan yi amfani da shi a duk duniya domin auna ko wani yana da jiki sosai, ko wani yana da kiba. Amma yaya aka iya samun wannan jimla? Alal misali, idan nauyin jikin wani mutum ya kai kilogram 80, kuma tsayinsa ya kai mita 1.85, to 80 a raba da 1.85 sau 1.85 shi ne 23.3 wato jimlarsa ta BMI. Idan wannan jimla ta kai 20 zuwa 25, wannan ya shaida cewa wannan mutum yana da koshin lafiya. Idan wannan jimla ta kai 25 zuwa 30, to wannan mutum ya samu kiba kadan, amma idan wannan jimla ta zarce 30, to wannan ya shaida cewa wannan mutum ya samu kiba fiye da kima.

Kididdigar da manazarta suka samu bayan shekaru 7 da suka gudanar da wannan bincike ta bayyana cewa, idan an ci kayan kwalama sau daya a ko wane mako, to jimlarsa ta BMI za ta karu da 0.13 a cikin wannan shekara, wannan ya yi daidai da karuwa da kilogram 0.42 ga wani mutumin da tsayinsa ya kai mita 1.78. Haka kuma kididdigar da suka samu bayan shekaru 10 da suka gudanar da binciken ta bayyana cewa, idan an ci kayan kwalama sau daya a ko wane mako, to jimlarsa ta BMI za ta karu da 0.24.