Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-01-13 16:57:37    
Abinci mai dadi a Yinchuan

cri
Yawancin mutanen da suka taba kai ziyara a birnin Yinchuan da ke arewa maso yammacin kasar Sin, su kan ci albarkacin bakinsu, su nuna babban yabo kan abinci mai dadi, har ma ba su manta da abincin ba, su kuma gabatar da abinci mai dadi na wannan birni ga saura. Birnin Yinchuan, babban birni ne na jihar kabilar Hui ta Ningxia mai cin gashin kanta ta kasar Sin. Abinci na wurin na nuna halin musamman na musulmai, haka kuma, ko abincin nama ko abincin garin alkama, ko cincin ko kuma shahararrun kayayyakin abinci dukkansu na da dandano mai danko, suna da matukar dadin ci.

In an tabo magana kan abinci mai dadi na Yinchuan, to, da farko za mu yi hira kan naman tunkiya a jihar Ningxia. Ana samun dimbin tumaki irin na musamman wato Tanyang a jihar Ningxia. A sakamakon muhallin musamman a wurin, naman tumakin Tanyang na da dadin ci ba tare da warin da naman tumaki kan fitar ba. A cikin shekaru 200 ko fiye da suka wuce, masu sha'awar abinci na dauloli daban daban na kasar Sin suna ta nuna babban yabo kan dandanon irin wannan naman tumaki. Yanzu kasashen Larabawa da ke yankin Gabas ta Tsakiya su kan shigo da wannan naman tumaki da yawa daga Ningxia.

A matsayinsa na babban birnin jihar kabilar Hui mai cin gashin kanta daya tilo a kasar Sin, naman tumaki da aka dafa ta hanyoyi daban daban ya fi jawo hankulan mutane a cikin dukkan abinci mai dadi a Yinchuan, inda dafaffun kayan cikin tumaki da aka dan yayyanka, wato Yang Za Sui a bakin Sinawa ya fi shahara. Mazauna Yinchuan da yawansu ya kai misalin kashi 20 cikin dari su kan ci irin wannan kayan abinci a matsayin karya kumallo a ko wace rana. Game da wannan kayan abinci mai dadi, Zhao Zinan, wata daliba mai shekaru 24 da haihuwa ta gaya mana cikin farin ciki cewar,

"A jihar Ningxia, ana dafa kayayyakin cikin tumaki da aka dan yayyanka a cikin jan miya tare da wasu yayyanka albasa a kai, wannan kayan abinci kan samar da kamshin naman tumaki irin na Ningxia, yana da yaji sosai, har ma ya kan sanya gumi da yawa, amma bayan da ka ci, kana son kara wani kwano na daban."

A kan yi amfani da sassa daban daban na jikin wata tunkiya, kamar kai da kofato da hanta da hanji da kuma jini da dai sauransu. Dukkan wadannan kayayyakin jikin tunkiya na da dadin ci sosai tare da kiyaye lafiyar mutane. Alal misali, hantar tunkiya na iya kyautata kwakwalwa da kuma idon mutane.

Kayan abinci mai suna Yang Za Sui ba ma kawai shi ne cincin din da ya fi shahara a duk fadin jihar Ningxia ba, har ma an taba zabe shi a matsayin shahararren abinci mai halin musamman na musulmai na kasar Sin. Xue Gang, shugaban hukumar aikin yawon shakatawa ta jihar Ningxia ya shahara ne a fannin rubuta rubutattun wakoki a arewa maso yammacin kasar Sin, yana sha'awar cin kayan abinci mai suna Yang Za Sui. Ya taba rubuta wata rubutacciyar waka kan wannan kayan abinci domin nuna kishin garinsa.

"Miyar kayan abinci na Yang Za Sui na da yaji, kayayyakin cikin tumaki na da dadi. Ga koren kayan lambu na caraway da albasa da ke miyar. A idon mazauna wurin, kayan abinci na Yang Za Sui na da dandano. A idon saura fa, ba za su iya mantawa ba."

In muna cewa, kayan abinci mai suna Yang Za Sui da ake iya gani a ko ina a Ningxia ya nisanci mutane sosai, kamar yadda sauran cincin mai halin musamman yake kasancewa, har ya zama wani kashi ne na zaman rayuwar mazauna Ningxia, to, soyayyen naman dan tunkiya ya yi suna ne a sauran wuraren kasar Sin bisa dandano mai danko, ya zama alamar Ningxia ta daban a fannin abinci.

Yanzu ga yayyankan naman dan tunkiya mai launin ja mai duhu, da bayananniyar taliyar da aka yi da sitati, kuma aka dafa ta hanyar da ko da an gutsura, ya ci gaba da kasancewa da karfi, da kayan lambu mai launin kore da kuma jar miya. Ko ka sansana kamshi? Soyayyen naman dan tunkiya ya yi kamar ya iya nuna halayen mazauna da ke zama a arewa maso yammacin kasar Sin, ya zama na farko a zukatan kusan dukkan mazauna Ningxia a fannin samarwa baki. Duan Guohai, mai shekaru 40 ko fiye da haihuwa ya sifanta mana dandano mai kyau na wannan kayan abinci. Ya ce,

"Mazauna Yinchuan da yawa suna son cin naman dan tunkiya mai dadi. Bayan da aka soya shi tare da yaji, ba shi da warin naman tunkiya ko kadan. Sa'an nan kuma, an kara taliyar da aka yi da sitaci. Dukkansu na da dadin ci kwarai. Mu kan samar wa baki, ko kuma cin irin wannan kayan abinci da kanmu a gidajen abinci a lokacin hutu."

Naman dan tunkiya mai inganci da aka samu a jihar Ningxia kawai da kuma hanyar dafawa da aka saba yi har tsawon shekaru fiye da dari daya sun sanya wannan kayan abinci na soyayyen naman dan tunkiya yana da kamshi irin na naman kaji, sa'an nan kuma, yana da laushi kamar yadda dafaffen naman zomo yake kasancewa.

Baya ga abinci iri daban daban da aka yi da naman tumaki, a birnin Yinchuan, a kan sami abinci iri daban daban da musulmai suka dafa da garin alkama, a ciki kuma, wani irin kayan abinci mai suna You Xiang da ake ci ta, fatarta tana garas-garas ya fi shahara.

Bisa wata almara, an ce, kayan abinci mai suna You Xiang shi ne Mahomet, wanda ya kafa addinin musulunci ya yayyata. An shigar da shi a kasar Sin yau da shekaru dari 7 ko fiye da suka wuce. A halin yanzu, ko a bukukuwa da salla, ko kuma lokacin da suka yi baki, ko kuma bikin aure da jana'izza, Sinawa musulmai ba su iya raba su da wannan kayan abinci ba. Zhao Jing, wadda ke zama a Yinchuan, ta bayyana cewa,

"A lokacin da muke ci, fatarta tana da garas-garas. Tana da laushi sosai a bakinmu. Ba za ta rube ba har tsawon rabin wata, haka kuma, laushinta da dadinta ba za su raunana ba."

Wannan budurwa ta kuma yi karin bayanin cewa, a zahiri, waina iri daban daban da gasasshiyar taliya sirirriya wato San Zi a bakin Sinawa da ke samu karbuwa sosai su ma suna matsayin wani kashi ne na kayan abinci na You Xiang. Ta kara da cewa,

"Kayan abinci mai suna You Xiang da ake samarwa a jihar Ningxia ya hada da waina da gasasshiyar taliya sirirriya wato San Zi a bakin Sinawa da kuma cincin mai suna Hua Hua. Hanyar samar da wannan cincin mai suna Hua Hua ita ce kullu kwallon garin alkama tare da sukari mai launin fari da na ja, ta haka wannan kwallon garin alkama ya iya hada da laukunan fari da baki. A sakamakon nannade shi, za a sami abincin garin alkama masu surorin malam-bude-littafi da furanni da sauran kananan dabbobi."

Gasasshiyar taliya sirirriya wato San Zi a Sinance ita ce abincin da musulmai na sassa daban daban na duniya suka saba ci. Wannan kayan abinci na San Zi da mazauna jihar Ningxia suke samarwa yana ta samun babban yabo a gida da kuma a waje saboda garas-garas da launinta na zinariya da kuma taliya sirirriya a cikin shekaru da dama da suka wuce. A shekarar 1985, a lokacin da mutanen kasashen Larabawa da suka kulla dangantakar zumunci a tsakaninsu da kasar Sin suke yin ziyara a jihar Ningxia, sun yaba wa gasasshiyar taliya sirirriya wato San Zi a bakin Sinawa da musulamai mazauna jihar Ningxia suka samar musu saboda garas-garas da kuma tsantsar dandano. Yanzu a jihar Ningxia har ma a duk fadin kasar Sin, gasasshiyar taliya sirirriya wato San Zi a Sinance tana matsayin abinci mai tsarki da 'yan kabilar Hui ba su rasa ba a lokacin da suke murnar bukukuwa.