Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-01-13 15:40:06    
Saurin bunkasuwar kimiyya da fasaha ya canja zaman Sinawa

cri
A cikin shekaru 30 da suka gabata bayan da kasar Sin ta aiwatar da manufar bude kofa ga kasashen waje da kuma yin kwaskwarima a gida, kasar Sin ta samu babban ci gaba a fannin kimiyya da fasaha, kuma abubuwan da ke da nasaba da kimiyya da fasaha sun riga sun shiga rayuwar jama'a a fannonin abinci da tufafi da zirga-zirga da kuma na'urorin zamani da ake amfani da su.

Da farko a fannin abinci, sanin kowa, kasar Sin ta ciyar da mutanen da yawansu ya kai kashi 1 cikin kashi 5 na duniya bisa gonakin da fadinsu ya kai kashi 7 cikin kashi dari na duniya. Amma ba a iya raba wannan al'ajabi tare da fasahohin horar da kyawawan ire-ire da dabarun zamani na yin noma ba. In an mayar da shinkafa mai aure da Yuan Longping, sanannen kwararre na kasar Sin a fannin ayyukan noma ya kaga a matsayin misali, to za a iya gano cewa, a cikin shekaru 30 da suka gabata, wannan fasaha ta samu yaduwa a gonakin da fadinsu ya kai a kalla kadada miliyan 15 a Sin, kuma matsakaicin yawan shinfaka da aka samu daga ko wace kadada guda ya karu da kilogram 4500 bisa na lokacin da, wanda ya kafa tushe mai inganci ga aikin samun isasshen abinci na Sin. Yanzu Mr. Yuan da shekarunsa ya kai 70 da wani abu yana yin nazari domin cimma wani sabon buri. Kuma ya ce,

"Makasudinmu na gonakin gwaji a karo na uku shi ne samar da shinkafa koligram 900 a ko wace gona da fadinta ya kai murabba'in mita 666, kuma na yi imani sosai wajen cimma wannan buri a shekara ta 2010."

A fannin zirga-zirga kuma, kayayyakin zirga-zirga na jama'a sun samu kyautatuwa sosai sakamakon saurin bunkasuwar tattalin arziki da kyautatuwar matsayin fasahohin ayyuka. Yanzu wani sabon kayan sufuri ya shiga zaman fararen hula na kasar Sin, wato motocin bus-bus da ke amfani da wutar lantarki. Madam Su Xiumin, wata fasinja ta birnin Beijing ta gaya wa wakilimu cewa, ta fi nuna sha'awa ga irin wannan motar bus in an kwatanta da motocin gargajiya masu amfani da man dizal. Kuma ta ce,

"A fannin jigilar mutane, babu bambanci a tsakanin motocin bus-bus masu amfani da wutar lantarki da masu amfani da man dizal. Amma abubuwan gurbata muhalli da irin wannan mota mai amfani da wutar lantarki ke fitarwa kadan ne. In za a iya kara yawan motoci masu amfanin da wutar lantarki yayin da a rage yawan motoci masu amfani da man dizal a nan gaba, to ingancin iska na Beijing zai samu kyautatuwa sosai. "

A fannin na'urorin zamani da ake amfani da su kuma, ko shakka babu zaman Sinawa ya riga ya shiga zamani sakamakon bunkasuwar kimiyya da fasaha. Haka kuma yaduwar fasahohin Internet ta kara ba da tasiri sosai ga bunkasuwar tattalin arziki da zamantakewar al'ummar Sin. Bisa kididdigar da aka bayar, an ce, ya zuwa yanzu, yawan masu amfani da Internet na kasar Sin ya zarce miliyan 250, kuma Internet ya riga ya zama wata muhimmiyar kaya wajen samun labaru da shakatawa da cudanyar aiki. Ban da wannan kuma ana amfani da fasahohin Internet wajen kyautata ayyukan gwamnati na ba da hidima. Alal misali, ta amfani da kwamfuta da Internet, yara na kauyuka suna iya samun ilmin da sanannun malamai ke koyarwa. Li Xiang, wani dan makarantar gundumar Huizhai ta lardin Guangdong da ke kudancin kasar Sin ya gaya mana cewa, irin wannan hanyar koyarwa ta kara sha'awar da ke nunawa karatu. Kuma ya ce,

"Ya yi kamar kallon sinima, akwai zane-zane masu motsi, akwai murya, yana da ban sha'awa sosai."