Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-01-12 20:18:46    
Kasar Sin ta kaddamar da zirga-zirgar matafiya ta lokacin bukin bazara a wannan shekara

cri
Tare da karatowar bukin sallar bazara na kasar Sin, an kaddamar da zirga-zirgar fasinjoji ta lokacin bukin bazara a shekara ta 2009. A cikin tsawon kwanaki 40, wato daga ranar 11 ga watan Janairu zuwa ranar 19 ga watan Faburairu, an kimmanta cewa, adadin mutanen da za su yi zirga-zirga a duk fadin kasar Sin zai zarce biliyan 2.3. A halin yanzu, hukumomi daban-daban masu kula da zirga-zirgar hanyoyin dogo, da hanyoyin mota, gami da jiragen sama suna zage damtse wajen zirga-zirgar fasinjoji.

A lokacin zirga-zirgar fasinjojin ta lokacin bukin bazara, layin dogo ya fi samun cunkoson matafiya. Kamar yadda mai magana da yawun ma'aikatar kula da harkokin hanyar dogo ta kasar Sin Mista Wang Yongping ya ce, sakamakon kokarin da ake yi a 'yan shekarun nan, zuwa karshen shekara ta 2008, an kara samun yawan jiragen kasa domin sufurin jama'a, haka kuma karfin layin dogo na yin sufurin matafiya ya sami ingantuwa kwarai da gaske. A lokacin zirga-zirgar fasinjoji ta lokacin bikin bazara, hukumar sufurin jiragen kasa za ta kara yawan zirga-zirgar jiragen kasa ta wucin-gadi. Mista Wang ya ce:

"Yayin da ake sufurin fasinjoji ta lokacin bikin bazara, muna kara maida hankalinmu kan wasu muhimman wurare da tashohin jiragen kasa, da kara yawan zirga-zirgar jiragen kasa, ta yadda za'a biya bukatun matafiya."

Akasarin matafiya wadanda suke yin zirga-zirga a lokacin bikin bazara su ne ma'aikata 'yan ci rani da dalibai. Wang Yongping ya yi nuni da cewa, a shekarar da muke ciki, hukumar sufurin jiragen kasa za ta cigaba sayar da tikiti na zuwa da dawowa kai-tsaye ga dalibai, da kara kawo sauki ga ma'aikata 'yan ci rani wajen sayen tikitoci, inda Mista Wang ya ce:

"Hukumar sufurin jiragen kasa za ta kara yawan zirga-zirgar jiragen kasa na musamman domin dalibai zalla, da shirya jiragen kasa na musamman ga manoma 'yan ci rani domin kai musu gida ba tare da tsayawa akan hanya ba."

A waje daya kuma, zirga-zirgar matafiya ta hanyoyin mota da jiragen sama na cigaba yadda ya kamata. Bisa hasashen da aka yi, an ce, a shekarar bana, adadin fasinjojin da za su yi zirga-zirga ta hanyoyin mota zai kai biliyan 2, wanda ya karu da kashi 3 bisa dari idan aka kwatanta shi da na shekara ta 2008. A rana ta farko da aka kaddamar da zirga-zirgar fasinjoji ta lokacin bikin bazara, yawan fasinjojin da suka yi zirga-zirga ta hanyoyin mota ya karu kadan, kuma ba'a samu cunkoso ba a yawancin hanyoyin mota. Mai magana da yawun ma'aikatar sufuri da kula da harkokin jigilar kayayyaki ta kasar Sin Mista He Jianzhong ya ce:

"Dangane da hakikanin halin da ake ciki a wannan shekara, yayin da ake zirga-zirgar fasinjoji ta lokacin bikin bazara, za mu kara yawan zirga-zirgar motocin dake dauke da fasinjoji dubu 760 da jiragen ruwa sama da dubu 13."

A fannin sufurin jiragen sama kuma, yawan fasinjojin da suka yi zirga-zirga ta jiragen sama ya karu ainun a rana ta farko da aka kaddamar da zirga-zirgar fasinjoji ta lokacin bikin bazara, wanda ya zarce dubu 500. Yanzu manyan kamfanonin zirga-zirgar jiragen sama suna daukar mataki na kara yawan zirga-zirgar jiragen sama, domin biyan bukatun matafiya.(Murtala)