Kwanan baya, Shuaibu Muhammed Rijiyar maikabi, a karamar hukumar Kamba, jihar Kebbi, tarayyar Nijeriya ya aiko mana wata wasika, inda ya ce, "Don Allah, ku ba ni tarihin sabon shugaban kasar Zambia, wato Rupiah Banda." To, a cikin shirinmu na yau, za mu amsa tambayarsa.
Rupiah Banda, sabon shugaban kasar Zambia, an haife shi ne a ran 19 ga watan Faburairu na shekarar 1937.
Mr.Banda ya fara shiga fagen siyasa lokacin da ya shiga bangaren matasa na jam'iyyar UNIP a shekarar 1960. Daga shekarun 1960 zuwa na 1970, Mr. Banda ya rike mukamai da yawa ta fannin diplomasiyya, ciki har da zama wakilin kasar Zambia a MDD. Daga baya, shugaba Kenneth Kaunda, wanda ya kafa jamhuriyar Zambia, ya nada shi a matsayin ministan harkokin waje na kasar.
A shekarar 1978, an zabi Banda a matsayin mamba a majalisar dokoki kuma ya yi aiki a majalisar dokokin kasar har zuwa shekarar 1991.
A watan Oktoba na shekarar 2006, tsohon shugaban kasar Zambia, marigayi Mwanawasa ya zabe shi a matsayin mataimakinsa, don ya maye gurbin Lupando, wanda ya rasa kujerarsa a majalisar dokoki.
A ran 29 ga watan Yuni na shekarar 2008, Mr.Mwanawasa wanda a lokacin ke da shekaru 59 da haihuwa, jikinsa ya shanye ba zato ba tsammani a lokacin da yake halartar taron shugabannin kungiyar tarayyar Afirka a birnin Sharm el Sheik da ke kasar Masar. Sa'an nan, a ran 1 ga watan Yuli, an kai shi birnin Paris don yi masa jiyya. A ran 19 ga watan Agusta, da misalin karfe 10 da rabi na safe, Mr.Mwanawasa ya rasu a birnin Paris.
Bisa tsarin mulkin kasar Zambia, idan shugaba ya mutu, to, mataimakinsa zai zama shugaban wucin gadi na kasar, amma tilas ne a sake gudanar da zaben shugaban kasar cikin kwanaki 90.
A ran 5 ga watan Satumba na wannan shekara, Mr.Banda ya ci zaben zama shugaban jam'iyyar MMD, wato jam'iyyar da ke rike da ragamar mulkin Zambia. A ran 30 ga wancan wata, an yi zaben shugaban kasar Zambia, wanda zai maye gurbin marigayi Mwanawasa. A ran nan da safe, da misalin karfe shida, masu jefa kuri'a sun fara zuwa rumfunan zabe 6456 da ke yankunan zabe 150 a duk fadin kasar, don kada kuri'a.
Gaba daya 'yan takara hudu, ciki har da shugaban jam'iyyar MMD, Rupiah Banda da Michael Sata daga jam'iyyar PF da dai sauransu sun shiga zaben. Zaben ya zama na biyar tun bayan da Zambia ta fara gudanar da tsarin kasancewar jam'iyyun siyasa da dama a shekarar 1991.
A ran 2 ga watan nan da muke ciki, Mr.Rupiah Banda ya ci zaben. Bisa sakamakon zabe da kwamitin zabe na Zambia ya bayar, an ce, yawan kuri'un da Mr.Banda ya samu ya kai kashi 40.09%, a yayin da Michael Sata, babban abokin takararsa daga jam'iyyar PF ya sami kuri'un da yawansu ya kai kashi 38.13%.
A ran nan, a Lusaka, babban birnin kasar Zambia, an rantsar da Rupiah Banda a matsayin shugaban kasar, kuma wa'adin aikinsa zai kammala a shekarar 2011, wato ke nan, ya zama shugaba na hudu a tarihin kasar Zambia. A gun bikin rantsuwar, Mr.Banda ya yi jawabin cewa, babban nauyin da ke bisa wuyansa a cikin wa'adin aikinsa shi ne kawar da talauci.
Uwar gidan Rupiah Banda ita ce Hope Mwansa Makulu, kuma suna da 'ya'ya biyar.(Lubabatu)
|