A birnin Wuzhong na jihar Ningxia mai ikon aiwatar da harkokin kanta ta kabilar Hui da ke arewa maso yammacin kasar Sin, akwai wani "Iyalin limamai daga zuriya zuwa zuriya". Yang Xuezhi, 'dan shekaru 103 shi ne wanda ya fi tsufa a cikin wannan iyalin, 'ya'yansa biyu, da jikansa na farko su ma sun zama limamai. A cikin shirinmu na yau kuma, za mu kawo muku wani bayani ne game da tsoho Yang Xuezhi da Iyalinsa na Limamai daga zuriya zuwa zuriya.
Tsoho Yang Xuezhi na kabilar Hui yana zaune a sabon gidansa mai benaye biyu.
Ko da ya ke yanzu yanayin sanyi ne ake ciki a jihar Ningxia, amma a lokacin da wakilinmu ke hira tare da tsoho Yang Xuezhi, iyalinsa sun kawo wasu 'ya'yan itatuwa da a kan samu a yanayin zafi.
Karamin 'dansa Yang Baoqing, 'dan shekaru 45 ya gaya wa wakilinmu cewa,
"Muna iya cin dukkan abincin da muke so, yanzu muna iya cin abincin da a kan samu a yanayin zafi."
Tun da daga lokacin kuruciyarsa, Yang Baoqing yana zaune tare da kakansa. A cikin tunaninsa, ya kan ji yunwa a lokacin da yake karami. Ya ce,
"Ina da 'yan uwa da yawa a gidanmu, saboda haka, mu kan lashe dukka abinci a lokacin cin abinci."
Amma, yanzu kayayyakin da ke cikin gidan tsoho Yang Xuezhi suna da kyau, kuma suna nuna sigar musamman ta musulmi. Kan kyautattuwar da suka samu wajen muhallin zaman rayuwarsu, Yang Baoqing ya jiku da cewa,
"A da, mutane suna yin fatan iya zama a wani gida mai benaye biyu, kuma tare da samun wutar lantarki sosai. Amma, yanzu kayayyakin da suka samu sun wuce fatansu sosai. Lallai, an samu sauye-sauye sosai kan zaman rayuwarsu."
Ban da wannan kuma, a shekaru fiye da goma da suka wuce, a karkashin kwarin giwa da tabbaci da gwamnatin kasar Sin ta bayar kan manufar samun 'yancin kai wajen bin addinai, tsoho Yang Xuezhi ya taba aiki a masallatai kusan goma, har ma ya zama kamar limamin masallatan da ke wurin. 'Dansa Yang Baoqing ya taba zaman koyon ilmin addini daga mahaifinsa, daga baya kuma, shi ma ya zama liman. Yanzu, Yang Baoqing yana aiki a babban masallaci na Wu Dong da ke birnin Wuzhong, wannan kuma daya daga masallatai fiye da dubu goma na birnin Wuzhong.
Game da makomar 'ya'yansa kuma, Yang Baoqing na fata za su zabi hanyar samun bunkasuwa bisa ra'ayoyinsu. Yanzu, 'dansa na farko yana karatu a sakandare, kuma ya sami sakamako mai kyau wajen karatu. 'Dansa na biyu yana karatu a firamare, ba ma kawai yana iya Sinnanci sosai ba, har ma ya koyi Larabci kadan a gidan renon yara na musulmi. Yang Baoqing ya ce,
"Yanzu, jam'iyyar kwaminis da gwamnatinmu na samar da dama mai kyau gare mu a fannoni daban daban. Saboda haka, ina fata 'ya'yana za su mayar da hankulansu kan karatu, ta yadda za su iya saka wa zaman al'umma da alheri."
Iyalin Yang Baoqing yana wani wurin da 'yan kabilun Hui da Han ke zaune tare. A ko wace shekara, gwamnati da kwamitin mazaunan wuri suna shirya bikin makwabta, ciki har da na zaman cin abinci tare, da yin yawon shakatawa tare. A lokacin bikin kuma, mazaunan wurin daga kabilu daban daban za su yi iyakacin kokarinsu don dafa nau'o'in abinci masu dadin ci, daga baya kuma za su ci wannan abinci tare. Ban da wannan kuma, a lokacin da iyalan kabilar Hui suka gamu da wahalhalu, mazauna na kabilar Han su kan bayar da taimakonsu. Yang Baoqing ya ce,
"Lallai, manufar gyare-gyare da bude kofa ga kasashen waje ta kara matsayin zaman rayuwar jama'a, na san wannan ne bayan da na ci gajiya."
A birnin Wuzhong, ban da masallatai kanana da na manya kuma, akwai sauran wurarren ayyuka na addinai daban daban, gaskiya ne, kabilu da addinai daban daban na iya zaman tare kamar yadda ya kamata. Yang Baoqing ya ce,
"Lallai, gwamnatin kasarmu ta dauki matakai da yawa don kiyaye zaman lafiya da hadin gwiwa. Mutane na iya bin addinin da suke so cikin 'yanci."
A 'yan shekarun da suka wuce, a karkashin kokarin da mabiya addinai masu kaunar kasa, ciki har da limamai na zuriyoyi uku daga iyalin Yang Xuezhi, mazaunan birnin Wuzhong suna zaman tare kamar yadda ya kamata.
|