Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-01-08 17:21:51    
Kasashen Sin da Amurka suna murnar cikon shekaru 30 da kafa huldar dimplomasiyya a tsakaninsu

cri

A ran 1 ga watan Janairu na shekarar 1979, wato yau da shekaru 30 da suka gabata, an kafa huldar diplomasiyya a tsakanin kasashen Sin da Amurka a tsanake. Yanzu wannan hulda ta riga ta zama daya daga cikin huldodin diplomasiyya mafi muhimmanci kuma mafi sabunta a duniya. Sabo da haka, a ran 7 da ran 8 ga wata, kasashen Sin da Amurka sun shirya jerin bukukuwa domin taya murnar cikon shekaru 30 da kafuwar huldar diplomasiyya a tsakaninsu. Alal misali, a ran 7 ga wata da yamma, an shirya wata gasar wasan Pingpon a tsakanin 'yan wasa na kasashen Sin da Amurka.

"A ran 7 ga wata da yamma an yi gasar wasan Pingpon ta sada zumunta a tsakanin 'yan wasa na kasashen Sin da Amurka domin taya murnar cikon shekaru 30 da kafuwar huldar diplomasiyya a tsakanin kasashen biyu. Mr. Wang Guangya, mataimakin ministan harkokin waje na kasar Sin ya raka Mr. John Negroponte, mataimakin sakatariyar harkokin waje ta kasar Amurka wanda ke yin ziyara a Beijing, sun kalli wannan gasa tare. 'Yan wasa 7 na kasashen Sin da Amurka sun shiga wannan gasa. Kuma 'yan wasa biyu daga cikinsu sun taba ganin yadda kasashen Sin da Amurka suka daidaita harkokin waje ta hanyar yin gasar wasan Pingpon a shekarar 1971."

A cikin shekaru 30 da suka gabata bayan da aka kafa huldar diplomasiyya a tsakanin kasashen Sin da Amurka, ana nuna mamaki sosai ga cigaban da aka samu kan huldar da ke tsakanin kasashen biyu. A da, shugabannin kasashen biyu su kan gana da juna sau 1 ko biyu a cikin tsawon wasu shekaru, amma yanzu suna tuntubar juna a kullum. A da, ba su yin shawarwari a tsakaninsu, amma yanzu an riga an kafa tsare-tsaren yin tattaunawa fiye da 60 a tsakaninsu. A waje daya kuma, a cikin wadannan shekaru 30 da suka gabata, yawan kudaden cinikin waje da aka yi a tsakaninsu ya ninka fiye da sau 120. Bugu da kari kuma, jama'arsu ba su iya kai wa juna ziyara a da, amma yanzu, mutane fiye da dubu 5 suna kaiwa ko kawowa a tsakanin kasashen biyu a kowace rana. Mr. Yang Mingjie wanda ke nazarin huldodin kasa da kasa ya bayyana cewa, huldar da ke tsakanin kasashen Sin da Amurka wadda ta samu cigaba sosai tana amfana wa duniya kwarai. Mr. Yang ya ce, "A cikin shekaru 10 kafin karshen yakin cacar baki, hadin gwiwar da aka yi a tsakanin kasashen Sin da Amurka, kuma a tsakanin kasar Sin da sauran kasashen duniya bisa manyan tsare-tsare ta bayar da gudummawa sosai ga kokarin kawo karshen yakin cacar baki. Sannan a cikin shekaru 90 na karnin da ya gabata, bangarorin biyu sun yi kokari kan yadda za su iya dacewa da hakikanin halin da ake ciki a duniya bayan da aka kawo karshen yakin cacar baki. Sun kuma bayar da gudummawa kwarai ga kokarin tabbatar da cigaban huldar da ke kasancewa a tsakanin manyan kasashen duniya. Yanzu, wato bayan da aka shiga karni na 21, bangarorin biyu suna fama da kalubale iri iri da suke kawo barazana ga kwanciyar hankali a duniya. Kasashen Sin da Amurka, wato kasa mafi girma daga cikin kasashe masu arziki, kuma kasa mafi girma daga cikin kasashe maso tasowa dukkansu suna samun moriya lokacin da ake kokarin raya duk duniya bai daya, kuma su ne karfin da ke sa kaimi ga kokarin raya duk duniya bai daya ko kara yin hadin gwiwa a fannonin tsaron kai ba irin na gargajiya ba."

A cikin shekaru 30 da suka gabata bayan da aka kafa huldar diplomasiyya a tsakanin Sin da Amurka, ko da yake su kan yi cece-ku-ce kan wasu batutuwa, amma abin da ya fi muhimmanci shi ne bangarorin biyu sun iya yin musayar ra'ayoyinsu, kuma sun iya tattauna batutuwa kai tsaye a fili. Madam Jan Merris, mataimakiyar shugaban kwamitin kula da huldar da ke tsakanin Amurka da Sin wadda ta taba ganin yadda aka kafa huldar diplomasiyya a tsakanin Sin da Amurka, ta ce, "Shekaru 30 sun riga sun wuce. A ganina, ya kamata kasashen biyu su kara fahimtar juna da sanin juna. A idon mutanen da suke kokarin kara kyautata huldar da ke tsakanin kasashen biyu, har yanzu ya kasance da rashin aminci da rashin fahimtar juna a tsakanin gwamnatoci da jama'a na wadannan kasashe biyu. Tabbas ne za a ci gaba da samun ra'ayoyi daban daban kan wasu batutuwa a tsakaninsu, amma ina da imani cewa, muhimmin abu shi ne bangarorin biyu su kwantar da hankalinsu su yi musayar ra'ayoyinsu bisa hakikanin halin da ake ciki, kuma za su iya sauraran ra'ayoyin bangare na daban cikin sahihanci." (Sanusi Chen)