Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-01-07 15:24:21    
Faduwar maki a kasuwannin hannayen jari na kasashen Afirka ta hana mutum sanin makomarsu

cri

A shekarar 2008 da ta wuce, faduwar maki da aka samu a ko wace kasuwar hannayen jari a fadin duniya ba ta bar kasuwannin kasashen Afirka kadai ba. A sakamakon dalilai daban daban, an samu faduwar maki sosai a mayan kasuwannin hannayen jari da ke kudu da hamadar Sahara, a shekarar bana. Amma, ba a rasa kasuwar da ta sha bamban da saura ta samu hauhawar maki ba. Bisa halin da ake ciki, manazarta ba su cimma ra'ayi daya ba, da wuya za a iya yin hasashe kan makomar kasuwannin hannyen jari na Afirka ta shekarar 2009.

A kasuwar sayar da hannayen jari ta Johannesburg ta kasar Afirka ta Kudu, wadda ta fi girma a nahiyar Afirka, ba a samu maki mai kyau ba cikin shekarar 2008. Zuwa ranar 12 ga watan Disamba, makinta ya kai dubu 21 da wani abu, ya ragu da kashi kimanin 28%, idan aka kwatanta shi da maki na dubu 30 da aka samu a karshen shekarar 2007. A wajen kasuwar Nijeriya kuma, makin ya kusan kai dubu 60 a farkon shekarar 2008, amma ya sauka da kashi 47% zuwa dubu 30 da wabi abu a farkon watan Disamba. A kasar Kenya da ke gabashin Afirka, ita ma ba ta samu wani sakomako mai kyau ba, inda makinta ya ragu da kashi 40% cikin shekarar 2008. Amma, duk da tabarbarewar da ake samu a kasuwannin sauran manyan kasashen Afirka, kasar Ghana da ke yammacin Afirka ta ki bin sahunsu, ta samu hauhawar makin kasuwarta ta hannayen jari da kashi 60% cikin shekarar 2008.

Manazarta na ganin cewa, dalilai da yawa sun haddasa faduwar maki a yawancin kasuwannin hannayen jari na kasashen Afirka, wadanda suka hada da sauyin yanayin siyasa, da hauhawar farashin kaya, da saukowar farashin danyen mai, da rikicin hada-hadar kudi da dai makamantansu.

Ga misali, a farkon shekarar 2008, kasuwar hannayen jari ta kasar Kenya tana cikin raguwa sakamakon tarzomar zaben da aka samu a karshen shekarar 2007. A kasar Zambia kasuwarta ta taba samun hauhawar, amma sai murna ta koma ciki ganin rasuwar shugaba Mwanawasa ta janyo faduwar maki sosai.

Haka kuma, dayan daga cikin abubuwan da ke addabar kasuwannin hannayen jari na kasashen Afirka shi ne, hauhawar farashin kaya da ta shafi makamashi da sauran kayayyakin masarufi, ta sa 'yan Afirka masu hannayen jari suka fara sayar da hannayen jarin da suka rike. A baya ga haka kuma, janye jari daga Afirka da 'yan kasuwan kasashen waje suka yi da raguwar samun kudin da 'yan Afirka ketare suke aika wa gida, su ma sun yi illa ga kasuwannin hannayen jari na kasashen Afirka. Domin kudin da aka samu daga zuba jari da 'yan Afirka ketare ya taba zaman muhimmin dalilin da ya sa kasuwannin hannayen jari na kasashen Afirka suka cira sama.

Har wa yau kuma, rikicin hada-hadar kudi da ke addabar tattalin arzikin kasashen duniya shi ma ya kawo matsin lamba ga kasuwannin hannayen jari na Afirka. Ko da ya ke matsin lambar din ba iri na kai tsaye ne ba, amma yana mummunan tasiri domin ya raunana imanin masu zuba jari kan makomar kasuwannin hannayen jari. Ban da wannan kuma, faduwar farashin danyen mai daga dala 150 ganga daya zuwa bai kai dala 40 ba na yanzu, ta kawo hasara sosai ga kasar Nijeriya, wadda ta fi yawan samar da danyen mai a nahiyar Afirka. Haka kuma, ta raunana kasuwar kasar ta hannayen jari sosai.

Dangane da makomar kasuwannin hannayen jari na kasashen Afirka, manazarta ba su cimma ra'ayi daya ba tukuna, wasunsu na sa ran cewa, dunkuluwar tattalin arzikin kasashen Afirka gu daya za ta haifar da hauhawar maki a kasuwar hannun jari, yayin da wasu na ganin cewa, da wuya za a gyara halin da ake ciki cikin gajeren lokaci, sakamakon rashin imani da ake wa kasuwar hannun jari.  (Bello Wang)