Kamar yadda kuka sani, a cikin shekarar 2008, kasar Sin ta samu babban sakamako a fannoni daban daban musamman a fannin wasannin motsa jiki. A cikin shirinmu na yau, bari mu yi muku bayani kan wannan.
Tun daga farkon shekarar 2008, mataimakin shugaban babbar hukumar wasannin motsa jiki ta kasar Sin Cui Dalin ya fara yin aikin share fage saboda ya kyautata tunani cewa, dole ne kasar Sin ta samu sakamako mai gamsarwa a yayin gasar wasannin Olympic ta Beijing ta shekarar 2008, in ba haka ba, kasar Sin ba za ta dace da matsayin kasashe masu saukar baki wato kasa mai shirya gasar ba, kuma jama'ar kasar Sin ba za su gamsar da aikinsu ba. Amma, a cikin shekarar 2007, 'yan wasa daga kasar Amurka da ta Rasha sun nuna babban karfi a yayin gasannin da aka shirya, wannan ya matsa lamba ga Cui Dalin. Kan wannan batu, Cui Dalin ya bayyana cewa, "A yayin manyan gasannin duniya da aka shirya a shekarar 2007, lambobin yabon da 'yan wasan Rasha suka samu sun zarce namu, lambobin yabon da 'yan wasan Amurka suka samu su ma sun zarce namu. Amma mun samu iznin shirya gasar wasannin Olympic ta shekarar 2008, shi ya sa dole ne mu sanya iyakacin kokari."
Cui Dalin ya taba gaya mana cewa, wannan aiki yana da wuya, amma sakamakon da 'yan wasan kasar Sin suka samu a shekarar 2008 ya faranta ran mutanen kasashen duniya sosai da sosai.
A watan Fabrairu na shekarar 2008, an yi gasar cin kofin duniya ta wasan kwallon tebur tsakanin kungiyoyi a birnin Guangzhou na lardin Guangdong dake kudancin kasar Sin. A yayin gasar, kungiyar kasar Sin ta sake samun zakarun kungiyoyin maza da mata, an mayar da sakamakon nasarar farko da kasar Sin ta samu a shekarar 2008.
Ran 8 ga watan Mayu da misalin karfe 9 da minti 18 da safe, an mika wutar yula ta gasar wasannin Olympic ta Beijing kan wuri mafi tsayi na dutsen Everest wanda ya fi tsayi a duniya a karkashin tsaron 'yan wasan hawa dutse 12 na kasar Sin. Wannan ne karo na farko da wutar yula ta wasannin Olympic ta isa wuri mafi tsayi a duniya. Koda yake wasan hawa dutse bai shiga gasar wasannin Olympic ba tukuna, kuma a wancen lokaci, ba a bude gasar wasannin Olympic ta Beijing ba, amma 'yan wasan hawa dutse na kasar Sin sun bude wani sabon shafi a tarihin hawa dutse na duniya, shi ya sa 'yan wasa sun yi ta ihu yayin da suke kan dutsen Everest. "Duniya daya, buri daya. A nuna kuzari, kuma a mika mafarki."
Ran 8 ga watan Agusta, an bude gasar wasannin Olympic a Beijing, ko shakka babu wannan shi ne gasa mafi muhimmanci a wannan shekara. A yayin gasar, 'yan wasan kasar Sin sun nuna kwazo da himma kuma sun samu babban sakamako.
Ran 9 ga watan Agusta da misalin karfe 12 da tsakar rana, 'yar wasan daukan nauyi daga kasar Sin Chen Xiexia mai shekaru 25 ta daga sandar karfe mai nauyin kilo 212 sama cikin nasara, daga nan ta samu lambar zinariya ta farko ta gasar wasannin Olympic ta Beijing ga kasar Sin, lambar zinariyar nan tana da ma'ana ta musamman. Chen Xiexia ta bayyana cewa, "Ina so in gaya musu cewa, ban bata ransu ba, a nan kuma ina so in nuna musu babbar godiya saboda goyon bayan da suka nuna mana cikin dogon lokaci."
A cikin 'yan kwanaki 16 da aka yi gasar, bi da bi 'yan wasan kasar Sin sun samu lambobin zinariya daya bayan daya, a karshe dai, sun samu lambobin yabo 100 wadanda a cikinsu lambobin zinariya sun kai 51, a karo na farko ne kasar Sin ta zama kasa mafi yawan lambobin zinariya a tarihin gasar wasannin Olympic. A cikin wadannan kwanaki 16, an rera taken kasar Sin sau da yawa, jama'ar kasar Sin suna jin alfahari kwarai da gaske.
Abu mafi muhimmanci shi ne a yayin gasar, 'yan wasan kasar Sin sun samu lambobin yabo a cikin kusan dukkan gasannin da aka shirya. Cui Dalin ya bayyana cewa, wannan shi ne muhimmin sakamakon da 'yan wasan kasar Sin suka samu a yayin wannan gasa. Ya ce, "Sakamakon da 'yan wasan kasar Sin suka samu ya nuna mana cewa, kasaitaccen karfin wasannin motsa jikin na kasar Sin ya samu sabon ci gaba."
A yayin gasar, 'yan wasan kasar Sin sun nuna karfinsu kan wasanni daban daban musamman wajen wasan kwallon tebur da na daukan nauyi da ninkaya da tsalle-tsalle da lankwashe-lankwashe. Game da wannan, babban malami mai horaswa na kungiyar 'yan wasan kwallon tebur ta maza ta kasar Sin Liu Guoliang ya ce, "Na tabbatar da kokarin 'yan wasanmu sosai, kafin mu shiga gasar, sai na gaya musu cewa, dalilin da ya sa kwallon tebur ya zama kwallon kasa a Sin wato wasan kwallo mafi muhimmanci gare mu ba domin kuna iya samun lambobin zinariya ba ne, sai dai dole ne mu mayar da gasar kwallon tebur a yayin gasar wasannin Olympic bikin jama'ar kasar Sin. A yayin gasar, 'yan wasanmu sun cimma burin."
A ranar da aka rufe gasar wasannin Olympic ta Beijing, 'dan wasan dambe daga kasar Sin Zou Shiming ya samu lambar zinariya a yayin gasar wasan maza na ajin kilo 48, wannan ce lambar zinariya ta farko da 'yan wasan dambe na kasar Sin suka samu a yayin gasar wasannin Olympic. Daga baya kuma, Zhang Xiaopin ya samu lambar zinariya ta wasan dambe na maza na ajin kilo 81. Bayan gasar, Zou Shiming ya ce, "Wannan lambar zinariya tana da muhimmanci sosai saboda mun yi kokari cikin dogon lokaci."
Cui Dalin shi ma ya ji dadi, ya ce, "A lokacin da muka lashe kungiyar kasar Amurka da ta Rasha, wato a ran 24 ga watan Agusta da misalin karfe 2 da yamma, Zhang Xiaopin ya samu lambar zinariya ta 51 ta kungiyar kasar Sin. Dukkanmu mun ji farin ciki kwarai da gaske."
A shekarar 1908, an taba gabatar da tambayoyi uku, yaushe kasar Sin za ta shiga gasar wasannin Olympic? Yaushe kasar Sin za ta samu lambar zinariya a yayin gasar? Yaushe kasar Sin za ta shirya gasar? Kawo yanzu, shekaru 100 sun wuce, sakamakon da muka samu fatan al'umma ne a kasar Sin cikin shekaru 100.
A cikin shekarar 2008, 'Yan wasan kasar Sin sun samu babban sakamako, ko shakka babu, za su tuna da shekarar har abada.(Jamila Zhou)
|